text
stringlengths
1
6.82k
shugaba idriss deby na chadi ya bukaci kasashen yammacin afrika da su hanzarta tura dakaru zuwa arewacin mali
da yake magana wajen bude taron kolin kungiyar yankin yammacin afrika ta ecowas a yamosssoukro babban birnin ivory coast shugaba deby ya ce lokacin surutu ya kare illa na daukar mataki
kasar chadi dai ta tura dakaru fiye da dubu 2 zuwa arewacin mali domin taimakawa dakarun faransa da na mali fatattakar masu tsatstsauran kishin islama da kuma azibinawa masu tayar da kayar baya
to amma kasashen yammacin afrika na sanyi sanyi wajen cika alkawarin aikewa da dakaru kusan dubu 8 a cansojojin chadi fiye da 20 ne dai aka kashe kawo yanzu
ana samun karuwar bakin haure a italiya bbc news hausa
image caption ana ceto bakin haure a tekun italiya
masu tsaron gabar tekun italiya sun ce an samu karuwar bakin hauren da ke kokarin tsallakawa cikin kasar daga kogin baharrum
jiragen ruwan kasar sun ceto mutane fiye da 4000 a kwanaki uku da suka wuce
a ranar lahadi kadai an ceto lalatattun jiragen ruwa guda 22 dauke da mutane
wani kwalekwale da yake dauke da mutane 150 ya nitse wani waje mai nisan kilomita 120 tsakanin sa da gabar tekun libya inda aka samu gawarwakin bakin haure guda tara kuma an kuma ceto mutane a kalla 140
ana zaton za a samu karin bakin haure da za su yi kokarin tsallaka tekun idan yanayi ya inganta
apc me ya hana kaddamar da kwamitin amintattu bbc hausa
apc me ya hana kaddamar da kwamitin amintattu
wasu 'yan kwamitin amintattun jam'iyyar apc mai mulki a nigeria sun ce rashin kaddamar da kwamitin shekaru uku bayan kafa shi na nuna cewa jam'iyyar ba ta san abinda ya ke mata ciwo ba
to sai dai jam'iyyar ta ce an rusa kwamitin kuma za a maye gurbinsa
a najeriya rahotanni daga garin potiskum a jihar yobe arewacin kasar sun ce jama'a da dama ne suke tsere daga gidajen su yayinda kasuwanni da shaguna suka kasance a rufe sakamakon wata tarzoma da ta barke
rikicin ya fara ne bayan da wasu gungun matasa suka fara kone kone su kuma jami'an tsaro suka fara mayar da martani da harbe harbe domin tarwatsa su
hakan na faruwa ne jim kadan bayan wani taron addu'oi da dubun dubatar 'yan kasuwa da malamai da wasu mutanen garin suka gudanar a harabar bakin kasuwar shanu
kasuwar da a makon da ya gabata wasu 'yan bindiga suka kai harin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da talatin tare da jikkata wasu da dama
najeriya yadda aka kashe mutum 86 a jihar filato bbc news hausa
image caption najeriya ta dade ta na fama da rikici tsakanin makiyaya 'yan kabilar berom da kuma makiyaya (tsohon hoto ne)
'yan sanda a jihar filato da ke tsakiyar najeriya sun ce akalla mutum 86 ne suka mutu bayan da fada ya barke tsakanin manoma da makiyaya
an daure tsohon gwamnan filato joshua dariye shekara 14
kun san mai shari'ar da ke tura gwamnonin najeriya fursina
tuni dai aka kafa dokar hana fita a wasu yankuna uku na jihar ta filato
kwamishinan 'yan sanda na jihar undie adie ya ce binciken da aka gudanar a wasu kauyuka bayan kai harin ya tattabatar da cewa an kashe mutum 86 sannan wasu shida su ka samu rauni
ya ce an kona gidaje 50 da baburan hawa 15 da kuma motoci biyu
kwamishinan yada labarai na jihar yakubu datti ya shaida wa bbc cewa dokar hana fitar za ta yi aiki daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe a riyom da barikin ladi da kuma jos ta kudu domin hana jama'a daukar doka a hannunsu da samar da zaman lafiya
