Spaces:
Runtime error
Runtime error
Dalilin da ya sa na fice daga PDP. | |
Tsohon shugaban majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ya bayyana wasu dalilai da ya sa ya fice daga PDP ya koma APC. | |
Idan ba a manta ba Tsohon Shugaban Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ya wancakalar da jam'iyyar PDP, ya koma APC a cikin wannan mako. | |
Dogara ya ce da ya tsaya yana shan wulaƙancin gwamna Bala na PDP a jihar Bauchi da ya taimaka wa matuƙa ya yi nasara a zaben 2019, gara ya tattara ya fice daga jam'iyyar ya koma inda ya APC. | |
Babban dalilin da ya sa na fice kiwa shine yadda PDP ke mulki a jihar Bauchi. | |
Kowa ya san irin rawar da na taka a zaɓen gwamnan jihar wanda tsohon ministan Abuja, Bala Mohammed ya doke gwamna mai ci, Mohammed Abubakar. | |
Amma kuma yanzu nine abin watsarwa da cakala a gwamnatin Bala. | |
Maimakon in ci gaba da zama a PDP ana min abinda aka dama gara na kauce in basu wuri, in koma inda na fito. | |
Dogara ya rubuta wasikar ficewa daga PDP wanda ya aika wa shugaban jam'iyyar na mazaɓar sa, Bogoro C, dake jihar Bauchi. | |
A ƙarshe ya ce kamar yadda ya rika nunawa sauran gwamnoni inda suka gaza da inda za su gyara a baya, shi kuma Bala ba shafaffe da mai bane. | |
Gara in yi tafiyata in ƙyale su. | |
Gobara ta tashi a wani gidan mai dake Kano. | |
Gobarar dai ta tashi ne da misalin karfe 10 na dare, wadda ta shafe kusan sa'o'i biyu tana ci, duk da daukin da jami'an hukumar kashe gobara ta Jihar Kano da jami'an tsaro da kuma al'ummar gari su kai wurin. | |
A lokacin Freedom Radio ta ziyarci wurin, ta iske jama'a cikin dimuwa da kuma jami'an tsaro daban-daban a wurin ta ko ina, kasancewar wurin na da alaka da babbar tashar mota da aka fi sani da tashar Kuka, wadda ake jigilar fasinjoji daga nan Kano zuwa sauran jihohi da ma kasashen masu makwabtaka da kasar nan. | |
Baya ga kasuwar Kofar Ruwa wadda ta yi fice a Arewacin Najeriya. | |
Freedom Radio ta zanta da wasu da wasu shaidun gani da ido, wadanda su ka ce tashin gobarar ya haifar da gudun tsira da rai a tsakanin jama'a. | |
Wani kwandastan mota a tashar ta Kofar Ruwa ya ce, sun yi hadin gwiwa da jami'an sintiri wajen tseratar da fasinjojin da suka shiga firgici sanadiyyar gobarar. | |
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ya zuwa lokacin da muke hada wannan rahoto tana ci gaba da tattara bayanai domin gano musabbabi da kuma asarar da gobarar ta haifar, kamar yadda kakakin hukumar Sa'idu Muhammad Ibrahim ya bayyana. | |
A wani bangaren kuma rahotonni na cewa an samu wasu bata-gari da suka yi kokarin kutsawa cikin kasuwar ta Kofar Ruwa domin yin sata, sai dai jami'an ƴan sanda da jami'an sinturi sun yi kokarin korarsu tare da tsare dukiyoyin al'umma. | |
A kan hakan ne muka tuntubi kakakin rundunar ƴan sanda ta jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da faruwar al'amarin. | |
MAGANIN KORONA: Har yanzu ba mu gama yin gwajin ingancin maganin da aka hada a Najeriya ba. | |
A yayin da ƙasashen Turai ke cigaba da yin gwaje-gwaje ingancin maganin Korona da suka hada, Najeriya ma ba a barta a baya ba wajen hadawa da yin nata gwajin magungunan. | |
Hukumar kula da Ingancin Abinci Da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta bayyana cewa tana yin gwajin magungunan warkar da Korona har guda 40 da masu hada magungunan gargajiya suka mikawa hukumar. | |
Shugaban hukumar Mojisola Adeyeye ta sanar da haka ranar Talata a garin Abuja. | |
Mojisola ta ce ana yin gwajin ingancin magungunan ne saboda kada wajen neman kiba a samo rama. | |
Tun bayan bayyanar annobar Korona, masu hada maganin gargajiya suka fantsama bincike domin ganin suma ba a barsu a baya ba wajen ganin an hada maganin cutar. | |
Da yawa cikin su sun mika samfarin maganin su ga hukuma domin yin gwaji da tantance ingancin sa. | |
Haka kuma NAFDAC ta gindaya musu wasu sharudda da dokoki da za su bi wajen hada maganin. | |
Za a yi gwajin ingancin magungunan a dabbobi a karon farko tukunna. | |
Mojisola ta gargadi masu maganin kada su kuskura su jaraba wani magani ba tare da hukumar ta bada damar haka ba. | |
A watan Mayu ne hukumar NAFDAC ta bayyana cewa a soshiyal midiya da shafukan jaridu ne kadai ake ganin labarai na masu ikirarin cewa sun gano maganin gargajiya wanda zai warkar da cutar Coronavirus. | |
Adeyeye ta bayyana cewa har mutum daya ne tak ya tunkari hukumar NAFDAC ya nemi ta duba ingancin maganin da ya yi ikirarin cewa ya hada na gargajiya, da ya ce zai iya warkar da Coronavirus. | |
Shi ma wancan mutum dayan, ba wai maganin cutar ce gidigat ya ce ya gano ba. | |
Cewa ya yi ya gano maganin alamomin rashin lafiyar da ake ganin su ne alamomin kamuwa da cutar. | |
Sai dai kuma tun bayan haka wasu masu maganin suka rika tunkarar hukumar da nasu hadin. | |
Ramaphosa ya fuskanci tambayoyi a majalisa. | |
Wannan ne karon farko na jerin tambayoyi da shugaba Ramaphosa ya fuskanta a gaban 'yan majalisa tun bayan da ake ta raɗe-raɗin cin hanci da rashawa tsakanin manyan jami'an gwamnatinsa da ma wasu mambobin jami'iyyarsa. | |
Ramaphosa ya yi alƙawarin zurfafa bincike da ma kawo gyara a fannin da ke da alhakin kula da ɓangaren sayen kayayyakin yaƙi da cutar ta covid-19. | |
Kasar Afirka ta Kudu na zama ƙasa ta biyar a jerin ƙasashen duniya da annobar coronavirus ta addabe su, sai dai shugaban ya ce cin hanci da rashawa na taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da cutar a ƙasar. | |
Ranar Asabar Najeriya Za Ta Bude Tashoshin Jiragen Sama Na Kasa Da Kasa. | |
Hukumomi a Najeriya sun ce za su bude tashoshin jiragen sama don zirga-zirgar fita da kuma shigowa kasar, daga ranar Asabar mai zuwa, a karon farko bayan watanni biyar da rufewa. | |
Tun a ranar 23 ga wata Maris gwamnatin kasar ta dakatar da shige da ficen jirage, a dalilin dakile yaduwar annobar coronavirus. | |
Gwamnatin ta ce jirage hudu na farko da za su shigo daga kasashen ketare za su fara sauka ne a birnin tarayya Abuja. | |
Sai birnin Lagos, amma ya zuwa yanzu ba a bayyana ko daga ina wadannan jiragen za su zo ba. | |
A cewar ministan sufurin jirage Hadi Sirika, matakin bude wannan shine, ganin yadda ba a samu wata matsalaba tun bayan bude hada-hadar jiragen na cikin gida a ranar 8 ga watan Yuli. | |
Sirika, ya kara da cewar za a tabbatar da cewar an bi duk ka'idodji da suka kamata wajen ganin an samu nasarar dawowar zirgar-zirgar jirage. | |
An Sake Samun Mutum 591 Na Cutar COVID-19 A Najeriya. | |
A ranar Juma'a aka samu sabbin mutane 591 suka kamu da cutar COVID-19. | |
Da wannan sabbin adadin mutane da suka kamu da Covid-19 a kasar ya kai ga adadin mutanen da suka kamu zuwa 39,539 kana 16,559 Suka warke kuma 845 suka mutu. | |
Cibiyar yaƘi da cutuka ta Najeriya, NCDC, ta bayar da adadin mutane da jihohi a shafin ta na Twitter. | |
An kara samun masu Corona a kungiyar mu - Marseille. | |
Kungiyar kwallon kafa ta Marseille dake kasar faransa ta ce an samu karin ƴan wasa guda uku da suka kamu da annobar cutar Corona, bayan mutun biyar da aka samu a makon da ya gabata. | |
Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai a yau Talata. | |
Haka kuma, kungiyar ta ce an dage gasar ta League 1 ta kasar Faransa da aka dauki niyyar farawa a ranar Juma'ar da ta wuce sakamakon ƴan wasan guda biyar da suka kamu da cutar ta COVID-19. | |
Marseille ta kuma ce, tuni ta sanar da masu ruwa da tsaki wajen shirya gasar ta League 1, sakamakon samun karuwar mutane uku da suka kamu da cutar bayan da mutune biyar na farko suka kamu, domin samun mafita daga lamarin. | |
APC Ta Zargi Gwamnan Neja Da Yunkurin Kawo Tarzoma A Jam'iyyar - Leadership Hausa Newspapers. | |
A wata sanarwa da jam'iyyar APC ta fitar Talatar makon nan ta zargi Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, da yunkurin kawo tarzoma a cikin jam'iyyar. | |
Takardar, wacce Shugaban Jam'iyyar Injiniya Muhammad Jibrin Imam da Sakataren Jam'iyyar Barista Muhammed Liman su ka sanya wa hannu, ta bayyana cewar, a tsawon shekaru shida da jam'iyyar ta yi ta na mulkin jihar, Naira miliyan 512 ne kadai ta samu. | |
Takardar ta ci gaba da cewar, taron da gwamnan ya kira na masu ruwa da tsaki, wanda ya jagoranta a daren Lahadin karshen makon da ya gabata zai taimaka wajen ci gaba da kawo tarzoma a jam'iyyar, inda su ka ce sun rubuta wa sakatariyar jam'iyyar ta kasa abubuwan da ke ci gaba da faruwa a jihar. | |
A cewar Injiniya Imam, "mun fahimci Gwamnan Jihar Neja ya na kokarin rarraba kawunan ƴaƴan jam'iyyar ta hanyar shirya taron masu ruwa da tsaki, wanda ba bisa ka'ida ba, domin duk wani korafin da a ke yi kan shugabannin jam'iyyar, a kan rubuta wa sakatariyar jam'iyya ne ta shiyya, domin su yi bincike". | |
Ya ci gaba da cewar zuwa yanzu a shekaru shida da kafa jam'iyyar, naira miliyan 512 ne ke cikin asusun jam'iyyar. | |
Ya ce, abinda ya fahimta a matsayin gwamnan na kasancewa a cikin kwamitin riko na kasa wanda an kafa su ne 25 ga Yuli, 2020, wanda shugaban kasa ya jagoranta domin su jagoranci shirya matsalolin da ke tsakanin ƴaƴan jam'iyyar da janye korafe-korafen da ke kotu tsakanin ƴaƴan jam'iyyar. | |
Yace kudaden da muka samu muna biyan albashin ma'aikatan sakatariyar jam'iyyar da su, da kuma wasu ayyukan da su ka shafi jam'iyya, zabukan fidda gwani da daidaita wasu matsalolin ƴaƴan jam'iyya kamar tallafin kiwon lafiya saboda rashin samun damar tallafin gwamnati, ba wani kudin jam'iyya da muka kashe ba bisa ka'ida ba, muna kalubalanta kowaye akan ya kawo mana hujjar barnatar da kudaden jam'iyya. | |
Kamar yadda na bayyana, zabukan fidda gwanin kananan hukumomin jihar da ya gabata, shi ne zaben fidda gwani mafi muhimmanci da a ka yi a kasar nan wanda muka yi tare da tsoffin kwamishinoni da kwamishinonin da ke rike da madafun iko a yanzu a dukkanin kananan hukumomi ashirin da biyar da ke jihar, wanda kudaden da a ka kashe a zabukan an rabawa kwamishinonin dan su kawo mazabun su. | |
Dan haka, kuskure ne ga kowane mutum yace kudaden jam'iyya ana kashe su ba bisa ka'ida ba, wannan kusan rashin adalci ne da kokarin baiwa kare mummunar suna dan kokarin rataye shi, yace ba wani kwamiti da a ka kafa dan yin binciken yadda a ka kashe kudaden jam'iyya kuma wa ya kafa ta. | |
Daga cikin kudaden da mai korafi yayi yace kudaden da ya ke zargin an barnatar, kudade ne da sakatariyar jam'iyya ta kasa ta bayar, ba wasu kudade ma irin wannan dan haka ina kalubalantar kowaye akan wannan batu da ya kawo shaidarsa dan tabbatar da wannan zargin na shi ta kowace hanya. | |
Imam yace mun tsaya tsayin daka akan kare jam'iyyar APC daga yunkurin ko waye ko kungiya daga ruguza jam'iyyar nan, ya kara da cewar duk wani zarge zarge akan jam'iyya ko wani shugaban jam'iyyar daga matakin jihar za a rubutawa kwamitin da ke kula da shiyya ne kamar yadda tsarin jam'iyyar ya bayyana a sashi na 21 (B) (bi), (d) a shafi na 82 na tsarin jam'iyyar. | |
Saboda haka masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ba su da wani rawar takawa musamman idan sun yi yunkurin kwace karfin kwamiti don haka hukuncin su bai da wani tasiri. | |
Saboda wannan dalilin, su ne ingantattun shugabannin jam'iyyar da a ka amince da su a jihar, a dara ta 21 da sakin layi na shida a shafi na 87 na kundin tsarin jam'iyyar, duk wani abinda ya saba ma wannan ba za a yi anfani da shi ba. | |
Saboda hukuncin yanke kauna da shugabannin riko su ka yi kuskure ne. | |
Ya ce, wadanda su ka gabatar tare da amincewa a zaman jiya littinin a taron da bai inganta ba, wanda Alhaji Abubakar Magaji, da Janar Muhammed Garba, da Hon. Ahmed Dogonkoli, har da Alhaji Ibrahim Balarabe da dukkanin kwamishinoni, ba mambobi ba ne na kwamitin zartaswa ta jam'iyya a jihar ba. | |
Kwamitin zartaswa na masu ruwa da tsakin jam'iyya shugaban jam'iyya Injiniya Mohammed Imam ne kadai zai jagorance shi ba gwamna zai jagoranci shugabannin jam'iyya ta jiha ba. | |
Takardar ta kara da cewar, gwamna Abubakar Sani Bello ya tuna cewar batun cika alkawalin da a ka yiwa al'ummar jihar a lokacin zabe, da tafiya da iyayen jam'iyya a cikin gwamnati ta yadda kowa zai amfana a jihar da dukkanin shiyyoyi ta hanyar bada mukaman siyasa, wanda shi ne matsalar gwamna da jam'iyya. | |
Takardar ta yaba wa ƴan majalisar dokoki na tarayya wadanda su ka ki halartar taron da kuma jawo hankali akan yin sulhu akan dukkanin matsalolin da ke tsakanin ƴayan jam'iyyar, wannan ba abin mamaki ba ne ga ƴan majalisun da su ka san ciwon kansu, da su ka ki amincewa da kama karya a matsayin dokar jam'iyya. | |
Saboda haka, akwai bukatar shugaban kwamitin riko na kasa ya janyo hankalin gwamna Abubakar Sani Bello a kan matsayin da ya dace kar ya yi yunkurin ruguza siyasar jihar. | |
A shirye Najeriya ta ke a dama da ita a tattalin arzikin Internet - Freedom Radio Nigeria | |
Ministan sadarwa da bunƙasa tattalin arziki ta internet Dr Isa Ali, Pantami ya ce, kasar nan a shirye take a dama da ita a juyin juya hali a ɓangaren tattalin arziki na internet. | |
Ya kuma ce gwamnati a shirye ta ke ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da masana da ke jami'oi da sauran masu ruwa da tsaki wajen ganin an riƙa damawa da ƙasar nan a duk wata harka ta fasahar zamani. | |
Dr Isa Ali Fantami ya bayyana hakan ne yayin wani taro na ƙasa da ƙasa kan bunƙasa fasahar sadarwa wanda aka gudanar ta kafar internet. | |
Haka zalika ministan ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin mataki na farko da gwamnati ta ɗauka domin ganin ana damawa da ƙasar nan kan fasahar ta sadarwa shine sauya sunan ma'aikatar daga ma'aikatar sadarwa zuwa ma'aikatar sadarwa da bunƙasa tattalin arziki ta internet. | |
Yadda sinadarin hana abinci lalacewa ke illa ga kiwon lafiyar mutane a Najeriya. | |
Wasu masana kimiyya sun gargadi mutane da su guji cin abincin da aka yi amfani da sinadarin hana abinci lalacewa cewa cin abinci irin haka na cutar da kiwon lafiyar mutum. | |
Masanan sun yi wannan gargadi ne bayan binciken da suka gudanar kan ingancin abincin da ake ci a kasar nan. | |
Sakamakon binciken ya nuna cewa akwai wasu abinci da ake zuba musu sinadari domin hana su rubewa. | |
Binciken ya kuma nuna cewa an fi amfani da wannan sinadari a wake, garin alabo da busasshhen kifi da ake saida wa jama'a. | |
Ana amfani da sinadarin ne domin idan mutum ya gani zai yi sha'awar siya ya yi amfani da shi. | |
Sannan cin abinci dake dauke da wannan sinadari na haddasa cutar daji, ciwon koda, bugawar zuciya da sauran su. | |
An yi kira ga mutanen kasar nan su maida hankali wajen kiyayewa daga amfani da ire-iren wadannan kayan abinci domin kiwon lafiyar su. | |
Idan ba a manta ba wata kwararriya masaniyar Ingancin abinci Grace Olasumbo ta yi kira ga ƴan Najeriya da su guji cin kayan itatuwan da aka nika su da sinadarin Calcium Carbide. | |
Olasumbo ta bayyana cewa Sindarin Calcium Carbide sinadari ne mafi yawan ƴan kasuwa ke amfani da shi wajen nika danyen kayan itatuwa, wato kayan marmari. | |
Bincike ya nuna cewa gajen hakuri da hadama na cikin abubuwan da ke sanya ƴan kasuwa yin amfani da wannan sinadarin domin a cikin kwana daya yake nunar da kayan itatuwa. | |
Olasumbo ta bayyana cewa wani abin da ƴan kasuwa suka kasa ganewa shine amfani da wannan sinadarin don nunar da kayan marmari na yi wa kiwon lafiyar mutane illa matuka. | |
A dalilin haka akan kamu da cututtuka da suka hada da amai da zawo, ciwon ido, gyambon ciki, dajin makogwaro, baki, hanta da sauran su. | |
An wanke shugaban bankin raya kasashen Afrika daga zargi - Freedom Radio Nigeria. | |
Kwamitin kwararru wanda tsohuwar firaministan kasar Ireland Mary Robinson ta ke jagoranta ya wanke shugaban bankin raya kasashen Afirka AfDB Akinwumi Adesina. | |
A cewar kwamitin Mista Akinwumi Adesina ba shi da laifi a zargin cin hanci da ake yi masa. | |
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa, a farkon wannan shekarar da muke ciki ne wani rahoto mai shafi goma sha biyar ya zargi Mista Adesina mai shekaru sittin da laifin nuna fifiko da rashin iya shugabanci da kuma arzuta kansa. | |
Sai dai kwamitin kwararrun da Robinson ta jagoranta tare da babban mai shari'a na kasar Gambia Hassan Jallow da kuma mataimakin shugaban gwamnan bankin duniya mai kula da bangaren nagartar aiki Leonard McCarthy, sun wanke tsohon ministan noman na Najeriya daga dukkannin zarge-zarge da ke kansa. | |
