text
stringlengths
1
6.82k
yanzu haka dai wasu al'umomi a najeriya da nijar da chadi dama sauran wasu kasashe a nahiyar afrika sun shiga halin kakanikayi sakamakon ambaliyar ruwa a 'yan kawanakin da suka wuce
za a iya cewa ambaliyar ruwa ta zama ruwan dare gama duniya a kasar pakistan kawai sama da mutane miliyan ashirin ne wannan matsala ta shafa
a jamhuriyar nijer an yi ambaliyar a wurare da dama da suka hada da yamai maradi damagaram da sauransu
a najeriya mai makwabtaka da nijar din ma an sami ambaliyar a jihohin da suka hada da borno da jigawa da sokoto da kano
dubbai sun rasa gidajensu suna zaune a wurare na wucingadi ko dai na hukuma ko kuma a wajen makwabta da 'yanuwa
ruwan kuma ya mamaye gonaki da dama mutane dayawa sun rasa rayukansu miliyoyi kuma sun bar muhallinsu sannan an yi asarar dukiya mai dimbin yawa
to ko wanne hali jama'ar da lamarin ya shafa suke ciki musamman a najeriya da niger shin wadanne irin matakan rigakafi ne za a iya dauka don tinkarar matsalar ambaliyar ruwan shirinmu na ra'ayi riga kenan na yau
wannan shi ne abin da za mu tattauna a cikin shirinmu na ra'ayi riga na wannan makon
kuma mun gayyato baki kamar su barrister yusuf mato kwamishinan muhalli na jihar jigawa da dr ado mukhtar bichi malami a jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar kano dake wudil kuma masani kan ilmin labarin kasa ko geography da turanci
haka nan kuma mun gayyaci malam mustapha sulaiman wani jami'in hukumar bayar da agajin gaggawa ta najeriya nema
a jamhuriyar nijar kuma mun samo laftana diam balah shugaban karamar hukumar tasawa
akwai kuma mutanen da matsalar ta shafa kai tsaye sannan kuma akwai wasu daga cikinku ku masu saurare ta wayar tarho
tura wannan labarin game da aika wa
babban labari
bidiyo me ya sa matasa ba sa iya magana da hausa sosai
me ya sa matasa ba sa iya magana da hausa sosai
bidiyo me ya sa elrufai ya rusa gidan hunkuyi
me ya sa elrufai ya rusa gidan hunkuyi
bidiyo black panther babban fim din 'yan afirka na farko
black panther babban fim din 'yan afirka na farko
bidiyo mutumin da ke rayuwa gida daya da namun daji
mutumin da ke rayuwa gida daya da namun daji
bidiyo duk abinda namiji ya yi mace ma za ta iya hannatu bashir
duk abinda namiji ya yi mace ma za ta iya hannatu bashir
ka'idojin amfani
manufar tsare sirri
zabin tallacetallace
copyright © 2018 bbc bbc ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba karanta tsarinmu game da bakin shafuka
jami'in gwamnatin syria ya koma ga yan adawa bbc news hausa
tsallaka zuwa abubuwan da ke ciki
abinda ke ciki
shiryeshirye na musamman
shiryeshiryen rediyo
jami'in gwamnatin syria ya koma ga yan adawa
aika wannan shafi facebook
aika wannan shafi email
aika wannan shafi
wannan shafukan na waje ne kuma za su bude ne a wani shafin daban
aika wannan shafi whatsapp
game da aika wa
rufe wurin aika labari
jami'in syria mafi girma da ya koma goyon bayan masu adawa da gwamnatin kasar ya shaidawa bbc cewa mahukuntan kasar ne ke amfani da dakarun alqaeda wurin kai baki dayan manyan hareharen bamabaman da ke haddasa asarar rayuka da dama
shugabannin syria dai sun sha musanta alhakin kai harin bamabaman tare da zargin 'yan ta'adda da kai hareharen
nawaf alfares wanda a makon jiya ya ajiye mukaminsa na jakadan syria a iraqi ya kwatanta shugabannin syria da kerkecin da aka jikkata wanda zai yi duk abinda zai iya domin tserar da ransa
nawef ya kara da cewa akwai bayanai da ba'a tabbatar ba cewa an dan yi amfani da makamai masu guba a garin homs sai dai na acewarsa ya yi imanin gwamnatin ba za ta ki amfani da makaman masu guba ba matukar ta ga cewa al'ummar syria na neman samun nasara a kanta
tura wannan labarin game da aika wa
karin bayani
fada na kara tsananta kusa da damascus
kofi annan zai gana da lavrov a moscow
ka'idojin amfani
manufar tsare sirri
zabin tallacetallace
copyright © 2018 bbc bbc ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba karanta tsarinmu game da bakin shafuka
tsallaka zuwa abubuwan da ke ciki
abinda ke ciki
shiryeshirye na musamman
shiryeshiryen rediyo
aika wannan shafi facebook
aika wannan shafi email
aika wannan shafi
wannan shafukan na waje ne kuma za su bude ne a wani shafin daban
aika wannan shafi whatsapp
game da aika wa
rufe wurin aika labari
jose mourinho ya dauki kofinsa na farko tun bayan da ya dawo chelsea bayan da kungiyar ta doke tottenham a gasar kofin league a filin wembley
bayan da christian eriksen ya kai wa chelsea hari kwallon ta doki saman karfen raga kyaftin din chelsea john terry ya ci kwallon farko a minti na 45
sai kuma kwallo ta biyu wadda diego costa ya shirgo dan wasan tottenham kyle walker ya je tarewa ya ci kansu a minti na 56
mourinho wanda ya dawo stamford bridge a farkon kakar bara bayan ya je inter milan da real madrid yanzu ya jagoranci kungiyar ta dauki kofuna bakwai a kociyanta da ya yi sau biyu
dukkanin kungiyoyin biyu sun doke junansu sau daidai a kakar bana kafin wannan haduwar tasu
rabon tottenham da daukan kofi tun wanda ta ci na league a 2008
tura wannan labarin game da aika wa
ka'idojin amfani
manufar tsare sirri
zabin tallacetallace
copyright © 2018 bbc bbc ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba karanta tsarinmu game da bakin shafuka
tsallaka zuwa abubuwan da ke ciki
abinda ke ciki
shiryeshirye na musamman
shiryeshiryen rediyo
aika wannan shafi facebook
aika wannan shafi email
aika wannan shafi
wannan shafukan na waje ne kuma za su bude ne a wani shafin daban
aika wannan shafi whatsapp
game da aika wa
rufe wurin aika labari
shugaban kasar faransa franswa holland ya yi kiran da a gudanar da sauyesauye a tsarin tarayyar turai bayan jam'iyyun dake adawa da hadewar tarayyar turan sun samu gagarumar nasara a zaben da aka gudanar na majalisar dokokin kungiyar da ta hada kasashe 28
gabanin wani taro da za su yi nan gaba a yau talata a brussels mr holland ya ce tsarin tarayyar turan na da ne kuma yana da wuyar fahimta ga 'yan kasashen yace yakamata alkiblar kungiyar ta zamo ta bunkasa tattalin arziki
ya yi maganar ne bayan jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayin 'yan mazan jiya the front national ta cinye zabukan tarayyar turai a faransa da kimanin kashi daya bisa ukku na kuri'un ta tura jam'iyyar socialist ta mr holland a matsayi na ukku
tura wannan labarin game da aika wa
karin bayani
dubban mutane sun bar gidajensu a czech
ka'idojin amfani
manufar tsare sirri
zabin tallacetallace
copyright © 2018 bbc bbc ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba karanta tsarinmu game da bakin shafuka