sai dai sabanin bayanin 'yan sanda mr datti ya ce sama da mutum 20 ne suka jikkata kuma suna samun magani a asibitoci daban daban
image caption ana sa ran hollande da merkel za su yi kira da a samu haɗin kai a kasashen turai
shugaban faransa francois hollande da shugabar gwamnatin jamus angela merkel na yin alhinin cika shekara 100 na yaƙi mafi tsawo da aka yi a lokacin yakin duniya na ɗaya
dubundubatar sojojin faransa da na jamus sun rasa rayukunsu a watanni 10 da aka shafe ana yaƙi a arewa masogabashin faransa
daga ƙarshe sai kasar faransa ta yi nasara a yaƙin
amma a yanzu ana ganin verdun a matsayin wata alama ta sulhu tsakanin 'yan ƙasar faransa da jamus kuma ana sa ran mista hollande da ms merkel za su yi kira da a samu haɗin kai a kasashen turai
za a samar da matakai don rage rikicin kudus bbc news hausa
mista kerry ya yi wannan magana ne a jordan wadda ita ce kasar da ke da alhakin kuka da masallacin na alaqsa
ya ce matakan da aka amince da su sun hada da sabunta bukatar isra'ila na tabbatar da dokokin da dama can ake amfani da su a wajen ibadar da kuma shirin tattaunawa a kan yadda za a karfafa matakan tsaro a wajen
a bayabayan nan ne ake ta samun rikicerikice tsakanin palasdinawa da isra'ilawa a yankin masallacin
jordan muna nan kan musayar fursuna da is bbc news hausa
jordan muna nan kan musayar fursuna da is
kasar jordan din ta nanata wannan kudirin ne duk da kashe dan kasar japan kenji goto da kungiyar ta is ta yi
wani mai magana da yawun gwamnatin jordan ya yi allah wadai da kisan
ita ma kasar japan ta baiyana matukar damuwa da kashe kenji goto da yan kungiyar kasar musuluncin suka yi
firaministan kasar shinzo abe ya yi tur da allah da kisan
jami'an japan dai sun hada hannu da hukumomin jordan domin ganin an sako mr goto da kuma matukin jirgin sama dan kasar jordan moaz alkasasbeh wanda shi ma 'yan kungiyar kasar musuluncin ke garkuwa da shi
za a ci kyautar dala 2000 a gasar hikayata ta 2017 bbc news hausa
za a ci kyautar dala 2000 a gasar hikayata ta 2017
ana iya aiko da rubutun ta hanyar imel na labaribbchausa@bbccouk har zuwa ranar lahadi 10 ga watan satumba da za a rufe gasar
zan sake dambatawa da furu a 2016 klitschko
image caption fury ya ce yana fatan shi ma zai kare kambunan da ya lashe zuwa tsawon lokuta
wladimir klitschko ya ce zai sake yin dambe da tyson fury a shekara mai zuwa bayan da ya yi rashin nasarar kumbunansa na damben boksin da suka kara a dusseldorf a ranar asabar
klitschko mai shekaru 39 ya ce tabbas an doke ni amma har yanzu akwai dambe a tare da ni za mu tsayar da ranar da za mu sake yin wasa da wurin da ya kamata mu fafata
fury ya mai da martani da cewar ni dan dambe ne a shirye nake na amsa kalubale ina son na zama fitatcen dan wasa a duniya kuma za mu sake karawa damben zai yi zafi
fury ya lashe kambun wba da ibf da kuma wbo daga hannun klitschko rabon da a doke shi tun a 2004 bayan da ya sha kashi a hannun lamon brewster
ku saukar da sababbin wakokin sayyad gadan kaya ga tsaraba album 2018
kamar yadda kuka sani a kwana kin baya mun kawo muku biyu daga cikin wakokin wannan sabon album din
domin haka yanzu ga cikakken album din mun kawo mukuayi sauraro lafiya
dolphins ta lashe gasar premier a najeriya bbc news hausa
dolphins ta lashe gasar premier a najeriya
wani magidanci yayi ma wasu yan mata fyade a jihar kano