A baya dai kasar Amurka ce ta dage kan dole sai an binciki mista Adesina kan zargin, biyo bayan wankeshi da hukumar gudanarwar bankin na AfDB ta yi, lamarin da ya sa a kafa kwamitin kwararru don gudanar da binciken kan badakalar. | |
COVID-19 Ta Hana Taron Yakin Neman Zaben Trump a Florida. | |
A jiya Alhamis shugaban Amurka Donald Trump ya sanar cewa ya soke babban taron jam'iyyar Repubican da za a bashi tikitin takara da aka shirya gudanarwa a Jacksonville jihar Florida, a wata mai zuwa, sakamakon karuwar masu kamuwa da coronavirus. | |
Duk da haka za a gudanar da ayyukan babban taron a jihar North Carolina. | |
Trump ya fada a Jacksonville cewa, yin babban taro bai dace a wannan lokaci ba. | |
Shugaba Trump ya maida wani bangare na taron GOP zuwa Florida a watan da ya gabata bayan da suka samu sabani da shugabannin jam'iyar Democrat a jihar North Carolina kan gudanar da taron a rufaffen dakin taro tare da magoya bayansa ba tare da sun sa takunkumin rufe fuska ba. | |
Wasu wakilan jam'iyar Republican kalilan za su hallara a garin Charlotte na jihar North Carolina, don su zabi Trump a hukumance a ranar 24 ga watan Agusta. | |
Trump ya ce zai yi jawabin amincewa a wani tsari na daban. | |
Trump wanda ya kwashe watanni yana nuna halin ko-in-kula game da tasirin annobar, inda a kwanan nan ma ya ce kashi 99 na yawan masu kamuwa da cutar da aka gani sun karu a Amurka, bai za zama da wata illa ba. | |
Buhari Ba Zai Karbi Masu Gaisuwar Sallah Ba. | |
Babban mai baiwa shugaban shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da fadar ta fitar a yau Laraba. | |
Sanarwar ta kuma ce Shugaban ba zai karbi baki a bana ba wadanda suka saba zuwa domin kawo masa gaisuwar sallah. | |
Shehu ya ce an dauki wannan matakin ne sakamakon shawarwari da aka samu daga majalisar koli ta adinin musulunci domin takaita cutar ta Coronavirus. | |
Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma jaddada matakan da majalisar ta ba da shawarar a bi na kaucewa tarurrukan da mutane da dama za su kasance a wuri daya. | |
A bikin karamar sallah da aka yi a wannan shekarar, shugaban ya yi sallar Idinsa a gida tare da iyalansa maimakon zuwa masallaci yadda ya saba yi a kowace shekara. | |
KORONA: An samu karin mutum 322 ranar Lahadi da suka kamu, Yanzu mutum 52,227 suka kamu a Najeriya. | |
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 322 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi. | |
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -130, Bauchi-36, FCT-25, Edo-17, Bayelsa-14 Ogun-14, Oyo-14, Anambra-13, Kaduna-12, Ondo-11, Abia-10, Osun-6 Filato-5, Kwara-5, Kano-4, Ebonyi-3, Sokoto-2 da Borno-1. | |
Yanzu mutum 52,227 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 38,945 sun warke, 1002 sun rasu. | |
Sannan kuma zuwa yanzu mutum 12,280 ke dauke da cutar a Najeriya. | |
Har yanzu dai jihar Legas ce ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 17,894 FCT -4,994, Oyo - 3,050, Edo -2,537, Delta -1,701, Rivers 2,048, Kano -1,708, Ogun - 1,614, Kaduna -2,011 Katsina -771, Ondo -1,512, Borno -740, Gombe - 709, Bauchi - 643, Ebonyi - 960, Filato -2,118, Enugu - 1,043, Abia - 749, Imo - 521, Jigawa - 322, Kwara - 936, Bayelsa - 356, Nasarawa - 396, Osun - 768, Sokoto - 156, Niger - 237, Akwa Ibom - 271, Benue - 430 , Adamawa - 206, Anambra - 194, Kebbi - 90, Zamfara - 78, Yobe - 67, Ekiti - 218 , Taraba- 78, Kogi - 5, da Cross Rivers - 80. | |
Sin Ta Cimma Nasarorin Wadata Jama'arta Da Abinci - Leadership Hausa Newspapers. | |
Abinci shi ne ruhin rayuwar dukkan halittu, ba a iya rayuwa tilas sai da abinci. | |
Wannan ne dalilin da ya sa mahukunta kasar Sin ke kara azama wajen tabbatar da wadata al'ummar kasar da abinci. | |
A cikin shekaru 71 da suka gabata tun bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, kasar ta samu manyan nasarori a fannin wadatar abinci lamarin da ya baiwa duniya mamaki duba da yawan jama'ar kasar wanda a bisa kiyasi ya nuna adadin Sinawa ya zarta biliyan 1.4. | |
Wannan kokari ya taimaka matuka lamarin da ya sa kasar Sin ta bayar da babbar gudunmawar kawar da yunwa a duniya, kamar yadda shugaban hukumar adana hatsi da kayayyakin amfanin gona na kasar Sin Zhang Wufeng ya taba bayyana cewa, tun daga shekarar 1949 har zuwa yanzu, a koda yaushe, Sin tana sanya batun magance yunwa a gaban dukkan ayyukan tafiyar da harkokin kasar. | |
Amma a kwanakin baya, wasu mutane da wasu kafofin yada labaru na yammacin kasashen duniya sun sake "nuna damuwa" kan batun wato ko kasar Sin za ta iya renon al'ummarta da kanta a inuwar bullar cutar numfashi ta COVID-19 a duk fadin duniya? | |
Muna musu godiya kwarai sabo da a kullum suna kula da kasancewar Sinawa a duniyar nan. | |
A karkashin jagorancin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kasar ta cimma nasarar samar da isasshen abinci bisa namijin kokarin da take yi. | |
Batun samar wa Sinawa isashen abinci yana daga cikin manyan ajandojin jam'iyyar JKS mai mulki a kullum. | |
A karshen makon da ya gabata, babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya ba da wani muhimmin umarni na a daina barnata abinci, inda ya yi nuni da cewa, kowa ya sani cewa duk wata kwayar abinci da wahalar aiki ne ake samunta. | |
Ko da yake a wannan shekara tasirin cutar numfashi ta COVID-19 da ta addabi duniya tana kuma kawo illa ga tattalin arzikin kasar Sin, amma kasar Sin za ta iya samar da isasshen abinci ga al'ummarta. | |
Alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar game da yawan kayayyakin gona, musamman shinkafa da kasar za ta samu a wannan shekarar ta 2020 ta nuna cewa, yawan shinkafar da aka samu a kasar a kashin farko a 2020, ya kai ton miliyan 27.29 inda ya karu da ton miliyan 1.08, wato ya karu da 3.9% idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2019. | |
Shi ma Ke Bingsheng, tsohon shugaban jami'ar aikin gona ta kasar Sin ya ce, kasar Sin ta samu manyan nasarori ta fuskar wadata kasar da abinci idan an kwatanta da farkon lokacin aiwatar da manufar yin sauye-sauye a gida da bude kofa ga ketare. | |
Huang Jikun, direktan cibiyar nazarin manufofin aikin gona ta kasar Sin ta jami'ar Peking, ya bayyana a yayin da yake ganawa da wakilin jaridar "The China Science Daily", cewar tsananin kalubale da kasar Sin take fuskanta yanzu shi ne a cikin shekaru 2 ko uku masu zuwa, ko kasar Sin za ta iya rage yawan alkama da shinkafa da ta adana a dakunan adana hatsi. | |
Yanzu yawan hatsin da kowane ya samu ya kai kilogram 474 maimakon kilogram 400 da ya kamata kowane mutumin kasashen duniya ya samu a duk shekara. | |
Kuma yanzu kasar Sin ta kan shigar da wasu kayayyakin gona miliyoyin ton domin renon dabbobin gida kawai. | |
Sabo da haka, ya kamata wadanda suke nuna damuwar batun su kwantar da hankulansu, su yi wanka su shiga barci, ko su mai da hankulansu kan harkokin cikin gidan kasarsu ke nan. | |
Su Sinawa suna iya renon kansu da abincin da suke samarwa da kansu. | |
Abun da ya sa na gurfanar da Ganduje a gaban kotu - Abba K. Yusuf - Freedom Radio Nigeria. | |
Dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ya bayyana dalilan sa na gurfanar da gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da wasu ƴan kasuwa a gaban babbar kotun jiha. | |
Abba Kabir ya bayyana hakan ne, ta bakin lauyan sa, Bashir Tudun wuzirci, wanda ya ce, ya shigar da karar ne, bisa zargin mallakawa wasu ƴan kasuwa gine-ginen gwamnati da al'ummar jihar Kano ke amfana da su. | |
Baya ga gwamnantin Kano da ƴan kasuwar, Abba Kabir Yusuf ya kuma yi karar ma'aikatar ayyuka da gidaje da sufuri ta jiha da atoni janar kuma kwamishinan shari'a na Kano da kuma hukumar kula da filaye ta jiha. | |
Abba Kabir Yusuf ya zargi gwamnatin Jihar Kano da mallakawa wasu daidaikun mutane tsohon otal din Daula da yanzu haka ke karakashin kulawar jami'ar kimiyyar da fasaha ta garin Wudil da kuma filin tashar Shahuci, da ya ce hakan ya ci karo da tanadin dokokin kasar nan. | |
Abi cancanta kawai, a wancakalar da tsarin karba-karba a 2023. | |
Dan Uwa kuma babban aminin shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Mamman Daura ya bayyana cewa salon mulki na karba-karba da ake yi a Najeriya ya zama tsohon yayi yanzu. | |
Mamman Daura ya ce Najeriya ta riga ta yi kwarin da yanzu ta watsar da tsarin karba-karba a maida hankali wajen zabo wanda ya fi cancanta a 2023. | |
BBC Hausa ta wallafa hira da tayi da Mamman Daura wanda a ciki ne ya bayyana haka. | |
Wannan tsari na karba-karba wajen zaben shugaba a Najeriya bai haifar da ɗa mai ido ba wanda aka fara tun a 1999. | |
Maimakon haka Daura ya ce a maida hankali wajen tsaida wanda ya cancanta ne ba sai an bi wannan tsari na karba-karba ba. | |
Sai dai kuma ƴan kabilar Igbo, wato Inyamirai sun maida wa Daura martani bisa wannan kalamai na sa. | |
Sun ce sai da shi da dan uwansa shugaba Buhari suka kwankwadi romon mulki ta hanyar karba-karba sannan ne zai fito yanzu yace yana bada shawarar kada a bi haka a 2023. | |
Shi kansa Buharin ba ya fi duka ƴan Najeriya bane aka zabe shi. | |
Haka manyan hafsoshin tsaron kasar nan da suke zaune daram a kujerun su shekaru da dama ba a cire su ba, suma ay ba sun fi sauran iya aiki bane. | |
Martanin Inyamirai. | |
Wata guguwar iskar siyasar shugabancin Najeriya da ta kada a ranar Laraba, yayin da Kungiyar Kare Muradin Kabilar Igbo Zalla, Ndigbo ta ragargaji Mamman Daura, saboda furucin kwalelen shugabancin Najeriya da ya yi wa kabilar Inyamurai. | |
A cikin wata tataunawa da aka yi da Daura, wanda dan uwan Shugaba Muhammdu Buhari ne, ya ce za a yi tsarin shiyya-shiyya ne a zaben shugaban kasa da za a yi a 2023. | |
A kan haka ne tun kalaman sa ba su gama karade soshiyal midiya ba, Ndigbo ta gaggauta fitar da sanarwar yi wa Mamman Daura tir, ta ke da kiran sa algungumin kitsa bangaranci. | |
A wata sanarwar da Ndigbo ta fitar a ranar Laraba, kungiyar ta ƴan kabilar Igbo zalla ta Yankin Kudu, kuma a kudun ma Shiyyar Kudu maso Gabas za a bari su fito da shugaban kasa a zaben 2023, wato kabilar Igbo kenan. | |
Kakakin Shugaban Kungiyar Kabilar Igbo Zalla, Emeka Attamah ya ce kalaman Mamman Daura kamar kwalelen shugabancin Najeriya a 2023 ya ke yi wa kabilar Igbo. | |
In banda hadama, me ya hana Mamman Daura yin maganar karba-karba tun a 2019. | |
Sun game kai sun kori Jonathan, yanzu kuma Daura na yi wa yankin kudu kwalelen wanda zai shugabanci Najeriya a zaben 2023. | |
Sai da ya gama tatsar abin da ya tatso daga hannun dan'uwan sa mai shugabancin kasar nan a yanzu, sannan kuma zai fito mana da wani batu ba wanda muka sani ba na karba-karba a 2023. | |
Kamata ya yi a matsayin sa na dattijo ya rungumi gaskiya ya rike ta da kyau. | |
Ba wai ya fito jagaliyancin furucin shugabancin kasar nan a 2023 ba, jagaliyancin kuma na nuna son kai da son rai. | |
Zauren Tattaunawar VOA Da Aka Yi Kan Fyade. | |
Batun cin zarafin mata da kananan yara ta hanyar yi musu fyade ya zama ruwan dare a arewacin Najeriya inda aka yi ta samun rahotanin da ke nuna yadda ake tauyewa yara hakkinsu. | |
Mutane daga bangarori da dama ne suka halarci zauren a ranar 23 ga watan Yuli domin tattauna yadda lamarin ke kara muni a kasar da kuma yadda ya kamata a shawo kansa. | |
Mahalarta zauren sun danganta matsalar da abubuwa kamar tallar da ake sa yara mata da kuma sakacin wasu iyaye. | |
Daya daga cikin iyaye mata da suka halarci taron Hajiya Fathi'a Sha'ibu, uwargidan tsohon gwamnar jihar Filato da Neja a zamanin mulkin marigayi Sani Abacha, ta bayyana talauci a matsayin daya daga cikin abubuwan da ke sanya iyaye na dora wa yaransu talla. | |
Hajiya Maryam mamman Nasir shugabar wata kungiyar da ke fadi-tashi wajen ganin an yi yaki da wannan masifa, ta ce "na farko ya kamata mu zagaya mu ilmatar da iyaye mata kan illolin barin yaransu su fita talla, domin sai yaro ya fita ne ma za a ganshi har a yi masa illa". | |
Za mu kuma yi kira ga Malamai su fara wa'azi da kakkausar murya ga iyaye da kuma 'yan uwan da ke yi wa yaransu da kannensu fyade. | |
Shi kuwa dan majalisar tarayya da ke wakiltar mazabar Maiyama, Koko da Besse na jihar Kebbi Honorable Shehu Mohammad, ya bayyana takaicin al'amarin da kuma goyon baya wajen ganin an saka doka mai tsauri da za ta hukunta duk wanda aka kama da laifin fyade a kasar. | |
Daga karshen Hajiya madina Dauda da Nasiru El-hikaya da suka jagoranci zauren taron sun mika godiya ga wadanda suka samu halartar taron a madadin hukumar VOA da suka amshi goron gayyatarsu. | |
Gudunmawar 'Arewa Media Writers' Ga Hadin Kan Arewa. | |
Kafafen sada zumunta na zamani irin su Facebook, Twitter, WhatsApp, Instagram, Bakandamiya da sauran su, sun dade suna taka rawa wajen samar da zaurukan tattaunawa, hadin kai da zumunci tsakanin al'ummomin duniya daban daban, tare da isar da sakonni, labaru, da yada manufofi na siyasa, ilimantarwa da kasuwanci. | |
Matasa a Nijeriya sun shiga cikin wannan sabuwar fasaha ta amfani da zaurukan sada zumunta, domin tafiya da zamani, da ba da tasu gudunmawa ko tofa albarkacin bakin su a sabgogin da suka shafi rayuwar su. | |
Za mu iya cewa, wadannan zauruka sun kawo mana cigaba masu yawa da matasan Arewa ke amfana da su a harkokin kasuwanci, tattalin arziki, ilimi da siyasar yankin. | |
Wasu da dama suna cin abinci ta hanyar rubuce rubuce da isar da sakonni a yanar gizo, sun samu ayyukan yi ko kuma sun bunkasa ayyukan da suke gudanarwa. | |
Sai dai abin takaici ne ganin yadda wasu matasan a maimakon su yi amfani da wannan dama wajen cin moriyar cigaban da aka samu, sai aka samu wasu da ke biye wa gurbatattun yaran kudancin kasar nan wadanda suka yi fice a duniya wajen damfarar jama'a, a ciki da wajen kasar nan, ko kuma yin rubuce rubuce na batanci da cin zarafin mahukunta da magabata. | |
Abin da ke nuna rashin wayewa, a ci gaban rayuwar matasan kasar nan ke ciki. | |
Zuwan kungiyar Arewa Media Writers a Kasar nan babban abin alheri ne, domin samar wa matasan Arewa mahanga, kyakkyawar alkibla da tsaftace abubuwan da matasa suke yi a Soshiyal Midaya, ta yadda za su zama suna rubuce rubuce masu ma'ana da yada manufofin al'ummar Arewa. | |
Ya zama wajibi mu bai wa wannan kungiya hadin kan da take bukata, domin cimma manufofinta na alheri, da za su kawo alfanu ba kawai ga yankin mu na Arewa ba, har ma da Nijeriya baki daya. | |
Ina mai shawartar matasan mu, musamman masu amfani da zaurukan sada zumunta su zo mu hada kai domin kare mutuncin Arewa da ƴancin ta, mu kuma samar da tsarin da zai zama ya kawo sauyi ga kowa. | |
Kamar yadda shugabannin mu na Arewa wadanda suka kwanta dama irin su Sardaunan Sakkwato, Firimiyan Arewa na farko Sir Ahmadu Bello, da makusanta sa suka yi burin samar wa al'ummar Arewa. | |
An rawaito cewa, Marigayi madugun yaki da zalunci da talauci Malam Aminu Kano, ya taba fadin cewa, Nijeriya kasa daya ce, amma kowa ya san gidan ubansa! | |
Don haka muke cewa, tabbas a yayin da muke kira ga samar da cigaban kasa da inganta sha'anin tafiyar da mulki, a kowanne mataki, muna kara kira ga hadin kan ƴan Arewa, ba tare da nuna wariyar addini ko kabilanci ba, don kawo wa yankin mu ci gaba. | |
Idan muka yi la'akari da yadda Arewa take a da ba haka take yanzu ba. | |
Don haka ya kamata mu yi amfani basirar da Allah ya bamu wajen ba da gudunmawa da shawarwari, domin samar wa da Arewa gamsashshiyar hanyar farfado da tattalin arzikin ta. | |
Ya kamata Arewa ta samar da hanyoyin kudaden shiga don aiwatar da kasafin kudinta ba tare da ta jira gwamnati tarayya ta bata kudi ba. | |
Bugu da kari in dai har muna son cigaban Arewa, sai mun bada muhimmanci ga ilimi, noma, da yawon bude ido, da kiwon lafiya da kuma kimiyya da fasaha. | |
Ba lailai sai da kudi za mu bada gudunmawa ba, akwai hanyoyi daban daban na yin hakan. | |
Muna ganin ta haka ne Arewa za ta cikawa magabatan mu burin su! | |
Arewa abin alfaharin mu ce. | |
Gwamnati ta ware naira biliyan 126 domin gyara asibitocin kasar nan. | |
Gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 126 daga cikin tsare-tsaren inganta tattalin arzikin kasar nan domin gyara asibitoci a kasar. | |
