text
stringlengths 6
1.75k
|
---|
wadannan su ne sunayen 'ya'ya maza na isra'ila, wadanda suka tafi masar tare da yakubu, kowanne da iyalinsa. |
su ne ra'ubainu, da saminu, da lawi, da yahuza,da issaka, da zabaluna, da biliyaminu,da dan, da naftali, da gad, da ashiru. |
zuriyar yakubu duka mutum saba'in ne, yusufu kuwa, an riga an kai shi masar. |
ana nan sai yusufu ya rasu, shi da dukan 'yan'uwansa na wannan tsara. |
amma 'ya'yan isra'ila suka hayayyafa, suka karu kwarai, suka ribabbanya, suka kasaita kwarai da gaske, har suka cika kasar. |
a wannan lokaci kuwa aka yi wani sabon sarki a masar wanda bai san yusufu ba. |
sai ya ce wa mutanensa, duba, jama'ar isra'ila sun cika yawa sun fi karfinmu. |
zo, mu san irin dabarar da za mu yi musu, don kada su ribabbanya, domin in aka fada mana da yaki, kada su hada kai da makiyanmu, su yake mu, su tsere daga kasar. |
suka kuwa nada musu shugabannin aikin gandu domin su wahalshe su da mawuyacin aiki. aka sa su su gina wa fir'auna biranen ajiya, wato fitom da ramases. |
amma ko da yake masarawa sun kara tsananta musu, duk da haka sai suka kara karuwa, suna ta yaduwa. masarawa kuwa suka tsorata saboda isra'ilawa. |
suka kuma tilasta wa isra'ilawa su yi ta aiki mai tsanani. |
suka bakanta musu rai da aiki mai tsanani na kwaba, da yin tubali, da kowane irin aiki a saura. a cikin ayyukansu duka suka tsananta musu. |
sarkin masar ya ce wa ungozomar ibraniyawa, shifra da fu'a,sa'ad da kuke yi wa matan ibraniyawa hidimarku ta ungozomai, in kuka gan su durkushe, in jariri ne suka haifa, sai ku yi masa sanadin mutuwa, in kuma jaririya ce, ku bar ta da rai. |
amma da yake ungozomar masu tsoron allah ne, ba su yi yadda sarkin masar ya umarce su ba, amma suka bar 'ya'ya maza da rai. |
don haka sarkin masar ya kirawo ungozomar, ya ce musu, me ya sa kuka bar 'ya'ya maza da rai? |
ungozomar suka ce wa fir'auna, domin matan ibraniyawa ba kamar matan masarawa ba ne, gama su masu kwazo ne, sukan haihu tun ungozomar ba su kai wurinsu ba. |
allah kuwa ya yi wa ungozoman nan alheri. mutanen suka ribanya, suka kasaita kwarai. |
allah kuma ya ba ungozoman nan zuriya domin sun ji tsoronsa. |
fir'auna kuwa ya umarci dukan mutanensa ya ce, duk jaririn da aka haifa wa ibraniyawa, sai ku jefa shi cikin kogin nilu, amma idan jaririya ce, ku bar ta da rai. |
sai wani mutum, balawe, ya auro 'yar lawi. |
matar kuwa ta yi ciki, ta haifi da. sa'ad da ta ga jaririn kyakkyawa ne, sai ta boye shi har wata uku. |
da ta ga ba za ta iya kara boye shi ba, sai ta saka kwando da iwa, ta yabe shi da katsi, ta sa jaririn a ciki, ta ajiye shi cikin kyauro a bakin kogin nilu. |
ga 'yar'uwarsa kuma a tsaye daga nesa don ta san abin da zai same shi. |
gimbiya, wato 'yar fir'auna, ta gangaro domin ta yi wanka a kogin nilu, barorinta 'yan mata suna biye da ita a gabar kogin nilu. da ta ga kwando a cikin kyauro, ta aiki baranyarta ta dauko mata shi. |
sa'ad da ta tude kwandon ta ga jariri yana kuka. sai ta ji tausayinsa, ta ce, wannan daya daga cikin 'ya'yan ibraniyawa ne. |
'yar'uwar jaririn kuwa ta ce wa gimbiya, in tafi in kirawo miki wata daga cikin matan ibraniyawa da za ta yi miki renon dan? |
sai gimbiya ta ce mata, je ki. yarinyar kuwa ta tafi ta kirawo mahaifiyar jaririn. |
da ta zo, sai gimbiya ta ce mata, dauki wannan jariri, ki yi mini renonsa, zan biya ki ladanki. matar kuwa ta dauki jaririn ta yi renonsa. |