you are athome»labarai»wani magidanci yayi ma wasu yan mata fyade a jihar kano
kotu a jihar kano ta daure wani magidanci kuma dan kasuwa mai suna lawan zubairu saboda aikata fyade akan wasu yan biyu yan shekaru 11
dan sandan da ya shigar da karan rufai inusa yace mahaifin yan biyun ibrahim musa wanda ke zama a hotoron fulani quarters a jihar kano ne ya shigar da karar ranar 18 ga watan maris
ya fadi wa kotu cewa zubairu ya rudi yaran ne da su bishi zuwa gidansa in da daga nan ya danne su yayi musu fyade
shi zubairu da ake zargi da aikata wannan mummunar aiki ya ki amincewa da zargin
alkali muhammad jibril ya yanke hukuncin da a daure shi har sai bayan ya yi shawara da babbar darektan hukumar kula da irin wannan laifuka na jihar kano sannan kuma ya daga ci gaba da sauraren karan zuwa 27 ga watan afirilu
allah ya kara dauka kaku ameen
allah yakiyaye wannan alamarin
hutudole labarai da hausa shin ko kun san garin da kusan kowa ke tallan asuwaki
shin ko kun san garin da kusan kowa ke tallan asuwaki
bisa tarihi dai kowanne gari da sana'ar da ya shahara a kai wadda kuma galibi al'umarsa ke dogaro da ita a kauyen abokim da ke karamar hukumar etung a jihar crossriver ta kudancin najeriya baya ga noma wanda shi ne gadon al'ummomin afirka da dama jama'ar kauyen maza da mata manya da yara babu sana'ar da suke yi kamar sana'ar ferewa da kuma tallan asuwaki ko magogi
a kwanakin baya wakilin bbc is'haq khalid ya ziyarci kauyen inda ya kuma tattauna da wasu masu wannan sana'a
wakilin bbc ya ce wasu masu wannan sana'a sun shaida masa cewa shaharar wannan sana'a ta kai ga har jama'a daga wasu kasashen afirka musamman jamhuriyar benin na zuwa garin wanda ke kan iyakar najeriya da kamaru domin sarin asuwakin buhubuhu zuwa kasashensu
to sai dai kuma rikicin 'yan aware da ake yi a yankin kamaru mai magana da harshen ingilishi inda ake sayo itacen da ake ferewa domin yin magogin ya fara kawo cikas ga sana'ar a garin na abokim da ke kan iyaka
fatan jama'ar wannan yanki dai shi ne sana'ar tasu ta kara bunkasa domin su samu karin kudin shiga sannan ita ma najeriya ta kasance mai alfahari da fitar da magogi kasashen duniya don bunkasa tattalin arzikinta
hutudole>>zai birgeka ya kayatar dakai zaka nishadantu ka kuma karu kalli tsohon hoton laila da isa a isa
hutudole labarai da hausa karanta yanda rahama sadau farantawa wani masoyinta rai
tauraruwar finafinan hausa da turanci rahama sadau ta nuna saukin kai tare da wani masoyinta da ya roke ta ta tayashi murnar zagayowar ranar haihuwarshi
masoyin na rahama yace ki taimaka ki farantamin rai ta hanyar tayani murnar zagayowar ranar haihuwata ai kuma sai gashi rahamar ta tayashi
daga zauren girkegirke girka masa (waina) ta musamman kuma cikin sauki (daga lola's kitchen) _ al'ummata mujallar hausa lamba daya
masa (waina) abincin hausawa ce da ta samu karbuwa sosai a tsakakkanin alummar hausa kuma a hankali makwabatan hausawa suka fara karbarta a matsayin abinci na musamman laalla saboda dadinta da kuma kasancewarta abinci ba gama gari ba
abinci ne da ake amfani da shi kwarai a gidan sarauta
ga yadda wata wacce ba bahaushiya ba ta bayyana yadda za ka sarrafa masacikin sauki ba tare kin fita dag cikin gida zuwa kai markade ba haka kuma ta yi wa tata masar kwalliya ta yadda ta kara armashi da gamsarwa
tabakalashe daga sabon kundin wakar da mawakin raps mi abaga ya saki