Asibitocin da za a gyara sun hada da asibitin FMC, wuraren yin gwaje-gwajen cututtuka, sashen kula da masu bukatan kula cikin gaggawa, sashen da ake kebe masu fama da cututtukan da ba a son sauran mutane su Kamu, da asibitocin koyarwa dake jihohin 36 a kasar nan. | |
A shekararun baya ne wasu kawararru a fannin kiwon lafiya suka yi kira ga sassan gwamnati kan hada hannu wajen ware isassun kudade domin inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan. | |
Kwararrun sun yi wannan kira ne a taron samun madafa kan samar da kiwon lafiya mai nagarta wa mutane cikin sauki kuma da aka yi a Abuja. | |
A jawabin sa dan takaran kujerar sanata mai wakiltan Kwara ta Arewa a karkashin inuwar jam'iyyar APC Sadiq Umar ya ce kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta dauki al'amuran inganta kiwon lafiyar kasar nan da mahimmanci. | |
Yace rashin yin haka ne ya sa fannin ke fama da matsalolin rashin kudade inda hakan ya sa take yawan dogaro da tallafin da take samun daga kasashen waje. | |
Umar yace duk da wadannan tallafi da ake samu babu rawar ganin da gwamnatin ta taka a fannin kiwon lafiya inda hakan ya sa suka fara janye tallafin da suke badawa. | |
KORONA: Najeriya ta zarce mutum 53,000 da suka kamu a Najeriya. | |
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 221 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba. | |
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -17, Filato-60, FCT-33, Kaduna-26, Rivers-18, Enugu-9, Kwara-9, Ondo-9, Nasarawa-6, Gombe-5, Anambra-5, Delta-4, Abia-4, Imo-3, Edo-2, Ogun-2, Oyo-2, Osun-2, Bauchi-1 da Kano-1. | |
Yanzu mutum 53,021 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 40,281 sun warke, 1,010 sun rasu. | |
Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,730 ke dauke da cutar a Najeriya. | |
Har yanzu dai jihar Legas ce ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,035 FCT -5,079, Oyo - 3,060, Edo -2,555, Delta -1,719, Rivers 2,108, Kano -1,722, Ogun - 1,633, Kaduna -2,085, Katsina -771, Ondo -1,524, Borno -740, Gombe - 719, Bauchi - 645, Ebonyi - 965, Filato -2,245, Enugu - 1,096, Abia - 759, Imo - 526, Jigawa - 322, Kwara - 945, Bayelsa - 378, Nasarawa - 427, Osun - 771, Sokoto - 156, Niger - 239, Akwa Ibom - 271, Benue - 451, Adamawa - 217, Anambra - 207, Kebbi - 92, Zamfara - 78, Yobe - 67, Ekiti - 238, Taraba- 87, Kogi - 5, da Cross Rivers - 82. | |
Mutanen da yunwa za ta kashe a Afrika za su haura wadanda Coronavirus ta kashe -IFAD. | |
Cibiyar Bunkasa Harkokin Noma ta Duniya (IFAD), ta bayyana cewa akwai wasu karin akalla mutane milyan 23 da yunwa za ta kassara a Kasashen Yankin Saharar Afrika, a cikin shekarar 2020. | |
Shugaban IFAD Gilbert Houngbo ne ya bayyana haka a wurin taron Zauren Tattauna Tattalin Arziki, na World Economic Forum. | |
Taron na bana an tattauna matsalar Hanyoyin Tattalin Abinci A Afrika, a lokacin annobar Coronavirus. | |
Houngbo ya ce nazari, hasashe da kirdadon yadda ake fuskantar matsalar abinci, ya nuna cewa a shekarar 2020 wadanda yunwa za ta kashe a yankin Afrika za su zarce wadanda cutar Coronavirus ta kashe, nesa ba kusa ba. | |
IFAD dai cibiya ce wadda ta shahara wajen tallafa wa mutanen da ke zaune a karkara wajen bunkasa noma, kara samar wa ƴaƴan su abinci mai gina jiki da kuma samar wa kan su kudaden shiga ta hanyar noma. | |
Houngbo ya ce Coronavirus ta nuna cewa akwai gagarimar matsalar tsarin samar da abinci, raba shi da kuma gyarawa. | |
Manoma da dama na kokawa da yadda ba su iya samun takin zamani saboda dokar hana zirga-zirga. | |
Sannan kuma ba su iya zuwa gona kuma wadanda suka noma amfanin gona na sayarwa, an rufe kasuwanni ballantana su rika sayar da amfanin gonar su. | |
Rahoton ya kara da cewa a shekarar 2019 yunwa ta kassara mutum milyan 135 a duniya, wadanda milyan 73 daga cikin su sun fito daga Afrika, cikin kasashe 36. | |
A Arewacin Najeriya yunwa ta kassara mutum milyan 5 a 2019. | |
NNPC Ta Samu Dala Miliyan 378.42 Daga Gas A Yuni. | |
Kamfanin mai na Nijeriya (NNPC) ya bayyana cewa, yawan kudaden da ya samu wajen fitar da danyan mai da gas a watan Yuni dai sun kai dala miliyan 378.42, inda ya samu dala miliyan 133.16 a watan Mayun wannan shekarar da muke ciki. | |
Kamfanin mai na Nijeriya ya kara da cewa, wannan shi ne karin kudaden haraji da aka samu tun lokacin da cutar Korona ta barke a Duniya, wacce ta haddasa saka dokar hana zirga-zirga da kuma faduwar farashin mai a kasuwar Duniya. | |
A cikin wata takarda da babban jami'in hulda da jama'a na kamfanin, Dakta Kennie Obateru, ya rattaba hannu ya ce, NNPC ta bayyana cewa, a cikin watan NNPC ya kara da cewa, ya samu yawan kudade daga danyan mai da gas wadanda su ka kai dala biliyan 4.60 a tsakanin watan Yunin shekarar 2019 da watan Yunin shekarar 2020. | |
Hakazalika, kamfanin ya bayyana cewa, ya samu yawan kudaden da su ka kai dala miliyan 378.42 daga danyan mai da gas wanda ya fitar zuwa kasashen ketare a watan Yunin shekarar 2020. Inda ya samu dala miliyan 133.16 a cikin watan Mayun shekarar 2020. | |
Kamar yadda kamfanin ya bayyana a baya dai, an samu dala miliyan 230.65 daga danyan mai, yayin da aka samu dala miliyan 75.97 da miliyan 71.80 a jumlance. | |
Rahoton kudaden da kamfanin ya bayar a watan Yunin shekarar 2020, shi ne rahoto na 59 wanda kamfanin ke wallafa wa duk wata. | |
Rahoton ya bayyana cewa, a tsakanin watan Yunin shekarar 2019 da watan Yunin shekarar 2020, an samu zunzurutun kudade wadanda su ka kai na dala biliyan 4.60 daga danyan mai da kuma gas. | |
Haka kuma rahoton ya nuna cewa, domin tabbatar da samun nasarar kaiwa da rarraba man fetur a fadin kasar nan a watan Yunin shekarar 2020, kamfanin NNPC ya raba litar mai wanda ya kai lita biliyan 1.34. | |
Rahoton ya ce, litar mai miliyan 950.67 aka sayar a watan Mayun shekarar 2020, sakamakon dokar hana zirga-zirga da aka saka a cikin kasar nan, wanda ya kawo nakasu da harkokin kasuwanci. | |
A cewar rahoton, a watan Yunin shekarar 2020, an sayar da litar man fetur sama da miliyan 1.3, yayin da aka sayar da litar gas miliyan 5.10, sannan an samar da litar kalanzir miliyan 1.65, wanda aka rarraba su a fadin kasar nan gaba daya. | |
Gaba daya dai a tsakanin watan Yunin shekarar 2019 zuwa watan Yunin shekarar 2020, an sayar da sama da litar mai biliyan 19.104 na mai, ya yin da aka sayar da gas sama da lita biliyan 18.9 ko kashi 99.36. | |
Rahoton ya bayyana cewa, dukkan jimillar kudaden da aka sayar da man a watan Yunin shekarar 2020 na naira biliyan 134.22, idan aka kwatanta shi da na watan Mayun shekarar 2020 wanda aka samu naira biliyan 92.58. yawan kudaden dai da aka samu a tsakanin watan Yunin shekarar 2019 da na watan Yunin shekarar 2020 sun kai naira tiriliyan 2.267, wanda aka samu na kashi 99.12. | |
A watan da aka gudanar da wannan kididdigar dai, an samu fasa bututun mai guda 33 wanda ya kai na kashi 11, wanda ya ragu a watan Mayun shekarar 2020 wanda aka samu 37. | |
Rahoton bayanan kudade na kamfanin NNPC na watan Yunin shekarar 2020, ya bayyana cewa, kamfanin ya hada kai da mutanen gari da masu ruwa da tsaki ta yadda za a shawo kan fasa bututun mai a fadin kasar nan. | |
EU za ta shiga tsakanin Turkiyya da Girka kan tekun Bahar Rum. | |
Ministocin kungiyar tarayyar Turai EU sun kudiri aniyar shiga tsakani, bayan da wata kiki-kaka ta kunno kai tsakanin Turkiyya da kasar Girka kan tekun Bahar Rum. | |
An sanya ranar Alhamis mai zuwa domin tattauna yadda za a kawo karshen ta da jijiyoyin wayar. | |
Tuni dai shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan a ranar Larabar nan ya murza gashin baki, inda ya ce babu wanda za su daga wa kafa kan batun tekun, saboda mallakinsu ne. | |
Kuma a shirye suke wajen daukar ko wane irin mataki da ya dace kama tun daga na siyasa har zuwa na soji. | |
A nata bangaren ministar tsaron Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer ta Jamus ta fara duba yadda za a warware bakin zaren lamarin, inda ta ce shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta shirya ganawa da shugaba Erdogan a Juma'a mai zuwa ta wayar tarho. | |
Shugaba Buhari ya Taya Dan Najeriya Murnar Nada Shi Minista a Canada. | |
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa Kaycee Madu wani dan Najeriya murnar nada shi matsayin Ministan shari'a kuma babban jami'in shari'ar gwamnatin lardin Alberta a kasar Canada. | |
A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai ba Shugaban Najeriya shawara na musamman, Femi Adesina. | |
Madu ya yi abun tarihi a matsayin dan Afrika da aka nada Ministan lardi a tarihin Canada, kuma shine Sakataren lardi da ke rike da hatimin lardin Alberta. | |
Shugaba Buhari ya bayyana wannan karramawar a matsayin "gagaruma a tarihi", ya na mai cewa hakan ya sake karrama ƴan Najeriya a matsayin masu hazaka, da ke bayyana kansu ta fannonin rayuwa daba-daban. | |
Shugaban ya ce a matayinsa bakar fata na farko da aka ba mukamin Ministan shari'a kuma Attoni janar a Canada, Madu ya shiga littattafan tarihi, Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya, a gida da waje, da su ci gaba da kasancewa wakilan kasarsu na gari. | |
RASHIN TSARO: An kashe mutum 415 cikin watan Yuli a Najeriya. | |
An kashe akalla mutum 415 a kashe-kashe daban-daban a Najeriya cikin watan Yuli, kamar yadda wani rahoto da wata kungiya mai suna Nigeria Mourn ta wallafa. | |
Cikin Rahoton Tashe-tashen Hankula a Watan Yuli, Nigeria Mourn, wadda aikin da ta sa gaba a kasar nan shi ne bibiya da kididdigar kashe-kashen gilla a fadin Najeriya, ta ce wannan adadi da ta lissafa, kididdiga ce ta jihohi 21 kadai daga jihohi 36 na kasar nan da Abuja. | |
Wannan kungiya ta kan binciki rahotannin da kafafen yada labarai sahihai suka buga, sai kuma bayanan da ta tattara daga bakin iyalai, ƴan uwa ko majibintan wadanda aka kashe da ba a buga rahotannin su a jaridu ba. | |
Rahoton baya-bayan nan da kungiyar ta buga sun nuna jihohin Barno, Kaduna da Katsina ne aka fi yi wa mutane kisan-gilla a Najeriya, a cikin watan Yuli. | |
Ga yadda rahoton ya lissafa yawan mutanen da aka kashe a jihohin 21 da ta kididdige. | |
Kaduna - 139 Barno - 113 Katsina - 80 Kogi - 17 Nasarawa - 13 Taraba - 10 Benuwai - 9 Ebonyi - 8 Zamfara - 7 Filato - 5 Edo - 2 Akwa Ibom - 2 Lagos - 2 Oyo -1 Ogun - 1 Bayelsa - 1 Delta -1 Kebbi - 1. | |
Rahoton ya ce mutum 185 duk mahara da ƴan bindiga ne suka kashe su. | |
Yayin da Boko Haram suka kashe mutum 123. | |
Makiyaya masu dauke da manyan bindigogi sun kashe mutum 67, wasu 26 kuwa wurin rikicin kabilanci aka yi musu kisan-gilla. | |
An kashe mutum shida a rikicin tankiya, wasu shida kuma jami'an tsaro suka yi musu kisan gilla kafin a gurfanar da su kotu. | |
Akwai kuma mutum biyu da suka rasa rayukan su a hannun fadace-fadace na kungiyar asiri. | |
283 da aka kashe fararen hula ne, sai jami'an tsaro har 132 aka kashe. | |
Rahoton baya na wannan kungiya ya nuna an kashe mutum 731 a cikin watan Yuni, cikin watan Mayu kuwa an kashe mutum 356. | |
Yayin da ake ci gaba da yi wa jama'a kisan-gilla, Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya nemi Gwamnatin Tarayya ta amince yan Najeriya su mallaki lasisin mallakar bindiga. | |
Dama kuma Sanata Kabiru Marafa ya taba yin irin wannan kira cikin 2018, a lokacin ya na Sanata mai wakiltar Zamfara. | |
Ba Buhari ne kaɗai da haƙƙin tsaron ƙasar nan ba - Nanono - Freedom Radio Nigeria. | |
Ministan Noma na ƙasa Alhaji Sabo Muhammad Nanono ya ƙalubalanci gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi kan matsalar tsaro a Najeriya. | |
A wata zantawa da ministan ya yi da sashen Hausa na Radio France International kan yadda matsalar tsaro ta shafi ɓangaren noma. | |
Ministan ya ce "maganar gaskiya ba gwamnatin tarayya ce ta ke da haƙƙin tsaron wannan abu kawai ba, gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi, idan ka tafi ƙasa har Dagatai da masu unguwanni, ya aka yi suka sake suka bar wannan yanayi na tsaro ya zama abin da ya zama, amma kowa ya tashi sai ya ce gwamnatin tarayya". | |
Eh gwamnatin tarayya tana da haƙƙin ta tsare rayuwar jama'a, amma ai su waɗannan da suke kusa da waɗannan mutanen su ya kamata tun da farko ma su fara maganar cewa muna ganin muna da matsala a kan waɗannan abubuwan. | |
Alhaji Sabo Nanono ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya tana iyakar ƙoƙarinta wajen bunƙasa noma da samar da abinci a ƙasar nan. | |
Shugaba Trump Ya Sanya Hannu a Dokar Rage Farashen Magunguna. | |
Ranar Juma'a 24 ga watan Yuli Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu a wasu dokokin Shugaban kasa guda hudu da zimmar rage kudaden da Amurkawa ke kashewa kan magungunan da likitoci ke rubuta musu, a yayin da ya ke fuskantar gwagwarmayar neman sake cin zabe da kuma caccaka akan yadda ya tunkari annobar COVID-19 a kasar. | |
Da ma a baya Trump ya ce zai yi kusan dukkan sauye sauyen da dokar wadda ya sanya wa hannu a ranar Juma'a ta kawo, amma wannan ne karon farko da aka sanya wa dokar hannu. | |
Daya daga cikin dokokin za ta bada dama a shigo da magungunan da likitoci ke rubutawa masu rahusa daga kasashe kamar Canada a hukumance, yayin da wata dokar kuma za ta bukaci kamfanonin da ke sarrafa magunguna su rage farashensu, a cewar Trump. | |
Wata dokar kuma na bukatar a rage farashen allurar insulin yayin da doka ta hudu, wadda ta yiwu ba za a aiwatar da ita ba idan aka samu nasara a ganawar da ake da kamfanonin magunguna, za ta bukaci tsarin Inshorar Medicare ya sayi magunguna a farashen da sauran kasashe ke saye, a cewar Trump. | |
Dan Najeriya Ya Samu Lambar Yabo A Gasar UNICEF. | |
Matasa 80,000 ne daga Najeriya suka shiga wani shiri da Asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, ya ɗauki nauyi na ƙirƙirar wata fasaha kan annobar COVID-19 da za a samar da mafita ga al'umma akan cutar, da suka kira "UNICEF COVID-19 Innovation Challenge". | |
Waɗanda suka samu lambobin yabo daga Najeriya sun fara daga ƴan shekaru 14 zuwa 35. | |
Daya daga cikin matasan mai suna Chukwuma Nwachukwu ɗan shekaru 28, ya gabatar da yadda za a yi amfani da hasken rana domin samar da ruwa don taimakawa wajen yaƙi da ƙwayar cutar. | |
Fanfon da ya ke amfani da hasken rana da Chukwuma Nwachukwu ya ƙiriƙira ya yi nasara a makon farko na fara gasar. | |
Chukwuma Nwachukwu ya ce, burin sa shi ne samar da tsaftataccen ruwan sha ga al'ummomin garin Abuja da ba su da damar samun ruwa mai tsafta. | |
Nwachukwu yana cikin dubbun matasa 'yan Najeriya da suka shiga shirin "UNICEF COVID-19 Innovation Challenge" wanda aka ƙaddamar a watan Mayu, aka kuma ci gaba har tsawon makonni shida. | |
UNICEF ta ce, sabbin ƙirƙire-ƙirƙiren sun nuna yadda matasa za su iya bayar da tasu gudummawa sosai lokacin da aka shiga mawuyacin lokaci. | |
Kimanin ƴan Nigeria miliyan 60 ne, ko kusan kashi ɗaya bisa uku na yawan ƴan kasar, ba sa samun tsaftataccen ruwan sha, a cewar Hukumar ba da tallafni ruwan sha. | |
Dattawan Kano Sun Kai Karar Ganduje Wajen Buhari - Leadership Hausa Newspapers. | |
Gamayyar kungiyoyin rajin kare mutuncin mutanen Kano ta kai karar Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan yunkurinsa na ciyo bashi daga wani bankin kasar China domin gina hanyar layin jirgin kasa. | |
Gamayyar kungiyoyi fiye da 15 karkashin inuwar Kano Forum ta bayyana abin da ta kira katafaren bashin da gwamnatin Ganduje ke son ciyowa domin gina kashin farko na layin jirgin kasa a birnin Kano a matsayin abin da ba shi da amfani ganin manyan kalubalen da ke gaban jihar. | |
Kungiyar ta yi zargin cewa Gwamna Ganduje zai ciyo bashin yuro miliyan 684, wato kimanin naira biliyan dari uku wanda suka ce sai an shekara 50 gwamnatin ba ta gama biyan bashin ba. | |
Shugaban kungiyar Alhaji Bashir Othman Tofa ya ce Abu ne da kusan ba zai yiwu ba a ce jihar Kano ta ɗauki nauyin wani bashi fiye da wanda aka riga aka jibga ma ta a baya. | |
Yanke Hukunci Kan Fyade A Nijeriya Ne Kadai Mafita -Maigidaje. | |
Wani mai fada aji a cikin alumma dake a jihar Kaduna Alhaji Aliyu Maigidaje ya yi nuni da cewa, yanke hukuncin kisa kan wanda aka kama da yin fyade a kasar nan, musamman a Arewacin NIjeriya shi ne kawai mafita. | |