da jaririn ya yi girma sai ta kai shi wurin gimbiyar. yaro kuwa ya zama tallafinta. ta rada masa suna musa, gama ta ce, domin na tsamo shi daga cikin ruwa. |
ana nan wata rana, sa'ad da musa ya yi girma, ya tafi wurin mutanensa, sai ya ga yadda suke shan wahala. ya kuma ga wani bamasare yana dūkan ba'ibrane, daya daga cikin 'yan'uwansa. |
da ya waiwaya, bai ga kowa ba, sai ya kashe bamasaren, ya turbude shi cikin yashi. |
kashegari da ya sāke fita, sai ya ga wadansu ibraniyawa biyu suna fada da juna. ya ce wa wanda yake kwaran dan'uwansa, me ya sa kake bugun dan'uwanka? |
ya amsa, ya ce, wa ya nada ka sarki ko alkali a bisanmu? so kake ka kashe ni kamar yadda ka kashe bamasaren? |
sai musa ya tsorata, ya ce, assha, ashe, an san al'amarin! |
da fir'auna ya ji, sai ya nema ya kashe musa. amma musa ya gudu daga gaban fir'auna, ya tafi, ya zauna a kasar madayana. da ya kai, sai ya zauna a bakin wata rijiya. |
ana nan wadansu 'yan mata bakwai, 'ya'yan firist na madayana suka zo su cika komaye da ruwa domin su shayar da garken mahaifinsu. |
sai makiyaya suka zo, suka kore su, amma musa ya tashi ya taimake su, ya kuma shayar da garkensu. |
lokacin da suka koma wurin mahaifinsu, reyuwel, wato yetro, ya ce musu, yaya aka yi yau, kuka komo da sauri haka? |
sai suka ce, wani bamasare ne ya cece mu daga hannun makiyaya, har ya debo ruwa, ya shayar da garkenmu. |
reyuwel kuwa ya ce wa 'ya'yansa mata, a ina yake? me ya sa ba ku zo da shi ba? ku kirawo shi, ya zo, ya ci abinci. |
musa kuwa ya yarda ya zauna tare da reyuwel. sai ya aurar wa musa da 'yarsa ziffora. |
ita kuwa ta haifa masa da, ya rada masa suna gershom, gama ya ce, bako ne ni, a bakuwar kasa. |
ana nan, a kwana a tashi, sai sarkin masar ya rasu. jama'ar isra'ila suka yi nishi, suka yi kuka kuma saboda bautarsu, kukansu na neman gudunmawa ya kai gun allah. |
allah kuwa ya ji nishinsu, sai ya tuna da alkawarinsa da ya yi wa ibrahim, da ishaku, da yakubu. |
allah ya dubi jama'ar isra'ila, ya kuwa kula da su. |
wata rana, sa'ad da musa yake kiwon garken surukinsa, yetro, firist na madayana, sai ya kai garken yammacin jeji, har ya zo horeb, wato dutsen allah. |
a can mala'ikan ubangiji ya bayyana gare shi cikin harshen wuta daga cikin kurmi. da musa ya duba, sai ga kurmin yana cin wuta, amma duk da haka bai kone ba. |
musa kuwa ya ce, bari in ratse, in ga wannan abin banmamaki da ya sa kurmin bai kone ba. |
sa'ad da ubangiji ya ga ya ratse don ya duba, sai allah ya kira shi daga cikin kurmin, ya ce, musa, musa. |
musa ya ce, ga ni. |
allah kuwa ya ce, kada ka matso kusa, ka cire takalminka, gama wurin da kake tsaye, tsattsarka ne. |
ya kuma ce, ni ne allah na kakanninka, wato ibrahim, da ishaku, da yakubu. sai musa ya boye fuskarsa, gama yana jin tsoro ya dubi allah. |
ubangiji kuwa ya ce, na ga wahalar jama'ata wadanda suke a masar, na kuma ji kukansu da suke yi a kan shugabanninsu. na san wahalarsu,don haka na sauko in cece su daga hannun masarawa, in fito da su daga cikin wannan kasa zuwa kyakkyawar kasa mai ba da yalwar abinci, wato kasar kan'aniyawa, da hittiyawa, da amoriyawa, da ferizziyawa, da hiwiyawa, da yebusiyawa. |
yanzu fa, ga shi, kukan jama'ar isra'ila ya zo gare ni. na kuma ga wahalar da masarawa suke ba su. |
zo, in aike ka wurin fir'auna domin ka fito da jama'ata, wato isra'ilawa, daga cikin masar. |