Alhaji Aliyu Maigidaje ya sanar da hakan ne a hirarsa da Leadership A yau a Kaduna, inda ya kara da cewa, matukar hukuma ta tabbatar da hakan bayan yin bincike, yanke hukuncin kisan shi ne kawai mafita. | |
Ya kara da cewa, yanke hukuncin zai rage yawan lamarin na fyade da za a iya samun sauki, amma babban saukin shi ne mu gyara zukatan mu. | |
Alhaji Aliyu Maigidaje ya ce, yace a masayin mu na jinsin Musulmai mu yiwa Allah mu yiwa Annabi mu tsaya mu gyra zukatan mu, domin a kullum mutum bai san randa zai mutu ba. | |
Yace abin kunya ne a ce cikakken da namiji baligi ko tsoho a ce ya samu yar karamar yarinya ko yar wata uku, yar shekara uku ko biyar ya yi mata a fyade. | |
Ya ci gaba da cewa, tsakani da Allah, ba za mu dinga zagin shugabanni, ko sarakunan kasa, inda ya yi nuni da cewa, babu yadda za a yi kasa ta samu ci gaba idan ana samun irin wannan badaƙala. | |
Ya kara da cewa, shi yasa gashi nan muna cikin kunci da wahala a cikin kasa, domin kasar ta ki ci gaba, su kansu Sarakauna da Gwamnononi da shugaban kasa, sun rasa yadda za su yi da lamarin. | |
Ya kara da cewa, sai sun dinke waccan barakar sai kuma wata ta bullo a saboda haka, ya zama wajbi mu gyara zukatan mu don Allah ya kawo mana mafita kan lamarin na fyade. | |
Ya sanar da cewa, ko da suna yi ne domin tsafi, ya kamata komai su fauwalawa Allah domin shi ne ke yaye dukkan wani bakin ciki da talauci ga alumma. | |
A cewarsa, duk halin da mutum ya shiga, Allah na sane da kai ba abinda za ka yi, sai istingifari da hailala kuma kullum ka dinga tunanin za ka mutu kuma kullum ka dinga tunanin kaima kana da baya, in kaima aka yiwa abinda ka Haifa fa. | |
Ya yi nuni da cewa, yan sanda a hukumance suma suna yin iya kokarin su domin suna tura irin wadanda ake zargi da yin fyade zuwa Kotukuma Alkali na yin iya nasu kokarin wannan abune da da ya zamo wata masifa, a yankin mu na Arewacin Nijeriya da kuma a cikin kasa. | |
Ya yi kira ga musamman iyaye dasu dinga sanya ido sosai kan yayansu, inda ya buga misali da tallace-tallacen da yaya mata iyayen su ke dora masu hakan na kara kawo matsalar. | |
Ya ce, wasu iyayen basa bibiyar rayuwar yayansu na ko sunje makaranta ko basu je ba ko sun dawo gida kan lokaci ko basu dawo ba, inda ya kara da cewa, laifin ta wani bangare akwai sakacin wasu iyayen domin ya kamata su sani cewar, Allah ne ya basu yayan kuma gobe kiyama zai tambaye su kan wacce irin tarbiyya suka yiwa yayansu. | |
Jimillar Wadanda Suka Kamu Da COVID-19 a Najeriya Ya Doshi 40,000. | |
Hukumar NCDC mai kula da cututtuka masu yaduwa a Najeriya ta ce an samu karin mutum 591 da suka kamu da cutar COVID-19 a ranar Juma'a 24 ga watan Yuli. | |
A sanarwar da ta fidda a shafinta Twitter a daren ranar Juma'a, hukumar ta ce jihar Oyo ta samu karin mutum 191 yayin da jihar Lagos da ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar a fadin kasar ta samu mutum 168. | |
Sauran jihohin sun hada da birnin tarayya Abuja inda aka samu mutum 61, sai Ondo 29, 26 a Osun, 24 a Ebonyi, 23 a Edo, 14 a Ogun, 13 a Rivers, 12 a Akwa Ibom, 10 a Kaduna, 6 a Katsina, 4 a Borno. | |
Jihohin Delta, Ekiti da Imo kuma mutum 3 kowannensu, sai kuma 1 a Niger. | |
Gaba dayan adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar yanzu ya kai 39,539, an kuma sallami mutum 16,559 bayan haka mutum 845 suka mutu. | |
Gwamnati ta sami sama da biliyan 651 a matsayin kudaden shiga. | |
Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce gwamnatin tarayya ta samu kudaden shiga daga bangaren harajin kayayyaki wato VAT cikin watanni shida na farko na wannan shekara da suka kai naira biliyan dari shida da hamsin da daya da miliyan saba'in da bakwai. | |
A cikin wani rahoto da hukumar ta NBS ta wallafa a website dinta, rahoton ya nuna cewa, adadin ya zarce wanda aka tattara a wa'adi irin wannan na watanni shidan farko a shekarar da ta gabata, wanda ya tsaya akan naira biliyan dari shida da miliyan casa'in da takwas. | |
Rahoton ya nuna cewa, an samu karin kaso takwas da digo biyar idan aka kwatanta da na bara. | |
Hukumar kididdiga ta kasar ta kuma ce bangaren kwararru shine ya fi samar da kudade masu yawa da ya kai naira biliyan casa'in da biyar da miliyan casa'in da biyu. | |
Sai bangaren masana'antu da aka tattara harajin na kayayyaki da ya kai naira biliyan sittin da bakwai da miliyan sittin da uku. | |
Haka zalika bangaren kasuwanci ya samar da naira biliyan talatin da daya da miliyan goma. | |
Sai kuma bangaren masaku da jima da kayyakin asibiti da sabulai da sauransu da suka samar da harajin na VAT da ya kai sama da naira biliyan daya da miliyan dari biyu da saba'in da biyar. | |
Manoman Shinkafa A Biniwe Na Tsammanin Girbi Da Wuri A Kakar Bana - Leadership Hausa Newspapers. | |
Manoman shinkafa a Jihar Biniwe su na tsammanin yin girbi mai yawa kamar watanni biyu bayan shuka. | |
Wasu daga cikinsu da aka tattuan da su a Makurdi sun bayyana fatan cewa girbi zai kasance a kowane lokaci tsakanin Oktoba da Nuwamba. | |
Wani karamin manomi a garin Mbatiab-Gboko na jihar, Titus Atondo, ya ce, ya shuka shinkafar ta sa ne a wani yanki mai girman hekta biyu a watan Yuli. | |
Atondo ya ce ya samo iri daga kasuwa a yankinsa kuma suna cikin rukuni biyu na CP da shinkafa OC yayin da yake amfani da sinadarin Dazzle don share filaye domin dasa shuki da takin. | |
A cewar Titus Atondo, kalubale na noman shinkafa a cikin karkara irin su maina suna da yawa saboda mun dogara sosai kan aikin kwadago kamar yadda kwastomomi ba sa iya samun hanyoyin gonar. | |
Titus Atondo ya kara da cewa, muna daukar mutane da za su yi aikin gona tun daga matakin kasa har zuwa girbi, inda ya kara da cewa, wannan ya gaji kuma yana da yawa. | |
Atondo ya ce dukkan kudaden da aka kashe a gonarsa wanda a yanzu suke a yanzu sun hada da shuka, sharewa, aikace-aikacen takin zamani da kuma ana sa ran girbin su ya kai N2020,000. | |
Titus Atondo ya ci gaba da cewa, amma, ya na tsammanin akalla jakar buhu 50 a matsayin girbi daga kadada biyu da watakila za a sayar a farashin Naira 29,000 a kowace jaka 100k. | |
Shi ma wani babban manomi shinkafa, Bitalis Tarnongu, ya dasa shuki a watan Yuni zuwa Yuli a kadada 274 na gonar wanda farashin ya tsaya a Naira 14, 500 a kowace kadada yayin da filin kasa ke biyan Naira 25,000 a hectare. | |
Ya shuka iri 44 (Supi) da Faro 61 (OC) iri da aka samu daga Majalisar Tsararrun Abubuwan gona ta kasa (tsaba) kuma wasu sun samo asali daga kamfanin Olam Nigeria. | |
Ya kara da cewa, matakan girma a wannan lokaci suna cikin fannoni daban daban yayin da wasu kuma suke cikin shirin kiwo, wasu kuma suna matakin farko na kashe dabbobi kamar yadda aka noma gona a matakai. | |
Tarnongu ya kara da cewa, kalubalen har zuwa yanzu sun hada da na kudi tunda farashin samar da dabbobin da ake zaba yana da tsada kuma farashin kwadago ya karu. | |
Ya ce ana sa ran girbin zai fara a watan Oktoba zuwa Nuwamba. | |
Ya kara da cewa jimlar farashin kayan masarufi a karshen ranar zai zama mafi karancin Naira 246,000 a kowace kadada yayin da ake sa ran samar da zai zuma ton uku wanda zai iya fassara zuwa Naira 360,000 a kan kudi Naira 120 a kowace kilo. | |
Tarnongu baya amfani da magunguna a kan gonar shinkafar sa, a maimakon haka, yana bayar da shawarwari da aiwatar da aikin gona na gargajiya, inda ya kara da cewa, saboda haka, muna amfani da tsire-tsire masu kashe kwari sosai, magungunan kashe kwari da takin mai magani. | |
Shi ma Shugaban kungiyar Manoma ta kasa (AFAN) reshen jihar Benue, kwamrade Aondongu Saaku, ya bayyana fatan cewa yanayin ruwan sama a wannan shekara zai dace da noman shinkafa mai yawa. | |
A cewar Shugaban kungiyar Manoma ta kasa (AFAN) rehen jihar Benue, kwamrade Aondongu Saaku, karin manoma sun shiga harkar noman shinkafa a karshen wannan shekara saboda matsalar cutar Korona wacce ta hana mutane da yawa barin ofisoshi tare da kasancewa a gonakinsu. | |
Ya ce, A bana bana za ta girbi kashi 20 cikin 100 na abin da ake samarwa a shekarar 2019 wanda aka kimanta sama da tan miliyan daya. | |
A cewarsa, a yanzu haka masu tattara bayanan suna daukar kididdigar manoma iri daban-daban kuma idan har aka kammala aikin, za'a tantance yawan manoman shinkafa a jihar. | |
Shugaban kungiyar Manoma ta kasa (AFAN) reshen jihar Benue, kwamrade Aondongu Saaku wanda ya ce, ya noma kadada uku na gonar shinkafa, ya lura cewa wasu manoma sun shuka shinkafar a watan Yuni yayin da wadanda ke nomar gajeren lokaci suna yin hakan a daidai lokacin girbi da ake sa ran a karshen Nuwamba ko farkon Disamba. | |
Shugaban na AFAN ya kara da cewa manoman shinkafar suna amfani da kayan masarufi ne wajen kashe ciyayi masu tsufa, da kebabbun sinadarai, da magungunan kashe kwari. | |
Ya nuna damuwarsa game da kalubalen dabbobin da ke barazanar noman shinkafa, ya kara da cewa manoma na yin shinge, suna sanya igiyoyi tare da share gefan gonakin don magance matsalar. | |
Covid 19: An Raba Takunkumin Kare Fuska Miliyan Biyu da Rabi Kyauta a Kano. | |
Gwamnatin jihar Kano dake yankin arewa maso yammacin Najeriya ta rarraba takunkumin kare fuska da hanci da yawan ta yakai Miliyan Biyu da Rabi. | |
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya jagoranci kaddamar da rabon kayayyakin a wani taro da ya gudana a gidan gwamnatin jihar. | |
Gwamna Ganduje yace amfani da takunkumin a fadin jihar baki daya ya zama dole, biyo bayan irin nasarar da jihar ke samu wajen yaki da bazuwar wannan cuta ta Covid 19 da aka fi sani da Corona Virus. | |
A cewar sa tuni suka sanya masarautun gargajiyar jihar cikin wannan raji, inda hakimai, dagatai da masu unguwanni ke aiki ka'in da na'in wajen tabbatar da dakile bazuwar ta. | |
Bugu da kari, gwamnan yace hakan ya sanya su rarraba takunkumin ga kungiyoyin ma'aikata a jihar. | |
A nasa bangaren mai martaba sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero godiya ya yi ga Allah bisa saukin yaduwar wannan cuta ta Covid 19 da aka samu a jihar Kano. | |
Ya kuma bakaci al ummah da su ci gaba da bawa gwamnati goyon baya wajen kawo karshen cutar tare da yin addu'a wadanda suka rasa rayukan su. | |
Inda ya shawarci jama'a da su yi bukukuwan sallah cikin kula da hanyoyin kare kai daga kamuwa da cutar Covid 19. | |
Ya kamata a ci gaba da bin ka'idojin kare kai da hukumomin lafiya suka gindaya musamman a wuraren sallar idi. | |
"Duk wasu bukukuwan da ba na dole ba ya dace a kaurace musu komai lokaci ne" In Ji Sarkin Kano. | |
Da yake jawabi tunda farko kwamishinan lafiya na jihar Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa yabawa gwamnatin jihar ya yi bisa matakan kariya da take ci gaba da dauka wajen dakile bazuwar wannan cuta ta Corona. | |
Bugu da kari, yace ana samun raguwar masu kamuwa da wannan cuta, kuma sassa daban daban na gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu na yabawa da irin kokarin gwamnati kan yaki da cutar Covid 19. | |
Da yake tsokaci yayin wannan taro, kwamishinan muhalli na jihar Dr Kabiru Ibrahim Getso, cewa ya yi, baya ga feshi da suka gudanar a ma'aikatun gwamnati da masu zaman kansu da kasuwanni, kawo yanzu sun rarraba fiye da safar ta kare hanci da baki da ta kai kimanin Dubu Saba'in. | |
Wasu daga cikin kungiyoyin da suka amfana da wannan tsari na rabon takunkumin kare fuska da hanci da yawan sa ya kai Miliyan Biyu da Rabi sun hada da kungiyoyin babura masu kafa uku TOAKAN, kungiyar yan union ta NURTW, NARTO, RTEAN, kungiyoyin masu sayar da motoci, kungiyar kansiloli da ma'aikatan kananan hukumomi da sauran su. | |
Taron wanda ya gudana a budadden filin taro dake fadar gwamnatin jihar Kano ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki kan harkokin lafiya, masarautan gargajiya, kungiyoyin ma'aikata dama dubban jama'a. | |
An Gudanar Da Taron Bitar Ayyukan Tsare Tsaren Zaben Jamhuriyar Nijer. | |
Batun mutunta kason da dokokin kasa suka yi tanadi domin jinsin mata da nufin basu cikakkiyar damar shiga harakokin zabukan da ake shrin gudanarwa ta yadda za su taka rawa sosai a harakokin gudanar da mulki na daga cikin muhimman batutuwan da taron na CNDP ya tattauna a kansu kamar yadda Dr Dita Idrissa kakakin kawancen MRN na jam'iyyu masu mulkin Nijer ya yi bayani. | |
Su ma dai jam'iyyu masu sassaucin ra'ayi da ake kira ƴan baruwanmu sun yi na'am da wannan tsari na shigo da mata cikin sha'anin siyasa, a fara daga batun basu tikitin zabe a cikin jam'iyyun siyasa, kamar yadda shugaban kawancen wadannan jam'iyyu, Malam Hambali Dodo ya bayyana. | |
Sake duba tsarin da ake gudanar da zabe a karkashinsa a Nijer na daga cikin bukatun da mahalarta wannan taro suka zo da su domin a cewarsu hanya ce da ka iya ba da damar dakile magudi. | |
Sai dai wannan bukata ba ta sami shiga ba, domin a cewar hukumar zabe dukkan wata kwaskwarimar doka a wannan lokaci da ake gab da soma fafatawa abu ne da ya sabawa doka. | |
yan adawa wadanda ke ci gaba da kauracewa dukkan wasu harakokin tsare tsaren zabe basu halarci wannan taro ba, matakin da ke nasaba da rashin halaccin da suka ce ya dabaibaye hukumar zabe ta CENI. | |
A ranar 13 ga watan Disambar 2020 ne ake sa ran gudanar da zaben kananan hukumomi yayin da za a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasa da na ƴan majalisar dokoki bayan makwanni 2 kacal wato 27 ga wata. | |
Tallafawa marayu zai inganta rayuwar su - Gidauniya - Freedom Radio Nigeria. | |
Gidauniyar tallafawa Marayu da Ƴan gudun hijira dake Unguwar Wudilawa ta bukaci al'umma dasu himmatu wajen tallafawa marayu da Ƴan gudun hijira dake nan Kano. | |
Shugaban Gidauniyyar Abubakar Hassan ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na gidauniyar Albdullahi Ahamad ya san yawa hannu,wanda aka rabawa manema labarai a nan Kano. | |
Gidauniyyar ta kuma ce akwai bukatar al'umma waɗanda Allah ya baiwa ikon layya da su rabawa marayu dake Unguwanninsu da kuma sansanin ƴan hudun hijira. | |
Sanarwar ta kuma bukaci sadakar fatar layya ko naman sallah ko kudi domin rabawa da mabukata da sauran masu bukata ta musamman. | |
Kazalika za'a iya kiran gudunmawar ta wadannan lambobin waya domin bada sadarkar layya domin rabawa mabukata, 08106211786 da 09036287631. | |
Shugaban Gidauniyyar ya bayyana cewa taimakawa marayu na ingata rayuwar su. | |
Daliban Najeriya da ke Cyprus sun karyata Abike Dabire da ta ce ana yi wa dalibai kisan-rubdugu a kasar. | |
Daliban Najeriya da ke karatu a kasar Cyprus, wato TRCN sun karyata Shugabar Hukumar Kula da ƴan Najeriya Mazauna Kasashen Waje (NiDCOM), da ta gargadi iyayesu daina tura ƴaƴan su Arewacin Cyprus, ta ce ana yi masu fyadar-ƴaƴan-kadanya. | |
A ranar Litinin ce Abike Dabiri-Erewa ta yi wannan gargadin cewa ana kashe daruruwan ƴan Najeriya a Arewacin Cyprus, ba tare da gwamnatin kasar ta yi kwakkwaran bincike ba. | |
Dabiri ta yi wannan ikirari bayan an samu labarin kisan wani dalibi mai suna Ibrahim Khaleel. | |
Dalibin wanda dan Najeriya ne, an kashe shi kuma har yau ba a ji wani karin bayani ba. | |
Kisan da aka yi wa Ibrahim Khaleel zai zama darasi ga iyaye su daina tura yaran su a duniya, ana kashe su a banza, musamman a ƙasar Arewacin Cyprus. | |
Matsalar ita ce mutane ba su san cewa duk duniya ba a yarda akwai kasar Cyprus ta Arewa ba. | |
Majalisar Dinkin Duniya ma ba ta amince da Kasar ba. | |
Amma dubban ƴan Najeriya na zaune a kasar su na karatu, amma sai kashe daruruwan ƴan Najeriya a ake yi a kasar. | |
Dabiri har cewa ta yi Najeriya za ta bayyana sunayen daruruwan "yan Najeriya da aka yi wa kisan gilla a kasar. | |
Sai dai kuma yayin da suke maida mata martani, daliban Najeriya da ke karatu a kasar ta ce, Zaman lafiya a kasar Cyprus ta Arewa, ya fi na Najeriya, nesa ba kusa ba. | |
Shugaban Kungiyar Daliban Najeriya Masu Karatu Kasashen Waje (NANS), Evidence Akhayere, ya ce duk da dai ƴan Najeriya masu karatu a kasashe su na fuskantar kalubale, to masu Karatu a Arewacin Cyprus ba su fama da matsala, kalubale ko wata tsangwama. | |
Haka Evidence ya shaida wa PREMIUM TIMES a ƴar tattaunawar da suka yi. | |
Ya ce ba gaskiya ba ne da ta ce daruruwan daliban Najeriya sun mutu a Cyprus. | |
Ya ce maganar mutuwar dalibi 100 karya ne. | |
Kalilan da suka rasu duk ciwon ajali ne, ba kisan-gilla ba. | |
Afirka: Ana samun raguwar cutar corona. | |
To sai dai babban jami'in na hukumar kula da cututtuka masu yaduwa a Afrika, John Nkengasong ya ce hakan ba yana nufin a koma gidan jiya ba ne domin wannan anobar ba a kai karshenta ba tukuna. | |
Masu aiko da labarai sun ruwaito jami'in na cewa gwaji da ma hanyoyin kariya da al'umma ke bi ana samun biyan bukata kuma yana da kyau a ci gaba da kiyayewa. | |
Ya zuwa yanzu kasashen 23 daga cikin 54 a nahiyar Afirka sun sanar da samun raguwar masu kamuwa da cutar. | |
Sama da mutane miliyan daya da dubu dari biyu ne ke dauke da cutar a Afirka wanda rabinsu ke a kasar Afirka ta Kudu. | |
Jirgin kasa zai ci gaba da sufuri tsakanin Kaduna zuwa Abuja. | |
Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya ce za a dawo a ci gaba da sifirin jirgin kasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna a ranar 29 ga watan Yulin da muke ciki. | |
Amaechi ya bayyana hakan ne lokacin gwada wasu sabbin taragun jirgi da za su rika zirga-zirga tsakanin Kaduna zuwa Abuja a yau Asabar. | |
An dai tsaida aikin ne a watan Maris din bana da ya gabata a wani mataki na dakile annobar cutar COVID-19. | |
A cewar Ministan, dimbin al'umma daga bangarori daban-daban ne suka bukaci da a dawo aikin kafin Sallar layya ta makon nan. | |
Ministan ya jaddada cewar, tuni gwamnati ta dauki matakan dakile yaduwar annobar cutar a wannan lokacin a bangarorin sufurin jiragen kasa. | |
Shugaban kamfanin sufurin jiragen kasa na kasa Fidet Okhiria ya ce aikin sufurin zai dawo gadan-gadan a Larabar makon nan. | |
Zaman tattauna hanyar maslaha a rikicin Mali. | |
Biyar daga cikin shugabannin kasashen yammancin Afirka sun soma wani taro a wannan Litinin da zummar shawo kan rikicin siyasar kasar Mali. | |
Taron wanda shi ne karo na uku tun bayan tsanantar rikicin, zai mayar da hankali kan samar da maslaha a tsakanin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da jagoran jam'iyyar adawa Imam Mahmoud Dicko. | |
Matakin shiga tsakani da Shugabannin kasashen Najeriya da Nijar da Ghana da Cote d'Ivoire da Senegal suka yi, da ma wanda tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya jagoranta duk sun ci tura. | |
A cewar Kungiyar Ecowas, ba a fidda zato na cimma matsaya ba duk da cewa sun nuna rashin amincewa da takaddamar muradun masu hamayyar da IBK na ya yi murabus daga mulki ba. | |
Yanzu dai an zura idanu domin ganin yadda za ta kaya. | |
Da shugabannin addinai na faɗawa mabiyansu gaskiya da ba za a riƙa samun tashin hankali ba. | |
Kakakin majalisar dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Zailani ya gargaɗi shugabannin addinai da su riƙa gayawa mabiyan su gaskiya komai ɗacinta maimakon zuga mabiyansu a wuararen ibada da tallata ƙiyyayya. | |
Zailani ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a ɗakin taro na fadar gwamnatin Kaduna a lokacin da gwamnatin jihar ke karɓar baƙuncin shugaban ƙungiyar Kiristocin Najeriya da suka ziyarci Kaduna a makon jiya. | |
Zailani ya ƙara da cewa "Gaskiya ce ba a so a riƙa faɗi, idan ka je wasu wuraren ibada sai ka ji masu jagorar su na zuga su sannan suna tallata musu ƙiyayyar abokan zaman su da ba addinin su ɗaya ba. | |
Hakan shine yake ruruta fitina a tsakanin mutane. | |
A ƙarshe ya ce dole sai an dawo an haɗa kai sannan shugabannin addinai na karantar da mabiya saƙon Allah maɗaukakin sarki kamar yadda ya zo a littafan addinan mu, ba za a samu zaman lafiya ba. | |
Haka shima sanatan da ke wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Uba Sani da ya halarci wannan taro ya roƙi waɗanda ba mazauna garin Kaduna bane da su riƙa tauna kalaman su kafin su furta su. | |
Wannan rikici ya shekara sama da 40 ana fama da shi. | |
A karon farko an samu gwamna jarumi da ya lashi takobin sai an kawo ƙarshen wannan matsala. | |
Amma kuma saboda yadda wasu ke karkata labarin ainihin abinda ke faruwa, mutane da yawa ɓangare ɗaya kawai suke ji banda wasu ɓangarorin. | |
Dubban matasan N-Power na zambatar shirin ne. | |
Ministan jinkai da bada tallafi, Sadiyya Farouk ta shaida cewa akwai dayawa daga cikin masu amfana da N-Power, wato karbar Alawus duk wata, suna aiki a wasu wuraren, haka bincike ya nuna. | |
A takardar da ministan ta fidda ranar Alhamis, ta ce tabbas akwai wadanda ba a biya su ba amma kuma ba daga ofishinta bane aka samu wannan matsala, tuni ofishin ta ta mika sunayen mutum sama da 500,000 domin a tantance su a biyasu kudadaen su na baya. | |
Ta ce akwai tantance sunaye da ake tayi ne domin bankado masu zambatar hukumar, suna karbar kudade bayan suna aiki a wasu wurare. | |
Wannan shiri na wadanda basu da aikin yi ne amma wasu dubbai cikin wadanda ke karbar alawus tuntuntuni ashe suna aiki a wasu wurare kuma suna karbar alawus din N-Power. | |
Yanzu ana yin tankade da reraya ne domin gano su da wancakalr da su daga cikin wadandaza a biya. | |
Ta roki masu amfana da shirin da ba a biya su kudaden su na baya ba su kara hakuri cewa nan ba da dadewa ba za su ji alat. | |
Yan N-Power sun yi zanga-zangar dakatar da su da minista Sadiya ta yi a Abuja | |
Daruruwan matasa da suka halarci taron gangami don yin zangazangar dakatar da su daga shirin tallafi na N-Power daga fadin kasar nan da aka yi a Abuja ranar Juma'a sun bayyana cewa lallai gurguwar shawara ce dakatar da matasa da gwamnati ta yi. | |
Matasan sun yi tattaki har zuwa majalisar Kasa domin nuna rashin amincewar su da dakatar da shirin cikin kankanin lokaci. | |
Daya daga cikin wadanda suka halarci wannan gangami kuma wakili daga jihar Kano, a zantawa da ya yi da wakilin PREMIUM TIMES HAUSA, ya shaida cewa suna kira ne ga gwamnati da ta jinkirta wannan shawara da ta yi, sannan ta biya wadanda har yanzu ba a biya su alawus dinsu na wata uku ba. | |
Sannan kuma sun yi kira da a basu kudin tallafi ganin cewa matasan sun dade suna amfana da wannan tallafi na gwamnati. | |
Bayan sun gana da wasu daga cikin ƴan majalisa da suka saurari kukan sai kuma suka dunguma zuwa rukunin sashen ma'aikatan gwamnatin Tarayya, domin ko za su yi kicibus da ministan samar da tallafi ta Kasa, Sadiya Farouk. | |
Fitaccen Mai Rajin Kare Hakkin dan Adam, Komared Mustapha Soron Dinki, da ya yi tattaki tun daga Kano zuwa Abuja tare da matasan ya ce wannan gangami an yi shi don tunasar da minista domin wadanda suke amfana da shirin da dama ba abiya su hakkokin su ba kafin a dakatar da su. | |
Tun safe matasa suka yi dandazo a majalisar Kasa. | |
Muna fatan gwamnati zata ji kukan matasan nan a samar musu da mafita da zai taimaka musu wajen ci gaba da rayuwa kamar da. | |
Matasan rike Kwaleye dauke da rubutu na kira ga gwamnati su waiwaye su da idon rahama. | |
An Yi Jana'izar Tolutope Arotile, Matukiyar Jirgin Yaki Mai Saukar Ungulu Ta Farko A Najeriya | |
An yi janaizar Tolulope Arotile mace ta farko matukiyar jirgin yaki mai saukar Ungulu a Najeriya tare da karrama ta a Abuja. | |
Arotile ta mutu ne sanadiyar buge ta da wasu tsoffin abokan karatunta a sakandaren sojan sama suka buge ta da mota ta baya lokacin da suka gan ta kwatsam a ranar Litinin, 14 ga Yuli. | |
Manyan jami'an rundunar sojin sama da jami'an gwamnati ciki har da gwamnan jihar Kogi, mahaifar Ms Arotile ne suka halarci jana'izar tata da aka yi a babbar makabartar sojin Najeriya da ke Gudu a Abuja. | |
An bayyana marigayiyar da cewa ta bayar da gudunmuwa sosai a yaki da ƴan bindiga masu fashin daji a jihar Neja inda ita ce ke tuka jiragen rundunar Gama Aiki. | |
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina mata bisa sadaukarwar da ta yi wajen ci gaban kasar. | |
Babban hafsan sojin saman kasar Air Marshal Sadique Abubakar ya ce mutuwar jami'ar babban rashi ga rundunar tare da jajanta wa iyalanta a madadin dukkanin jami'an rundunar sojin sama na Najeriya. | |
Baƙin Mutum Sarki Ne, Na Shan Yabo Da Suka. | |
Fim mai cike da waƙoƙin nan da mawƙiya Beyonce ta yi mai taken "Black is King", wato Baƙin Mutum Sarki Ne na ci gaba da shan yabo da kuma suka a duniya, saboda yadda ya bayyana al'adar Afirka. | |
A kasar Afirka Ta Kudu, inda aka haɗa wannan fim mai tsawon minti 85, mutane da yawa sun ce wannan ya ma wuce fim. | |
Black is King, dai wani fim ne mai cike da waƙoƙi wanda shahararriyar mawakiya kuma marubuciyar wakokin nan na Amurka, Beyonce ta jagoranci tsarawa, da harhaɗawa da kuma kammalawa. | |
Wannan fim ɗin ya yi fice irin na waƙarta mai taken "The Lion King: The Gift", wato Sarakin Zaki: Ɗan Baiwa. | |
Bara ne aka yi fim ɗin a Amurka, Kudanci da Yammacin Afurka, da kuma Turai, kuma ya ƙunshi mawaƙan Afirka da dama. | |
Wannan fim ɗin, wanda aka fitar a watan Yuli, ya samu karɓuwa matuƙa daga masu saurare, amma kuma akwai masu suka. | |
Wasu na cewa Beyonce, wadda aka haifa a birnin Houston na jihar Texas ta nan Amurka, ta ari abubuwan Afirka ba bisa ƙa'ida ba, musamman siffofin da su ka jiɓinci Afirka a fim ɗin, alhalin kuwa a al'adance ba ta da wani tushe a nahiyar ta Afirka. | |
To amma a Afirka ta Kudu, sai ma murna waɗanda su ka taka rawa wajen yin wannan fim ɗin ke ta yi. | |
Sibusiso Mathebula, wani ɗalibi mai karanta harkar fim, ya ce an martaba shi da aka sa shi cikin masu yin fim ɗin. | |
Ya ce fim ɗin ya burge shi. | |
Fim ɗin ya taɓo abubuwa da dama waɗanda ba a koya masu ba a makaranta game da tarihin baƙar fata. | |
Ya ce lokacin da ya ga fim ɗin ne ma ya fara ganin labarin da kuma tufafin da ta ke sawa da kuma ɗaukacin abubuwan fim ɗin, wanda hakan ya ɓullo da abubuwa da dama fiye ma da yadda aka zata zai faru. | |
Kgosi Motosoane mai son wakokin Beyonce ya ce ƴan Afirka da ke ƙasashen waje - ciki har da baƙaƙen fatar Amurka - na da damar amfani da abin da wasu ke ganin kayan al'adun Afirka ne. | |
Yace shi dai yana sha'awar fim ɗin. | |
Kgosi ya ce an fi mayar da mata baƙaƙe can mataki na ƙasa a cikin al'umma. | |
Don haka ɓullowarsu cikin al'amura masu matukar tasiri haka, abu ne mai ƙarfafa gwiwa. | |
Dalibi mai karanta yadda ake fina-finai, Mathebula yace fim ɗin Beyonce ya sa shi sha'awar fara yin nashi fim ɗin domin ya daɗa yaɗa bayanai game da Afirka. | |
Yan Afurka magoya bayan Beyonce sun yi muwafaka kan abu guda: Idan Bakin Mutum Sarki Ne, to Beyonce sarauniya ce. | |
Anita Powell ta nan Muryar Amurka ce ta hada mana wannan rahoton. | |
Minista Sadiya Ta Yabi Ƴan Jarida Da Ma'aikatan Agaji. | |
Ministar Harkokin Agaji Da Jinkai ta Nijeriya, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta yaba da kokarin kafafen yada labarai, ma'aikatan agaji da hukumomin hadin gwiwa a daidai lokacin da ma'aikatar ta ta cika shekara daya da kafuwa. | |
Ita dai wannan ma'aikata, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya kirkire ta a ranar 21 ga Agusta, 2019 domin aiwatar da manufofi da ayyukan agaji, da rigakafin aukuwar bala'o'i tare da kai agajin gaggawa, sa'annan da gudanar da aikace-aikacen taimaka wa jama'a mabukata. | |
A cikin wata takardar sanarwa da mai agaza mata a harkar aikin yada labarai Halima Oyelade ta raba, ministar ta yi la'akari da cewa wannan shekara ce da aka yi abubuwa da dama, mai cike da kalubale da abubuwan sha'awa wadda a cikin ta mu ka koyi hanyoyin kai agaji ga jama'a da kula da bala'o'i, amma a duk cikin ayyukan mun maida hankalin mu wajen cika aikin da aka ba mu wanda ya kunshi kai wa jama'a dauki, hana aukuwar bala'i tare da agaza wa wadanda bala'i ya auka mawa, da kuma fito da hanyoyin rage radadin bala'i idan ya faru, wanda hakan ya taimaka mana wajen inganta aikin mu saboda nan gaba. | |
A lokacin da ta ke yaba wa Shugaban Kasa a kan hangen nesa da ya yi na kirkiro ma'aikatar wadda ta kasance kan gaba wajen yaki da annobar korona, Hajiya Sadiya Umar Farouk ta gode masa saboda dora ta a kujerar direbar ma'aikatar da ya yi. | |
Haka kuma ta yi la'akari da cewa a cikin wannan shekara dayan, ta koyi muhimman darussa tare da samun sabuwar fahimta game da hanyoyi masu bullewa da marasa bullewa a wannan aiki. | |
Yayin da ta ke yaba wa kafofin yada labarai, ministar ta ce wadannan kafofi abokan tafiya ne wadanda tilas ne a hada karfi da su domin samun nasara. | |
Ta ce, "Ina so in bayyana maku a yau cewa aikin da ku ke yi ya dace". | |
Ta kuma ce da yake ba hurumin ta ne ta bai wa kan ta maki kan nasarorin da ta samu ba, amma a shirye ta ke ita da abokan aikin ta za su ci gaba da aikin su a cikin sadaukarwa da jajircewa domin cika alkawurran aikin su, wanda ya yi daidai da jigon cikar su shekara daya, wato Service2Humanity. | |
Ministar ta yi jinjina ta musamman ga "ma'aikatan agaji da kuma abokan hadin gwiwar mu a wannan sashe daga hukumomin Majalisar Dinkin Duniya irin su OCHA, IOM, UNHCR da Hukumar. Abinci ta Duniya, Bankin Duniya, USAID da Tarayyar Turai (EU), da kuma sauran hukumomin hadin gwiwa wadanda su ka ci gaba da bada agaji duk da halin rashin tsaro da ake ciki da kuma wahalhalun da su ke fuskanta. | |
Ta kuma yi jaje kan wadanda su ka rasu a wuraren da ake da rashin tsaro a cikin wannan shekara dayar da ta gabata. | |
Ministar ta yi bayanin cewa cika shekara daya da kirkiro ma'aikatar ya sa tilas su dage sosai. | |
Ta ce, "A yayin da mu ke murnar cika shekara daya, ina so in ce lokaci ya yi da ya dace mu sake zage dantse wajen aiwatar da aikin mu". | |
Dole ne mu nemo hanyoyin da za mu fadada aikin kula da bala'o'i, samar da agaji da kuma fito da hanyoyin tallafin jama'a wanda hakan zai taimaka mana wajen inganta aikin mu a nan gaba. | |
A daidai lokacin da manoma ke dab da cin moriyar nomansu a Najeriya, manoman yankin jihar Sokoto sun soma kokawa akan barazanar da tsuntsaye suka soma yi musu, abinda ka iya kawo cikas ga amfanin gona da ake tunanin samu. | |
Barazanar tsuntsayen masu jan baki a yankin jihar Sokoto na zaman tamkar murna ta koma ciki, duba da cewa an ga alamun samun kakar abinci mai kyau a wannan shekara ta 2020. | |
Akan dole, wasu manoman yankin suka rungumi wata dabara ta gargajiya ta korar tsuntsayen kamar yadda wani matashi mai suna Faruk daga yankin Dange Shuni ya bayyana. | |
Sambo Abubakar, ɗaya daga cikin manoman yankin, ya ce tsuntsayen yanzu haka suna addabar dukkan shuke-shuken da suka fara ƙosawa a gonaki. | |
Shugaban ƙungiyar manoma ta Najeriya reshen jihar Sokoto, Murtala Gagado Minannata, ya ce yanzu haka a kashi biyu bisa uku na jihar Sokoto ana fama da wannan matsalar. | |
Ya kuma ce yanzu suna jira ne su ji halin da yankunan ƙananan hukumomi a jihar ke ciki don su hada rahoton da za su aika wa ma'aikatar gona ta jiha da tarayya domin ɗaukar matakin da za a taimaka wa manoma. | |
Jami'in ma'aikatar gona ta tarayya mai kula da sashen maganin tsuntsaye da ƙwari, Ya'u Maƙeri Kagara, ya ce ba a wuce wata ɗaya da kammala feshin maganin kashe tsuntsaye a yankin na Sokoto ba. | |
Ya kara da cewa tsuntsayen na shigowa ne daga jamhuriyar Nijer da ƙasar Benin, kuma harkar ƙasa da ƙasa dole sai da wata yarjejeniya kafin a haɗa kai a magance matsalar. | |
A watan Yuni ne gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da aikin feshin kashe tsuntsaye a jihohin arewacin Najeriya guda 12 waɗanda ke maƙwabtaka da ƙasashen waje waɗanda ta nan ne tsuntsayen ke shigowa Najeriya. | |
Sai dai sake samun wannan matsalar na iya mayar da hannun agogo baya ga ci gaban da ake ganin ana samu a fannin noma wanda gwamnatoci ke iƙirarin cewa suna ba shi kulawa ta musamman. | |
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir. | |
Ana samun rarar biliyan 4 a kullum bayan aiwatar da IPPIS - Akanta. | |
Gwamnatin tarayya ta ce ta samu rarar naira biliyan ashirin da daya daga ma'aikatu da hukumomi da sassan gwamnati bayan kaddamar da tsarin biyan albashi na IPPIS. | |
Haka zalika ta ce gwamnati na samun rarar naira biliyan hudu a kullum sakamakon kaddamar da tsarin na IPPIS a ma'aikatu da hukumomi da sassan gwamnati guda dari shida da biyu. | |
Akanta janar na tarayya Ahmed Idris ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da Ƴan kwamitin kula da sadarwa na majalisar dattijai wadanda suka kai masa ziyara ofishinsa da ke Abuja. | |
Haka zalika akanta janar na tarayyar ya kuma ce ofishinsa na yin hadin gwiwa da ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro domin dakile fitar da bayanan sirri na gwamnati don gudun fadawarsu hannun bata gari. | |