amma musa ya ce wa allah, wane ni in tafi gaban fir'auna in fito da isra'ilawa daga cikin masar? |
sai allah ya ce, zan kasance tare da kai, wannan kuwa zai zama alama a gare ka, cewa ni ne na aike ka. sa'ad da ka fito da jama'ar daga masar, za ku bauta wa allah a bisa dutsen nan. |
sai musa ya ce wa allah, idan na je wurin isra'ilawa na ce musu, ‘allah na ubanninku ya aiko ni gare ku,’ idan sun ce mini, ‘yaya sunansa?’ me zan fada musu? |
allah kuwa ya ce wa musa, ni ina nan yadda nake, ya kuma ce, haka za ka fada wa isra'ilawa, ‘ni ne ya aiko ni gare ku.’ allah kuma ya sāke ce wa musa, fada wa isra'ilawa cewa, ‘ubangiji allah na kakanninku, wato na ibrahim, da ishaku, da yakubu ya aiko ni gare ku.’ wannan shi ne sunana har abada. da wannan suna za a tuna da ni a dukkan zamanai. |
tafi, ka tattara dattawan isra'ila, ka fada musu, ‘ubangiji allah na kakanninku ya bayyana gare ni, wato na ibrahim, da ishaku, da yakubu, ya ce, sosai ya ziyarce ku, ya kuma ga abin da ake yi muku a masar. |
ya yi alkawari cewa zai fisshe ku daga wahalar masar zuwa kasar kan'aniyawa, da hittiyawa, da amoriyawa, da ferizziyawa, da hiwiyawa, da yebusiyawa. kasa wadda take mai ba da yalwar abinci.’za su kasa kunne ga muryarka. sa'an nan kai da dattawan isra'ila za ku tafi gaban sarkin masar ku ce masa, ‘ubangiji allah na ibraniyawa ya gamu da mu. yanzu fa, muna rokonka, ka yarda mana mu yi tafiyar kwana uku a cikin jeji mu mika masa hadaya.’amma na sani sarkin masar ba zai bar ku ku fita ba, sai an yi masa tilas. |
domin haka zan mika hannuna in bugi masar da dukan mu'ujizaina wadanda zan aikata cikinta, sa'an nan zai bar ku ku fita. |
zan sa wannan jama'a su yi farin jini a idanun masarawa, sa'ad da kuka fita kuma, ba za ku fita hannu wofi ba. |
amma kowace mace za ta roki makwabciyarta da wadda take cikin gidanta kayan ado na azurfa, da na zinariya, da tufafi, za ku sa wa 'ya'yanku mata da maza. da haka za ku washe masarawa. |
musa kuwa ya amsa ya ce, ai, ba za su gaskata ni ba, ba kuma za su kasa kunne ga maganata ba, gama za su ce, ‘ubangiji bai bayyana gare ka ba.’ amma ubangiji ya ce masa, mene ne wannan a hannunka? |
ya ce, sanda ne. |
ubangiji ya ce, jefa shi kasa. sai ya jefa shi kasa, sandan ya zama maciji, musa kuwa ya yi gudunsa. |
sa'an nan ubangiji ya ce wa musa, mika hannunka ka kama wutsiyarsa. ya mika hannunsa ya kama shi, ya zama sanda kuma a hannunsa. |
sai ubangiji ya ce, ta haka za su gaskata ubangiji allah na kakanninsu ne, wato na ibrahim, da ishaku, da yakubu, ya bayyana gare ka. |
sai ubangiji ya sāke ce masa, sa hannunka cikin kirjinka. sa'ad da ya fitar da shi, ga hannunsa a kuturce fari fat. |
allah kuma ya ce masa, mai da hannunka cikin kirjinka. sai ya mai da hannunsa cikin kirjinsa. sa'ad da ya fitar da shi, ga hannun ya koma kamar sauran jikinsa. |
ubangiji kuma ya ce, idan kuma ba su gaskata ka ba, ba su kuma kula da mu'ujiza ta fari ba, ya yiwu su gaskata ta biyun. |
idan ba su gaskata mu'ujizan nan biyu ba, ba su kuma kula da maganarka ba, sai ka dibi ruwa daga kogin nilu, ka zuba bisa busasshiyar kasa. ruwan zai zama jini a bisa busasshiyar kasa. |
amma musa ya ce wa ubangiji, ya ubangijina, ni ba mai lafazi ba ne, ban taba zama ba, ko a yanzu ma, bayan da ka yi magana da bawanka, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma. |
ubangiji kuwa ya ce masa, wa ya yi bakin dan adam? wa ya yi bebe ko kurma, ko mai gani ko makaho? ko ba ni ubangiji ba ne? |