Da ya ke mai da jawabi shugaban kwamitin kula da sadarwa na majalisar dattawa Sanata yakubu Oseni, ya ce kasar nan na fuskantar matsaloli da dama da suka shafi kutse da batagari ke yi ga bayanan sirri na gwamnati ta internet. | |
An Cafke Mutum Uku Bisa Zargin Kisan Matar Wani Sarki A Arewa. | |
Rundunar ƴan sandan jihar Kogi ta sanar da damke mutum 3 da take zargi da kashe matar babban limamin jihar. | |
Wani ganau ba jiyau ba, ya sanar da cewa ƴan ta'addar sun halaka Yemisi Baderu a gaban mijinta da ƴaƴanta. | |
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP William Aya, ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ya ce ana bincikar wadanda ake tuhuma, a kalla mutum uku ne suka shiga hannun rundunar ƴan sandan jihar Kogi sakamakon zarginsu da ake da kashe matar. | |
Kisan da aikata shi a yankin Stereo, inda suka hallaka Yemisi Baderu, a karamar hukumar Ijumu ta jihar. | |
Wani ganau ba jiyau ba, ya ce an kashe matar a cikin gidanta a kan idon mijinta da ƴaƴanta. | |
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, an halaka matar ne ta hanyar sara da adda. | |
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP William Aya, yayin tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce an kama wadanda ake zargin kuma ana tuhumarsu. | |
A wani bangare kuwa, babban mai ba da shawara a kan harkar tsaro na yankin, Taufik Isa, wanda ya ziyarci yankin a ranar Asabar, ya kwatanta lamarin da rashin imani. | |
Buhari na jagorantar taron majalisar zartarwa. | |
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar taron majalisar zartaswa ta kasa a Abuja. | |
Rahotanni sun ce kafin fara taron sai da aka gudanar da shiru na ƴan mintuna don karrama mahaifin gwamnan jihar kwara kuma lauya na farko a arewacin kasar nan Alhaji Abdulganiyu Abdurrazak wanda ya rasu a baya-bayan nan a birnin tarayya Abuja. | |
A makon jiya ne dai mahaifin na gwamnan jihar Kwara ya rasu bayan fama da wata gajeruwar rashin lafiya. | |
Sarkin Hausawan Afrika ya nemi ɗalibai su koyi sarrafa harshen Hausa - Freedom Radio Nigeria. | |
Sarkin Hausawan Afrika kuma Sardaunan Jihar Agadaz Dakta Abdulkadir Labaran Koguna, ya buƙaci ɗalibai da su mayar da hankali wajen koyo tare da sarrafa harshen hausa. | |
Dakta Abdulkadir Labaran na bayyana hakan a yau ta cikin shirin "Barka da Hantsi" na nan tashar freedom Rediyo, wanda ya mayar da hankali kan ranar Hausa ta duniya da za a gudanar a gobe Laraba. | |
Dakta Labaran ya kuma ce, harshen hausa na taka rawa wajen ɗabbaka al'adun bahaushe, yana mai cewa, matasan yanzu na ƙoƙarin aron al'adun wasu harsunan wanda ba daidai ba ne. | |
A cewar sa, harshen hausa ya mamaye ƙasashe hamsin da tara a faɗin duniya, wanda ya ba su damar yin sarautu a wasu ƙasashen a ɓangaren harshen na hausa. | |
Shi ma da ya kasance cikin shirin, sarkin ƙungiyar ɗaliban Hausa ta ƙasa Malam Nura Sulaiman Janburji, ya ce harshen hausa na da alfarma ta yadda a ƙasashen ƙetare akan bai wa dalibai damar kafa daula. | |
Baƙin biyu, sun yi kira ga gwamnatoci a dukkanin matakai da su ɗabbaka harshen hausa a majalisun ƙasar nan dmion kare marbatar sa a idon duniya. | |
Jamus ta tsaurara matakan yaki da corona | |
Angela Merkel dai na mai goyon bayan saka haraji na Euro 50, kwatankwacin Naira dubu 22, ga duk wanda aka kama ba ya sanye da takunkumin rufe baki da hanci a bainar jama'a. | |
Har wayau tana mai bukatar saka dokar rage yawan taron mutane a cikin gida da ma waje. | |
Shugabar gwamnatin ta ce tana goyon bayan ministan lafiya da ya bukaci a daina gwajin cutar kyauta ga masu dawowa balaguro daga ketare. | |
A baya dai Jamus ta yi nasarar shawo kan annobar amma bisa janye dokokin da suka sanya a farkon shekarar nan ana yawan samun sabbin kamu da cutar a yanzu haka. | |
Za a Sake Gabatar Da Sabon Kudurin Tallafin COVID-19 a Amurka. | |
Yayin da alkaluma ke nuna cewa adadin wadanda ke kamuwa da cutar COVID-19 na ci gaba da karuwa a Amurka, a yau Litinin ake sa ran ƴan Jam'iyyar Republican a Majalisar Dattawan kasar za su gabatar da wani kudurin ba da tallafi. | |
Ana tunanin cewa tallaffin zai kai kudade dala tiriliyan daya domin sassauta radadin da annobar coronavirus ta haifar a kasar. | |
Shirin na zuwa ne kwanaki gabanin karewar wa'adin ba da agajin kudade na farko ga miliyoyin Amurkawa da suka rasa ayyukansu sanadiyyar cutar ta COVID-19. | |
A jiya Lahadi, bayan da aka kwashe kwanaki ana tattaunawa da ƴan Republican a majalisar dokokin kasar, shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Amurka, Mark Meadows da kuma Sakataren Baitul- Mali Steven Mnuchin sun ce tallafin ya kunshi fadada shirin ba da kudaden ne ga wadanda suka rasa ayyukansu. | |
Amma a cewarsu, a wannan karo, Amurkawa za su ga kashi 70 cikin 100 ne na kudaden da aka ba su a baya. | |
A dai ranar Juma'a wa'adin tallafin farko zai kare wanda aka biya wasu kunshin kudade ga wadanda suka rasa ayyukansu, aka kuma rika ba su 600 a kowanne mako baya ga wanda jihohi suke bayarwa. | |
Su dai "yan Republican suna korafin cewa wannan shiri na nufin wasu mutanen da ake biya na samun kudaden da suka haura wanda ake biyansu a lokacin da suke aiki, idan aka hada tallafin gwamnatin tarayya da wanda jiha ke biyansu. | |
Amma "yan Democrat a nasu bangaren, sun kalubalanci wannan ikrari suna masu cewa lura da yadda cutar ta coronavirus ke karuwa, wasu ma'aikatan ba su da kwanciyar hankalin da za su iya komawa bakin aikinsu. | |
Dalilin da ya sa na koma APC bayan ficewa daga PDP. | |
Tsohon shugaban Majalisar Wakilan Najeriya Yakubu Dogara ya bayyana dalilan da suka sa shi ya sake sauya sheka daga Jam'iyyar PDP zuwa APC bayan shugaban riko na Jam'iyyar Mai Mala Buni ya sanar da komawar sa cikin Jam'iyyar ta su. | |
A wasikar da ya rubutawa Jam'iyyar PDP a mazabar sa ta Bogoro, Dogara yace rugujewar shugabanci a Jihar sa ta Bauchi a karkashin gwamnatin Bala Muhammed da ya taimakawa samun nasara shine dalilin da ya sa ya bar Jam'iyyar. | |
Dogara yace ba zai iya bude baki yayi tambaya kan yadda ake tafiyar da gwamnatin Jihar ba sai a zarge shi da rashin biyayya, saboda haka ya haure takalman say a fice daga Jam'iyyar. | |
Tsohon shugaban Majalisar yace idan ya nade hannayen sa yaki cewa komai kan yadda al'amura ke tabarbarewa a Jihar Bauchi a karkashin gwamnatin Bala Muhammed zai zama maci amana, bayan a lokacin Gwamna Isa Yuguda da Mohammed Abubakar kowa ya ji muryar sa ya na bayyana ra'ayin sa idan yaga ba daidai ba. | |
Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin noma domin samar da abinci da kuma aikin yi. | |
Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da Shirin Noma Domin Samar Da Abinci Da Aikin Yi (AFGP), wanda wani reshe ne daga shirin Tabbatar Da Dorewar Tattalin Arziki. | |
wannan shirin noma an kaddamar da shi ne domin rage wa manoma kuncin rayuwa sanadiyyar bullar cutar Coronavirus. | |
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Ministan Harkokin Noma, Sabo Nanono, a lokacin da ake kaddamar da shirin a Katsina. | |
Sanarwar da kakakin yada labarai na Ma'aikatar Gona, Ezeaja Ikemefuna, ya fitar a ranar Alhamis. | |
Wannan shiri zai magance kuncin rayuwar da mutane suka shiga sakamakon barkewar cutar Coronavirus a kasar nan da ma duniya baki daya. | |
Shirin kuma zai kara zaburar da manoma hanyoyin bunkasa abinci, gyara shi da kuma hanyoyin sufurin sa a Najeriya. | |
Minista kamar yadda aka ruwaito, ya ce, wannan taron kaddamar da shiri ya na wakiltar sama da kananan manoma sama da su 1, 100,000 a fadin kasar nan. | |
Ya ce wadannan adadin kananan manoma sama da milyan 1, 100,000, suna cikin Rukunin Manoma ne da ke karkashin kamfanoni 6 da suka hada da AFEX, BabanGona, Value Seeds, Universal, Thrive Agric da kuma Oxfam. | |
Nan ba da dadewa ba kuma za mu bayyana rukuni na biyu na B, na wadanda za su ci moriyar wannan shiri na noma. | |
Nanono ya tunatar da yadda Shugaba Muhammdu Buhari ya kafa Kwamitin Farfado da Tallalin Arziki daga nakasun da ya samu bayan barkewar cutar Coronavirus. | |
Ya ce daya daga cikin hanyoyin farfado da tattalin arzikin kasar nan, har da Shirin AFJP, tare da cewa shirin zai bunkasa noma daga kasancewar sa noman tara abincin hannu-baka-hannu-kwarya zuwa na zamani kuma mai samar da wadataccen abinci. | |
Ya ce shirin dai ya kunshi shirin da gwamnati ta yi na raba abinci metrik tan na abinci har 100,000 ga shirin tsamo marasa galihu daga jigatar karancin abinci da yunwa a lokacin bullar cutar Coronavirus. | |
Ya ce a cikin shekara daya ana sa ran wannan gagarimin shiri, zai sanar wa matasa milyan 5 zuwa milyan 10 aiki. | |
Kuma zai samar da abinci kimanin metrik tan milyan 10 a hekta daga 20,000 zuwa 100, 000 a kowace jiha, ga manoma akalla milyan 2.4. | |
Akwai bukatar mutane su san kundin dokar shari'a ta 2019 - Kungiyar KCSF. | |
Hadakar kungiyoyin sa kai na farar hula masu zaman kansu a jihar Kano wato Kano Civil Society Forum (KCSF), tare da hadin gwaiwar tarayyar turai EU, da kungiyar yada al'adun kasar Birtaniya ta British Council, da kungiyar tabbatar da doka da yaki da cin hanci ta Rule of Law and Anti-corruption (Rolac), sun gabatar da makalar wayar da kai dangane da kundin tafiyar da shari'ar laifi ta shekara 2019. | |
Taron wanda ya gudana a cibiyar Dimokradiyya da fadada bincike ta Aminu Kano dake gidan Mumbayya, ya yi duba akan sabbin dokoki da yadda tsarin gudanar dasu yake ga al'umma wanda aka shiryawa kungiyoyin farar hula dake Kano 150 da ƴan Jarida. | |
Da yake jawabi Babban mai gabatar da maƙalar, Dakta Nuhu Musa Idris , na sashen koyar da shari'a ta Jami'ar Bayero dake nan Kano, ya yi tsokaci kan wasu dokokin da suka fi sarkakiya. | |
Inda ya yi kira da a duba wasu dokokin da suka tsufa sakamakon shari'a na tafiya da Zamani. | |
A bagaren sa, shugaban hadakar kungiyoyin fararen hula na jihar Kano (KCSF) Ibrahim Wayya, ya ce rashin sanin dokokin ya taka rawa matuka wajen take hakkin al'umma da yasa ake da bukatar sanin yadda suke. | |
Wasu mahalarta taron wanda shi ne irin sa karo na uku da aka shirya , a shiyyoyin Sanatoci Kano guda uku, daga kungiyoyin farar hula sun bayyana yadda suka kalli tsarin dokokin da sakon su. | |
Wakilin mu Aminu Halilu Tudunwada, da ya halarci taron wayar da kan , ya ruwito mana cewa an tattauna matsalolin wasu dokoki da aka tsakuro waɗanda al'umma ke fuskantar Kalubale a kan su. | |
Waɗanda galibi basu san hakkin su ba akan su, kasancear dokar tana da dokoki sama da 400, da suka yi Karin bayanan wayar da kai. | |
Ana Muhawara Kan Sabuwar Dokar Rajistar Wuraren Ibada a Najeriya. | |
Kungiyar SERAP mai fafutukar kare hakkin bil'adama da ci gaban tattalin arzikin kasa da ake kira SERAP ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tsawatawa Ministan Shariar Najeriya Abubakar Malami da kuma Babban Darakta a hukumar rajistar kanfanoni da su dakatar da shirin fara rajistar wuraren ibada. | |
A cewar kungiyar ta SERAP wannan mataki tamkar tauye hakkin bil'adama ne kamar yadda yake kunshe a kundin tsarin mulkin Najeriya. | |
Kafin kungiyoyin kare hakkin bil'adama su koka game da wannan mataki na gwamnati, tuni shugabannin addinai daban daban suma suka gabatar da kukansu ga gwamnatin ta Buhari, cewar a sake mayar wa ƴan Majalisa wannan dokar domin dubawa da kuma amincewa da ita, ta yadda ba za ta yi karo da ƴancin da tsarin mulkin kasa ya bayar ba na addini da walwala. | |
Pastor Yohanna Buro shugaban kiristoci ne a jihar Kaduna ya shaida wa wakilin Muryar Amurka cewa wannan doka ba ta da tushe balle makama, saidai idan gwamnati tana neman hana ibada ne ko saka takunkumi. | |
Kawai kamata ya yi ta yi anfani da hanyoyin ta wajen saka ido da bibiyar duk masu karya doka ba tare da saka wata sabuwar doka ba. | |
Shi ma a bangarensa, Dr Bashir Yankuzo, limamin jami'ar kimiyya dake Minna ya ce koda yake babu laifi gwamnati ta saka ido ga kamfanonin da kungiyoyi domin tsaron kasa, amma hakan ba yana nufin tsaurarawa ta yarda za a tauye ƴancin wani ba ko wasu ba. | |
Yanzu dai abin jira a gani shine ko gwamnati zata saurari wannan kuka na jama'a. | |
Yadda Jami'ar Fasaha ta Akure (FUTA) ta yi kokarin durkusar da shafin PREMIUM TIMES a intanet. | |
Jami'ar Fasaha ta Akure (FUTA) ta dauki nauyin wani gogarman yi wa shafukan yanar gizo shigar-kutse, domin durkusar da shafin PREMIUM TIMES, fitacciyar jaridar "online" da ke Najeriya. | |
Wannan gogarman tsallaka shingayen gidajen yanar gizo wato intanet, ya yi duk wata dabarar da masu harkallar kutse a shafukan mutane ke bi su shiga shafukan su, amma bai yi nasara ba. | |
Ya fara jaraba yin shigar kutsen ne, wato "hacking" tun a ranar 28 Ga Fabrairu, inda ya jibge muggan makaman kayan aikin sa a harabar Jami'ar, kuma ya ya rika kai hare-haren sa ta hanyar yin amfani "data" din jami'ar. | |
A gefe daya kuma idan ya yi kokarin kutsawa rumbun intanet na PREMIUM TIMES da kwamfuta, sai kuma ya sake kai wani harin da wayar GSM din sa. | |
Kwanaki biyar cur ya shafe ya na saran kofar shiga shafin Babban Rumbun PREMIUM TIMES, amma bai yi nasara ba, duk kuwa da cewa ya yi amfani da muggan makaman fasahar zamani daban-daban. | |
Bai samu nasarar kutsawa ba, saboda jami'ar ba ta san cewa jaridar PREMIUM TIMES ta na da kwakkwaran shirin da ta ke da shi, wanda ta gina gabjejiyar kuma gadangarkamar kofar da wani dan dagaji bai isa ya fasa ta ba. | |
Sannan kuma PREMIUM tana da gwarazan jami'an tsaron shafin Babban Rumbun Intanet din ta na zamani da suka hada da Sarkin Yakin PREMIUM TIMES da Babban Dakare, Garkuwar Yanar Gizon PREMIUM TIMES. | |
Wadannan jami'an tsaron da suke da kwarewar zamani wajen murkushe duk wani gungun mahara ko wani barden da ya nemi yin kumumuwa shi kadai, ko yin shahadar-kudan kokarin afkawa cikin Rumbun Bayanan PREMIUM TIMES. | |
Irin Makaman Da Dan Shigar-kutsen Intanet Ya Rika Kai Wa Shafin PREMIUM TIMES Hari Da Su: | |
Karfe 8 na safe ya fara sukuwa da zamiya kofar Babban Rumbun PREMIUM TIMES, domin ya ga ta yadda zai yi kunar-bakin-wake ya kutsa a ciki, ya ruguza rumbun gaba daya. | |
Da bai yi nasara ba a cikin dare, washegari kuma da sassafe, karfe 6:15 sai ya sake jaraba sa'a, wannan karon ta hanyar yin amfani da "WPScan", abin da ake yi domin a gano karfi ko rashin karfin matakan tsaron shafukan Intanet manya irin na PREMIUM TIMES. | |
Bayan minti 90 ne sai ya fara yunkurin kutsawa da karfin dabarun fasahar zamani na na'ura mai kwakwalwa, wato "custom script". | |
Da safe ne kuma ya yi duk wani kokarin da zai yi ta hanyar siddabarun na'urar kwamfuta domin ya kulle shafin PREMIUM TIMES gaba daya. | |
Yadda Mai Gona Ya Yi Maganin Mabarnacin Biri: | |
Wannan mai shigar kutsen bai san cewa PREMIUM TIMES ta yi kwakkwaran tanajin maganin kananan beraye da manyan biran da ke shiga gonakin shafukan sadarwar zamani su na kutsen rufe shafi ko kwace shafin sukutum ba. | |
Wannan rashin sanin na sa ne ya sa dukkan kayan faman da ya yi amfani da su, gaba daya tsoffin kamaman da ba su iya yi wa PREMIUM TIMES wata illa ko lahani ba. | |
A wannan rana ya sha wahalar banza ya gaji domin ya bi ta hanyar kai hari da DDOS ne a Rariyar Likau din NTP, wacce tsohuwar hanya ce da aka rika amfani da ita tun Kano na kauye. | |
Ranar 3 Ga Maris ne ya yi duk wata dabarar da ta rage a kwakwalwa da tunanin sa, amma duk bai yi nasara ba. | |
Wannan yunkurin karya kofar Babban Rumbun PREMIUM TIMES ya zo ne kwanaki kadan bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin kwatagwangwamar takun-saka tsakanin Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari a Fannin Tsaro, Babagana Monguno shi da tsohon Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, Marigayi Abba Kyari. | |
Wasu da ke cikin Jami'ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure, sun gulmata wa PREMIUM TIMES cewa jami'ar ta dauko sojan-hayar wasu manyan berayen da ke wa shafukan Intanet shigar-kutse, domin su yi wa shafi da Babban Rumbun PREMIUM TIMES dirar-mikiya, su lalata ko su ruguza shi. | |
Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta tuntubi jami'ar ta FUTA, ta nesanta kan ta da wannan yunkurin na kokarin afkawa Babban Rumbun PREMIUM TIMES na Intanet. | |
FUTA ta ce sai dai idan wani mai karambani ne kawai da ke dalibta a jami'ar ya yi kokarin shi kadai, ba da yawun FUTA ba. | |
KORONA: An samu karin mutum 604, yanzu mutum 38,948 suka kamu a Najeriya. | |
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 604 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Alhamis. | |
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -203, Oyo-87, FCT-79, Edo-41, Osun-35, Ogun-24, Rivers-22, Kaduna-22, Akwa Ibom-20, Filato-18, Delta-9, Ebonyi-9, Imo-8, Enugu-5, Kano-5, Cross River-5, Katsina-4, Nasarawa-3, Borno-2, Ekiti-2 da Bauchi-1. | |
Yanzu mutum 38,948 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 16,061 sun warke, 833 sun rasu. | |
Sannan kuma zuwa yanzu mutum 22,054 ke dauke da cutar a Najeriya. | |
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 14,009 FCT - 3,376, Oyo - 2,306, Edo - 2,105, Delta - 1,453, Rivers -1,587, Kano -1,452, Ogun - 1,227, Kaduna - 1,289, Katsina -717, Ondo - 1001 , Borno -605, Gombe - 558, Bauchi - 535, Ebonyi - 724, Filato - 780, Enugu - 726, Abia - 527, Imo - 462, Jigawa - 322, Kwara - 707, Bayelsa - 326, Nasarawa - 292, Osun - 394, Sokoto - 153, Niger - 166, Akwa Ibom - 196, Benue - 294, Adamawa - 115, Anambra - 132, Kebbi - 90, Zamfara - 77, Yobe - 64, Ekiti - 88, Taraba- 54, Kogi - 5, da Cross Rivers - 31. | |
Hanyoyin guje wa kamuwa da cutar covid-19. | |
Ita cutar akan kama ta ne a dalilin cudanya da dabbobi domin sune ke dauke da ita. | |
Sakamakon bincike da aka yi game da cutar ya nuna cewa akan kamu da cutar ne ta hanyar yin mu'amula da dabbobi na gida da na daji. | |
A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu. | |
Za a iya amfani da man tsaftace hannu wato "Hand sanitizer" domin tsaftace hannu idan Babu ruwa da sabulu. | |
A rika rufe hanci da baki idan za a yi atishawa da kuma tari. | |
A Wanke da kuma dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci haka kuma kwai. | |
A Nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman mura ko Kuma tari. | |
A Rika amfani da takunkumin fuska musamman idan za a fita ko Kuma ana cikin mutane. | |
A gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya. | |
Shugabannin Yarbawa sun yi barazanar kaurcewa zaben 2023. | |
Shugabannin kungiyoyin Yarbawa a Najeriya sun yi barazanar kauracewa zabukan kasar na shekarar 2023, muddin aka ki amsa bukatarsu ta sauya fasalin tsarin mulkin kasar wato "Restructuring" a turance. | |
Kungiyoyin Yarbawan sun sha alwashin ne cikin takardar bayan taron da suka fitar, inda suka ce sauya fasalin tsarin mulkin Najeriya ne kadai zai ceto kasar daga cikin mawuyacin halin da ta fada, musamman ta fuskokin tsaro da kuma tattalin arziki. | |
Shugabanin da suka halarci taron hadin gwiwar sun hada da jagoran kungiyar Afenifere pa Reuben Fashoranti, da farfesa Banji Akintoye shugaban kungiyar Yoruba World Congress sai kuma tsohon gwamnan jihar Ondo Dakta Olusegun Mimiko. | |
Gamayyar kungiyoyin Yarbawan sun kuma koka kan rashin daidaito wajen raba mukamai da gwamnatin Najeriya ke yi, karkashin shugabancin Muhammadu Buhari. | |
Yayin da gwamnatin jihar Kano ta rage kasafin kudinta na bana da kimanin naira biliyan 70 saboda mummunan tasirin da annobar cutar coronavirus ta yi ga tattalin arzikin jihar, majalisar dokokin jihar ta zartar da sabuwar dokar kula da tsarin tafiyar da harkokin kudaden gwamnatin jihar. | |
Sai dai kungiyoyin rajin shugabanci na gari na cewa, batun samar da doka lamari ne mai sauki, amma aiwatar da ita shine kalubalen. | |
Samar da sabuwar alkiblar tafiyar da kudaden gwamnati bisa tsarin dimokaradiyya na daga cikin manufar sabuwar dokar a jihar Kano wadda tun a shekarun baya aka samar da ita a matakin tarayya da ma wasu jihohin Najeriya. | |
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano, Honarabul Kabiru Hassan Dashi, ya shaida wa Muryar Amurka cewa, dokar za ta bai wa ma'aikatu da gwamnatin jihar ka'idar yadda za su kashe kudadensu, tare da yadda jihar za ta kasafta kudinta. | |
Yanzu haka dai kungiyoyin rajin shugabanci na gari sun yi maraba da wannan doka, muddin dai za a bita sau da kafa. | |
Daraktan kungiyar Organization for Community Civic Engagement mai shelkwata a jihar Kano, Comrade Abdulrazak Alkali ya ce suna fatan jami'an gwamnati, da gwamnatin jihar za su aiwatar da dokar yadda ya kamata. | |
To amma kwamishinan kudi da harkokin tattalin arziki na jihar Kano Alhaji Shehu Na'Allah ya ce sun shirya sosai domin aiki da dokar ka'in da na'in. | |
Tuni dai gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu akan wannan sabuwar doka a karshen makon da ya gabata, kuma nan take ake sa ran za ta fara aiki. | |
INEC ta shirya wa zaben Edo -Farfesa Yakubu. | |
Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa hukumar sa ta shirya tsaf domin gudanar da zaben gwamnan Jihar Edo, wanda za a jefa kuri'a a ranar 19 Ga Satumba. | |
Yakubu ya yi wannan bayani mai karfafa guiwa a ranar Alhamis, lokacin da ya ke ganawa da Kwamitin Tuntubar Harkokin Tsaron Gudanar da Zabe a Benin, babban birnin Jihar Edo. | |
Farfesa ya ce INEC ya zuwa yanzu ta samu nasarar aiwatar da tsare-tsare har guda 10 daga cikin 14 da suka kudiri aniyar aiwatarwa dangane da zaben. | |
Yakubu ya kara da cewa, dalilin wannan ziyara shi ne domin ya ga irin shirye-shiryen da aka fara tun yanzu kafin gabatowar ranar zabe. | |
Tabbas mu na samun dukkan rahotannin shirye-shiryen da ke gudana. | |
Amma duk da haka mu ka ga ya dace mu zo da kan mu, domin gani da idon mu karara. | |
Wannan hukuma ta fitar da jadawalin tsare-tsaren yadda matakan zabukan Edo da Ondo za su gudana, tun a ranar 6 Ga Fabrairu, 2020. | |
Kenan mun bayar da sararin watanni kusan bakwai zuwa takwas domin a shirya wa zabubbukan biyu sosai. | |
To a yau ina farin cikin cewa mun aiwatar da tsare-tsare 10 daga cikin 14 da INEC ta shirya aiwatarwa. | |
Kuma babu wanda aka samu wani tsaikon da har sai da ta kai an sake daga ranar da za a aiwatar da shi. | |
Abu na karshe shi ne damka rajistar gaba dayan masu jefa kuri'a adadin su baki daya ga jam'iyyu 14 da za su fafata takara Inji Yakubu. | |
Ya ce ayyuka hudu da suka rage wa INEC sun hada buga sanarwar zabe da za a yi ranar Talata mai zuwa, gabatar da sunayen ejan-ejan na kowace jam'iyyar da ta shiga takara, duk a rana daya. | |
Sai kuma dakatar da kamfen sa'oi 24 kafin zabe. | |
Kenan za a dakatar da kamfen 12 na daren Alhamis, kafin Asabar din da za a yi zabe. | |
Saboda haka mu dai sai mu ce mun ma rigaya mun kimtsa, sai jiran zuwan ranar zabe kawai. | |
In ji Yakubu. | |
Sai dai kuma ya yi tsinkayen cewa zaben gwamnan jihar Edo ne zaben farko da INEC za ta fara gudanarwa a lokacin korona. | |
A kan haka ya ce hukumar zabe ta fito da ka'idojin yadda za a gudanar da zaben a wannan yanayi da ake ciki. | |
Mun jaraba tsarin da ka'idojin a wani karamin zaben cike, gurbi a Jihar Nasarawa. | |
Kuma mun shirya maimaita tsarin a wannan babban zabe a Edo. | |
Tun da farko Kwamishinan Zabe na Jihar Edo, Johnson Alalibo, cewa ya yi akwai masu rajista mutum milyan 2,210,534 a Jihar Edo. | |
Ya ce milyan 1,159,325 maza ne, mata kuma milyan 1,051,209. | |
Takaddama ta kunno kai a tsakanin Amurka da Chaina. | |
Chaina ta mayarwa Amurka da martani a sakamakon rufe ofishin jakandancin Amurka na birnin Chengdu da ta yi a wannan Juma'a. | |
Ma'aikatar harkokin wajen Chainan ta ce, ta yanke shawarar ce a sakamakon rufe ofishin jakadancin kasarta da ke birnin Houston na jihar Texas da Amurkan ta yi a farkon wannan makon. | |
Dama fadar Beijing ta yi gargadin yin ramuwa, muddun fadar Washington ba ta gaggauta janye matakinta ba. | |
Shekaru talatin da biyar da suka gabata, Amurka ta bude ofishin na birnin Chengdu da ke da ma'aikata kimanin dari biyu. | |
Dangantakar kasashen biyu, ta fada cikin mawuyacin hali tun bayan bullar annobar Coronavirus a daidai lokacin da suke kokarin daidaita rikici, kan kulla yarjejeniyar kasuwanci. | |
Atyap, Hausa-Fulani Sun Cimma Yarjejeniyar Zaman Lafiya Tsakaninsu. | |
Al'ummomin kabilun Atyap, Fulani da Hausawa da su ke da zama a cikin karamar hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna sun yi nasarar kammala wani taron sasantawa, domin samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin nasu. | |
Mahalarta taron wadanda su ka nuna kuduri da aniyarsu na ganin wanzar da zaman lafiya da yafe wa juna, sun yi tir da kashe-kashe da barnatar da dukiyoyi da su ka afku a yankin nasu. | |
Sun kuma shelanta aniyarsu ta taimakawa hukumomin tsaro da bayanan sirri, domin kama duk wasu batagari da su ke boye a cikin yankunan nasu. | |
Taron kuma ya yaba wa kokarin gwamnati na sanya jami'an tsaro a yankin, haka nan ya yaba wa kungiyoyin matasa daban-daban a bisa dattakon da su ka nuna na rungumar juna da nisantar duk wani abin da zai iya kawo yamutsi a yankin gami da kokarin da matasan su ka yi na ganin samun nasarar kafa wannan yarjejeniyar sulhun a tsakaninsu. | |
Taron, wanda a ka yi shi a karkashin jagorancin basaraken Agwatyap, Dominic Gambo Yahaya, ya samar da haduwar al'ummomin uku, domin tattaunawa a kan samar da zaman lafiyan. | |
Taron an yi shi ne a cibiyar nan ta Mariyamu and Yakubu Ebent Centre da ke Unguwar Wakili. | |
Haka kuma taron ya sami shugabancin ABM Stephen Shekari (rty) da Dakta Salim Umar, wanda ya wakilci masarautar Atyap, domin sasantawa a tsakanin al'ummomin da dakatar da zubar da jini da barnatar da dukiyoyin da ke wakana a tsakaninsu. | |
Dukkanin shugabannin al'ummomin uku na Atyap, Fulani da Hausawa, ne su ka sanya hannu a kan takardar bayan taro gami da mai martaba basaraken Agwatyap. | |
A takardar bayan taron wacce ke dauke da matsaya har guda 14, mazauna masarautar ta Atyap sun yi kira da ka da wani ya dauki doka a hannunsa, a maimakon hakan a rika kai kuka ne zuwa ga hukumomin tsaro. | |
Taron ya kuma nuna tabbacin da tsarin mulkin kasar nan ya bayar ga duk wani dan Nijeriya na zama da kai-komo a duk wani sashe na kasar nan da yake da bukata a cikinsa, wanda ya hada har da masarautar ta Atyap, ba tare da tsoro ko nuna masa wata barazana daga kowa ba ta kowace fuska. | |
Taron ya kuma yi kira ga hukumomi da su hanzarta tsara hanyar komawar duk ƴan gudun hijirar masarautar zuwa cikin gidajensu. | |
Taron ya kuma bayar da shawarar kafa wani kwamitin wanzar da zaman lafiya da zai kunshi kabilun, Hausa, Fulani da Atyap da matasansu domin shirya manyan taruka da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi samar da tsaro daga lokaci zuwa lokaci domin wanzar da zaman lafiya a masarautar ta su. | |
Taron sulhun zaman lafiyar yana zuwa ne awanni bayan da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi sassauci a kan dokar taɓacin da ta kafa a kananan hukumomin na Zangon Kataf da Kaura, na Jihar domin toshe kafar barkewar rikici a tsakanin mazauna yankin. | |
Yadda Ganduje ya maida hakiman da Sarki Ado da Sanusi suka kora, zai maida su masu naɗa sarakuna a Kano. | |
Gwamna Abdullahi Ganduje na so Majalisar Dokokin Jihar Kano ta gyara dokar jihar ta 2019, yadda zai tabbatar da naɗin wasu manyan muƙarraban masarautar Kano biyu da marigayi Sarki Ado Bayero da Sarki Sanusi suka sallama, ta yadda dokar jihar za ta tabbatar da naɗin su a matsayin manyan hakimai masu naɗa Sarki a Kano. | |
Kakakin Majalisar Kano, Abdullahi Gafasa ne ya karanta buƙatar Ganduje a gaban zauren majalisa, kuma ana sa ran za su yi zaman tattauna batun kafin ƙarshen watan Yuli. | |
Hakiman da aka dawo da su masarautar Kano su ne Aminu Babba Ɗan'agundi da kuma, wanda ya yi Sarkin Dawaki Mai Tuta da kuma Ciroman Kano, Sanusi Ado-Bayero. | |
Su biyun dai Sarki Ado da Sarki Muhammadu Sanusi ne suka cire su, bisa zargin yin maƙarƙashiya. | |
Babba Ɗan'agundi ya ƙalubalanci tsige shi a kotu. | |
Shekaru 17 ana tafka shari'a har dai Kotun Koli ta zartas da cewa ya tsigu. | |
Shi ne kuma Ganduje ke son ya maida a kan sarautar sa, kuma a gyara doka ya kasance ya na cikin masu naɗa sarki a masarautar Kano. | |
Ado Bayero ya cire Ɗan'agundi cikin 2003 bayan an same shi da laifin maƙarƙashiya da kuma yin kane-kane cikin lamarin siyasa. | |
An kafa kwamitin da zai bincike shi, amma aka gayyace shi ya ƙi zuwa gaban kwamiti domin ya kare kan sa. | |
Daga nan ya ƙalubalanci cire shi a Babbar Kotun Jihar Kano har zuwa Kotun Koli. | |
Kafin Kotun ƙoli, Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta yanke hukuncin a mayar da Aminu Babba a kan kujerar sa. | |
Amma masarautar Kano karkashin mulkin Muhamamdu Sanunmsi II, ta daukaka kara, inda Kotun ƙoli ta jaddada cirewar da aka yi masa a matsayin Hakimin Gabasawa, kuma Sarkin Dawaki Mai Tuta, a ranar 5 Ga Yuni. | |
Bayan an cire Sanusi Bayero, Ciroman Kano saboda ya ƙi amincewa da Sarautar Sarkin Kano da aka nada Muhammdu Sanusi II a cikin Yuni, 2014. | |
Daga baya an nada shi Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa ta Kasa a zamanin Jonathan. | |
Shi ne aka nada Wamban Kano, a ƙarƙashin Sarkin Kano na yanzu. | |
Gwamnatin jigawa na yi wa ma'aikata rijista a shirin asusun kiwon lafiya. | |
Gwamnatin jihar Jigawa, ta fara yi wa ma'aikatan jihar rijistar shirin Asusun kiwon Lafiya bayan sanya hannu kan dokar shirin da gwamnan jihar Alhaji Muhd Badaru Abubakar ya yi, tun a bara. | |
Babban Sakataran zartarwar hukumar asusun kiwon Lafiya ta jihar Jigawa Dr. Nura Ibrahim Salisu ne ya bayyana haka ga manema labarai, jim kadan bayan fara yin aikin rijistar a gidan Gwamnatin jihar Jigawa. | |
Ku saurari wakilinmu daga Dutsen Jihar Jigawa Muhd Aminu Umar Shuwajo a cikin jerin labaru na nan gaba. | |
NAPTIP ta cafke masu safarar mutane, ta ceto mutum 71 a jihar Kano. | |
Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa NAPTIP reshen jihar Kano ta cafke masu safaran mutane guda uku sannan sun ceto mutum 71 daga hannun su a jihar. | |
Kwamandar hukumar na shiyar jihar Kano Shehu Umar ya sanar da haka ranar Juma'a da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya. | |
Ya ce hukumar ta yi wa masu safarar mutane dirar mikiya bayan ta samu bayanan siri kan aiyyukan safarar mutane a jihar. | |
A dalilin haka ne hukumar ta yi farautar wadannan mutane daga ranar 15 zuwa 19 ga watan Yuli inda har aka yi nasarar damke su. | |
Daga cikin mutum ukun da muka damke mutum biyu ƴan kasar Kamaru ne daya dan Najeriya sannan shekarun su duka ba su wuce 21 zuwa 36 ba. | |
An Kama wadannan mutane yayin da suke hanyar zuwa kasashen Algeria, Morocco da Libya. | |
Bayan haka Mutum 18 daga cikin mutum 71 din da za a yi safarar su daga kasar Kamaru suke inda daga ciki akwai maza 14, Mata 4. | |
Sauran mutane 19 da suka rage daga Najeriya suke, maza 11, Mata 8 duk kuma ƴan daga jihar Kano. | |
Umar ya ce za a damka mutum 18 ga gwamnatin kasar Kamaru domin ci gaba da bincike. | |
Ya Kuma ce hukumar ta karbi Mutum 34 da hukumar NIS ta ceto a jihar Katsina. | |
An Kama wadannan mutane ba tare da cikakkun takardun tafiya ba sannan ga dukkan alamu a hanyar su na kokarin ficewa daga kasar nan. | |
Ƙoƙari Da Jajircewa Da Neman Na Kai, Abu Ne Da ke Cikin Zuciya - Leadership Hausa Newspapers. | |
A ƙauyen Longyuan na yankin Hongsipu na birnin Wuzhong da ke jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta, dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin. | |
Akwai wata jajirtacciyar mata mai suna Li Yaomei ko kuma Sadiya (wato sunanta na musulunci) da ta shahara saboda irin gwagwarmayar da ta sha a rayuwa da kuma nasarar da ta samu bisa ƙoƙarinta na fita daga ƙangin talauci. | |
Labarinta ya gaya mana cewa, ƙoƙari da jajircewa da neman na kai, abu ne dake cikin zuciya. | |
Da farko dai ita Li Yaomei ko Sadiya, ba ta taɓa zama a aji da nufin ɗaukar darasi ba, lamarin da ya sa ba ta iya karatu bare rubutu ba. | |
Sai dai Allah ya yi mata baiwar basira da hazaƙa da kuma hikima mai tarin yawa, inda har ta kasance abun misali a fannin yaƙi da talauci. | |
Kimanin shekaru 20 da suka wuce, Madam Li Yaomei, ta yi fama da ciwon sankarar ciki, inda aka kai ga yi mata tiyata a ciki har sau 3. | |
Bayan farfaɗowarta kuma, sai ta gamu da mummunan hatsari, yanzu haka tana tafiya ne tare da ƙarfen da aka sanya a cikin ƙafarta. | |