yanzu fa, tafi, zan kasance tare da bakinka, in koya maka abin da za ka fada. |
amma musa ya ce, ya ubangijina, in ka yarda, ka aiki wani. |
ubangiji kuwa ya hasala da musa, ya ce, haruna dan'uwanka balawe ba ya nan ne? lalle na san shi ya iya magana, ga shi nan ma, yana fitowa ya tarye ka. sa'ad da ya gan ka kuwa zai yi murna cikin zuciyarsa. |
sai ka yi magana da shi. ka kuma sa masa maganata a baka, zan kuwa kasance tare da bakinka da bakinsa. zan kuma sanar da ku abin da za ku yi. |
shi zai yi maka magana da jama'a, zai zama bakinka, kai kuwa za ka zama kamar allah a gare shi. |
za ka rike wannan sanda a hannunka, da shi za ka aikata mu'ujizan. |
musa ya koma wurin yetro, surukinsa, ya ce masa, ina rokonka, ka bar ni in koma wurin 'yan'uwana a masar, in ga ko a raye suke har yanzu. |
sai yetro ya ce wa musa, ka tafi lafiya. |
ubangiji kuwa ya fada wa musa a madayana, ya koma masar, gama dukan wadanda suke neman ransa sun rasu. |
saboda haka musa ya dauki matarsa da 'ya'yansa maza, ya haushe su bisa kan jaki, ya koma kasar masar, yana rike da sandan allah a hannunsa. |
ubangiji kuwa ya ce wa musa, sa'ad da ka koma masar, sai ka kula, ka aikata a gaban fir'auna dukan mu'ujizan da na sa cikin ikonka. amma zan taurara zuciyarsa, don kada ya bar jama'a su fita. |
za ka ce wa fir'auna, ubangiji ya ce, ‘isra'ila dan fārina ne. |
na ce maka ka bar dana ya tafi domin ya bauta mini, amma in ka ki ka bar shi ya tafi, yanzu zan kashe dan fārinka.’ ya zama kuwa sa'ad da musa yake masauki a kan hanya sai ubangiji ya gamu da shi, ya nema ya kashe shi. |
sai ziffora ta dauki kankara ta yanke lobar danta, ta taba gaban musa da shi, ta ce, kai angon jini kake a gare ni. |
sa'an nan ubangiji ya kyale shi. ta kuma ce, kai angon jini ne, saboda kaciyar. |
sai ubangiji ya ce wa haruna, tafi, ka taryi musa cikin jeji. ya kuwa tafi ya tarar da shi a dutsen allah, ya sumbace shi. |
sa'an nan musa ya fada wa haruna abubuwan da ubangiji ya aike shi ya yi, da dukan mu'ujizan da ya umarce shi ya aikata. |
sai musa da haruna suka tafi suka tattara dukan dattawan isra'ila. |
haruna dai ya hurta wa dattawan al'amuran da ubangiji ya fada wa musa. ya kuma aikata mu'ujizan a idanunsu. |
dattawan kuwa suka gaskata. sa'ad da suka ji ubangiji ya ziyarci isra'ilawa, ya kuma ga wahalarsu, sai suka sunkuya, suka yi masa sujada. |
bayan wannan musa da haruna suka tafi gaban fir'auna, suka ce, ga abin da ubangjiji allah na isra'ila ya ce, ‘bar jama'ata su tafi domin su yi mini idi cikin jeji.’ amma fir'auna ya ce, wane ne ubangiji, har da zan ji maganarsa, in bar isra'ilawa su tafi? ai, ban san ubangiji din nan ba, balle in bar isra'ilawa su tafi. |
sai suka ce, allahn ibraniyawa ya gamu da mu, muna rokonka, ka bar mu mu yi tafiyar kwana uku cikin jeji domin mu yi wa ubangiji allahnmu hadaya, don kada ya aukar mana da annoba ko takobi. |
amma sarkin masar ya ce wa musa da haruna, me ya sa kuke hana jama'ar yin aikinsu? ku tafi wurin aikin gandunku. |
ya kuwa ci gaba ya ce, ga jama'ar kasar sun yi yawa, yanzu kuna so ku hana su yin aikinsu. |
a ran nan fa fir'auna ya umarci shugbannin aikin gandu da manyan jama'a, ya ce,nan gaba kada ku kara ba mutanen nan budu na yin tubali kamar dā. ku sa su, su tafi, su tara budu da kansu. |
End of preview. Expand
in Data Studio
README.md exists but content is empty.
- Downloads last month
- 93