Waɗannan ƙalubale da ta fuskanta sun jefa ta cikin mawuyacin hali baya ga na lafiya, har ma da batun kuƙin magani, dalilin da ya sa ta karɓi rancen kimanin Yuan dubu dari 3, kwatankwacin sama da Naira miliyan 16. | |
Abun mamaki shi ne, wannan ƙalubale da Malama Sadiya ta fuskanta ya zame mata wata hanyar zaburarwa da zage damtse domin ganin ta inganta rayuwarta. | |
Sannan tallafin da gwamnatin ƙasar Sin ta ba ta, ya ƙara mata ƙwarin gwiwa. | |
Sana'arta ita ce yin tsintsiya nau'ika daban-daban bisa amfani da ciyayi. | |
Saboda namijin ƙoƙarinta, sana'ar tata ta bunƙasa sosai, inda ma'aikatu daban-daban ke ba ta odar tsinya. | |
Baya ga haka, ta ƙirƙiro injuna da dama da suke taimaka mata wajen sauƙaƙa aikin. | |
Misali, ta kan ɗauki minti 15 wajen haɗa babbar tsintsiya ɗaya, amma yanzu a cikin wannan lokaci, za ta haɗa tsintsiyoyi har 5. | |
Baya ga haka, ta samar da wasu ƙarin injunan dake tsaftace ciyayin da take mayarwa tsintsiya. | |
Sannan akwai ƙarin injin dake tsaftace mata abincin dabbobi, kuma yanzu har sayar da waɗannan injunan take ga masu nema. | |
Ganin ƙalubalen da Malama Sadiya ta shiga, da kuma ƙoƙarin da har yanzu take yi na inganta rayuwarta da na ma'aikatanta, za a fahimci cewa lallai mai nema na tare da samu. | |
Aikin yaƙi da talauci da kyautata rayuwa, ba abu ne da ya rataya kacokan a kan gwamnati ba. | |
Idan gwamnati za ta riƙa samar da tallafi, amma mutane ba su da karsashi ko sha'awar inganta zaman rayuwarsu ta hanyar nemarwa kansu ayyukan yi bisa halin da suke ciki, to kwan-gaba-kwan-baya kaɗai za a ci gaba da yi ba tare da cimma wata manufa ba. | |
Labarinta ya nuna cewa gudanar da wata sana'a ko aikin samun kuɗin shiga ba ya buƙatar wasu maƙudan kuɗaɗe ko tafiye-tafiye zuwa wasu garuruwa ko ƙasashen waje. | |
Domin ita ta yi la'akari ne da yanayin da take ciki, ta yi amfani da albarkatun da ke akwai a muhallinta wajen kyautata rayuwarta. | |
Bugu da ƙari, malama Sadiya ta gudanar da waɗannan ayyuka ne bisa tsayawa da ƙafarta ba tare da dogaro da mijinta ba, domin ya gudu ya bar ta. | |
Wato dai, kokari da jajircewa da neman na kai, abu ne dake cikin zuciya. | |
Sannan ya nuna irin ƙarfin da mata ke da shi na sauya rayuwarsu da kuma tsayawa da kafarsu ba tare da neman taimakon wani ba. | |
Wannan ma darasi ne da ke nuna cewa, duk abun da mutum zai yi, ya kamata ya tsaya da kafarsa, domin dogaro da wani ba shi da tabbas. | |
Hakika Malama Sadiya ta kasance jajirtacciya, mai kaifin basira da hazaƙa wadda ta zama misali kuma abun koyi ga sauran jama'a. | |
Har ila yau, zuwa watan Maris na bana, Malama Sadiya ta kammala biyan dukkan bashin da ake binta, sannan kuma ta dakatar da karɓar tallafi daga gwamnati bisa raɗin kanta. | |
Faeza Mustafa. | |
Akwai Fargabar Ƴan Siyasar Amurka Za Su Lalata Kokarin Dakile COVID-19 - Leadership Hausa Newspapers. | |
A kwanakin baya ne babban daraktan hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya nuna damuwa kan matakan da wasu kasashe suke dauka, na adana allurar rigakafin cutar numfashi ta COVID-19 da ake fatan an samar, inda ya bayyana cewa, dole ne a kaucewa nuna fifiko kan al'ummun kasashe daban daban, yayin da ake raba allurar rigakafin annobar. | |
Kuma ya kamata a raba allurar ta hanyar da ta dace a fadin duniya, saboda hakan zai dace da babbar moriyar kasashe daban daban. | |
Hakika wasu ƴan siyasar Amurka suna aiwatar da manufar nuna fifiko kan moriyar kansu, game da raba allurar rigakafin cutar, haka kuma suna gurgunta haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasa da ƙasa a bangaren yaki da annobar. | |
A halin yanzu, gaba daya adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a fadin duniya ya riga ya zarta miliyan 23. | |
A cikin adadin kuma, akwai mutanen da suka rasa rayukan su sakamakon cutar da ya kai sama da dubu 800. | |
A karkashin irin wannan yanayi mai tsanani, ana ƙara mai da hankali kan tasirin allurar rigakafin cutar, kuma abun farin ciki shi ne, a kwanakin baya bayan nan, an samu babban sakamako wajen nazarin allurar a wasu kasashe, lamarin da ya samar da fata, da imani ga ɗaukacin al'ummun kasashen duniya baki daya. | |
Amma abun bakin ciki shi ne, wasu ƴan siyasar Amurka sun nuna burin ƙwace allurar. | |
Har ma mujallar "Science" ta fayyace cewa, gwamnatin Amurka ta riga ta daddale yarjejeniyoyin sayen allurar rigakafin COVID-19 da darajarsu ta kai dala sama da biliyan 6, daga kamfanonin hada magunguna da dama. | |
Duk da cewa, an fahimci manufar gwamnatin Amurka, kasancewar Amurkar ce kan gaba wajen yaduwar cutar, amma sauran kasashe masu tasowa su ma suna bukatar allurar matuka, duba da cewa sun fi fama da karancin albarkatun kiwon lafiya. | |
Mujallar "The Ecologist" ita ma ta yi nuni da cewa, idan Amurka ta cimma burin kwashe allurar rigakafin da za a samar, to adadin allurar da za a samarwa kasashe masu tasowa zai ragu. | |
Kaza lika babban daraktan cibiyar dakile cututtuka ta Afirka CDC Mr. John Nkengasong, shi ma ya nuna damuwa kan wannan batun. | |
Kamar yadda wasu masu yin sharhi kan al'amuran yau da kullum suka bayyana, ko da ma an yi nasarar samar da allurar rigakafin, ba zai yiwu a cimma burin ganin bayan cutar ba, sai an tsara yadda za a raba allurar, wanda hakan batu ne mai muhimmanci matuka ga kasa da kasa. | |
Kuma ya dace kasashen duniya su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu. | |
Babban daraktan hukumar WHO Tedros, shi ma ya nuna cewa, idan ana son ganin bayan cutar, dole ne a dakile ta daga dukkanin fannoni a fadin duniya, kana ba zai yiwu wasu sassa na duniya, ko wasu kasashe kalilan su cimma burin farfadowa daga tasirin annobar su kadai ba. | |
Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa. | |
An maka jiga-jigan gwamnatin Buhari da suka raka gawar Abba Kyari makabarta a Kotu. | |
Wani Mai nemar wa Ƴan Najeriya hakki, ya maka dukkan jiga-jigan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da suka raka gawar Abba Kyari makabarta. | |
Kyari, wanda shi ne Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, an binne gawar sa a Makabartar Gudu da ke Abuja, a ranar 18 Ga Afrilu, bayan ya mutu sanadiyyar cutar Coronavirus. | |
Mai kara Tope Akinyade, ya maka su Kutun Majistare da ke Kado, Abuja, inda ya nemi kotu ta hukunta su, saboda sun karya dokar killace mutane a gida da gwamnatin tarayya ta kakaba a lokacin. | |
Ya ce akwai rashin adalci matuka ga Ƴan Najeriya wadanda aka rika kamawa ana hukuntawa a lokacin zaman gida tilas, amma kuma ga wasu gungun jama'a sun karya dokar, babu wanda aka hukunta daga cikin su. | |
Ya ce idan dai har gwamnatin Buhari adalci ta ke kururuwar tabbatarwa, to bai ga dalilin da zai sa a rika bin talakawa ana kamawa idan sun karya dokar Korona ba. | |
Su kuma wasu gungun na jikin gwamnati sun karya dokar amma an kyale su. | |
Daga cikin wadanda Tope ya maka kotu, akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Ministan Sufurin Jirage, Hadi Sirika, Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, Ministar Harkokin Agaji da Jinkai, Sadiya Umar. | |
Akwai kuma Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu, jami'in yada labarai na soshiyal midiya, Bashir Ahmed, Mashawarcin Shugaba Buhari kan Harkokin Tsaro, Babagana Monguno, Sufeto Janar na Ƴan Sanda, Mohammed Adamu da wasu jiga-jigan gwamnatin masu yawa. | |
Mai Shari'a Celestine Odo ya nemi ya nuna cewa Mai shigar da kara ya yi kuskure tunda wadanda ake kara din ba su sa hannu a takardar karar su da ya yi ba. | |
Sai dai kuma shi Tope ya tunatar wa Mai Shari'a din cewa shi fa kai tsaye ya kawo kara a kotu, bai yi wani biye-biye ta hannun "yan sanda ba. | |
Ya ce aikin alkali ne ya aika wa dukkanin wadanda ake karar sammacin da za su sa hannu. | |
Domin shi dai ya yi abin da dokar Najeriya ta ba shi ƴancin yi wajen shigar da karar a kotu. | |
Mai Shari'a ya dage sauraren shigar da karar, ya ce a koma kotu ranar 4 Ga Agusta, domin ci gaba da saurare. | |
An Sake Zabar Adesina Shugaban Bankin Ci Gaban Afirka - Leadership Hausa Newspapers. | |
An sake zaben Akinwunmi Adesina a matsayin shugaban bankin Ci gaban nahiyar Afrika (AFDB). | |
Adesina zai sake jagorantar bankin na tsawon karin shekara biyar a matsayin wa'adi na biyu. | |
Hakan na zuwa ne bayan da aka wanke shi daga aikata ba daidai ba a wa'adinsa na farko. | |
An sake zabar Mista Adesina ne a yau Alhamis, yayin wani taro da ake yi ta shafin intanet da manyan jami'an bankin suka halarta. | |
Adesina tsohon ministan aikin gona na Nijeriya ya lashe zaben babu hammaya bayan da wani kwamiti na musamman ya wanke shi daga zargin nuna bambamci tare da fifita ƴan Nijeriya wajen bayar da aiki da kuma kwangiloli a bankin na bunkasa Nahiyar Afrika. | |
Najeriya za ta karbo Dala miliyan 200 na badakalar Malabu. | |
Gwamnatin Najeriya ta ce tana dakon karbar Dala miliyan 200 daga cikin badakalar cinikin rijiyar man da aka yi wa lakabi da Malabu wanda za su fito daga kasashen Netherland da Switzerland. | |
Ministan Shari'a Abubakar Malami ya sanar da haka, inda yake cewa a karkashin shirin yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Muhammadu Buhari ke yi, Najeriya ta yi nasarar kwato kudin da ya kai Dala biliyan 62 daga hannayen kamfanonin mai. | |
Malami ya kuma ce a karkashin wannan gwamnati, Najeriya ta karbo Dala miliyan 311 daga gwamnatin Amurka da New Jersey daga cikin kudaden da Abacha ya diba da kuma wasu karin Dala miliyan 6 da dubu 300 daga Jamhuriyar Ireland. | |
Ministan Shari'ar ya ce, Najeriya ta yi nasarar kwato Naira miliyan 685 a cikin shekara guda da taimakon masu kwarmato, yayin da gwamnati ta kuma samo Naira miliyan 500 daga jiragen ruwa da tankunan mai da ake amfani da su wajen sace man kasar. | |
Malami ya ce ma'aikatarsa ta taimaka wajen tsara yadda za a karbi harajin gidan waya wanda ya tashi daga Naira biliyan 22 da ake karba zuwa Naira biliyan 66 a cikin watanni 6 da suka gabata. | |
Fadar shugaban Kasa Ta Maida Martani Kan Kira Da PDP Ta Yi Na Shugaba Buhari Yayi Murabus. | |
Fadar shugaban kasa ta ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, watau Peoples Democratic Party (PDP)Furuci da dabi'un ta sun saba wa doka. | |
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya yi wannan sanarwar ne ta wata sanarwa da ya fitar a daren Juma'a. | |
Da yake mayar da martani ga wata sanarwa da aka yi wa shugaban jam'iyyar PDP na kasa, inda aka yi kira ga murabus din Shugaba Buhari. | |
Shehu ya ce, a daidai lokacin da duniya baki daya ke hada kai domin tunkarar maki guda, jam'iyyar adawa ta Najeriya, Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP ta fara yakin neman zabe. | |
Wanda wannan ɗabi'a ce da ta saɓa da tsarin mulkin ƙasa, ta yin kira ga murabus din Shugaba Muhammadu Buhari saboda barin izinin bincike ga wasu ofisoshin gwamnati da dama, har da Hukumar Yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC. | |
Dangane da bayanin da shugaban jam'iyyar, Prince Uche Secondus ya bayar, a bayyane yake cewa za su so shugaban kasar ya dakatar da bincike amma ya rufe abubuwa. | |
kar a tayar da zaki daga barci kamar yadda wani daga cikin shugabanninsu ya furta. | |
PDP ba za ta iya tsoratar da gwamnati daga zartar da mummunan zargi da aka yiwa MDAs da shugabanninsu ba saboda rashin yin hakan zai zama tarihi na cin amanar jama'a. | |
Shugabannin ECOWAS Na Ci Gaba Da Kokarin Sasanta Rikicin Mali. | |
Shugabannin kasashen Afrika ta yamma za su yi wani taron koli ta yanar gizo ranar Litinin 27 ga watan Yuli domin gabatar da matakan kawo karshen rikicin siyasar kasar Mali da ke kara muni, bayan da wasu Shugabannin kasashe biyar na kungiyar suka gana da gwamnatin Mali da bangaren ƴan adawa a Bamako babban birnin kasar ranar Alhamis 23 ga watan Yuli. | |
Jagoran kungiyar kasashen ECOWAS, Shugaba Mahammadou Issoufou na Nijer, ya ce kungiyar kasashen na yammacin yankin Afrika za ta yi duk abinda ya dace domin sulhunta rikicin siyasar da ke faruwa a Mali, a cewar wata sanarwar da gwamnatin Najeriya ta tura wa manema labarai. | |
Taron da aka yi ranar Alhamis, wanda ya samu halartar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da Shugaban Mali Ibrahim Boubakar Keita mai masaukin baki, da Shugaba Machy Sall na kasar Senegal, da Nana Akufo -Addo na Ghana, da Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire, sun saurari jawabai daga wakilin ECOWAS na musamman tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, da kuma madugun ƴan adawar Mali Imam Mahmoud Dicko, da wakilan hadakar ƴan adawa, da kuma kungiyoyin al'umma. | |
Shugaban Mali ya yi wa Shugabannin kasashen jawabi game da yanayin zamantakewa da siyasar kasar, musamman rashin jituwar da aka samu da ta kai ga zanga-zanga da tashin hankali. | |
Keita ya ce Shugabannin na ECOWAS sun riga sun amince da cewa akwai bukatar a cimma yarjejeniya domin kiyaye zaman lafiya da mutuncin kasar. | |
Ya kara da cewa barin rikicin siyasar Mali ya kara tsananta zai iya shafar yanayin tsaro a yankin Afrika ta yamma, musamman kasashe makwabtan Mali. | |
Gwamnatin Najeriya za ta kashe dala biliyan 6 kan lantarki. | |
Ministan lantarkin Najeriya Injiniya Sale Mamman, yace gwamnati ta ware dala biliyan 6 da miliyan 15, kwatankwacin naira tiriliyan 2 da biliyan 37, domin kawo karshen matsalar wutar lantarkin da kasar ta share shekaru tana fama da ita. | |
Cikin sanarwar da ya fitar bayan cika shekara guda da nada shi kan mukamin, Ministan yace shirinsu a yanzu shi ne cimma matakin samar da lantarki da karfinta ya kai Megawatts dubu 25 nan da shekarar 2025 a karkashin yarjejeniyar aikin da Najeriya ta kulla da kamfanin Siemiens kan dala biliyan 2 da miliyan 300. | |
Wasu karin ayyukan da ministan lantarkin Najeriyar ya ce za a aiwatar da dalar biliyan 6 sun hada da gayara kananan tashoshin rarraba hasken lantarki 105 da gina wasu 70 sabbi, sai kuma samar da manyan layuka ko wayoyin lantarki na tsawon sama da kilomita dubu 5. | |
A halin yanzu dai karfin megawatts dubu 5 Najeriya ke da shi, da a wani lokacin ma kan sauka kasa da dubu 4. | |
Yan Bindiga Sun Sace Dalibai a Karamar Hukumar Chukun, Kaduna. | |
Al'ummomin garuruwan da ke yankin Udawan, karamar hukumar Chukun sun ce banda dalibai shida da ke rubuta jarabawar WEAC da aka sace, akwai wasu mutane ma da su ka kwashe watanni ba a sako su ba. | |
Hare-haren 'yan bindiga a wasu yankunanan jihar Kaduna dai sun hana al'umma da damar sukuni amma gwamnatin jihar Kaduna ta ce tana dukkan mai yuwuwa domin kawo karshen wadannan hare-hare, Inji Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida malam Samuel Aruwan. | |
Hare-haren 'yan bindiga a yankunan karkara dai sun hana manoma da dama zuwa gona wanda wasu ke fargabar hakan zai iya haifar da karancin abinci a Najeriya. | |
Sasancin Gwamnatin Katsina Da Ƴan Bindiga Ɓarnar Kuɗin Talakawa Ne, Cewar Mai-Shari'a Ummaru Abdullahi - Leadership Hausa Newspapers. | |
Dole Sai Mun Koma Wa Gaskiya Za A Zauna Lafiya A Nijeriya. | |
Tsohon Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Ƙasa, Mai Shariah Umaru Abdullahi (Walin Hausa) ya bayyana cewa sulhun da Gwamnatin Jihar Katsina, ta yi da ƴan bindiga, da wani babban kuskure da ɓarnar kuɗin talakkawa. | |
Saboda bai yi tasiri ba ko alama na kawo ƙarshen kashe-kashen ƴan bindiga da suka addabi jihar Katsina. | |
Mai Shari'ah Umaru Abdullahi ya bayyana hakan ne, a lokacin da yake tattaunawa ta musamman da manema Labarai a gidansa da ke Katsina, cikin har da Leadership A yau. | |
Bayan kammala aza harsashin gina ɗakin Mata da yara, mai ɗaukar gadaje ashirin da biyar, wanda wani ɗan kasuwa zai gina a babban asibitin garin Katsina, wanda shi ne Shugaban taron. | |
Tsohan Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Ƙasa, ya Ƙara da cewa sulhun da aka yi da Ƴan bindigar, ba haka ya kamata a aiwatar da shi ba. | |
Saboda yace, ya za a ce ɗan ta'adda ya kawo bindiga a bashi dubu dari biyu da hamsin, da ya koma daji, sai ya sayi bindiga ƙirar AƘ 47. | |
Walin Hausa ya ci gaba da cewa duk duniya babu inda yaƘi ya haifar da nasara, kamata ya yi a yi sulhu da su, ta hanyar inganta rayuwar makiyaya, wato a samar masu da wurin kiwo da makarantu da ruwan sha da wajen kiwon lafiya. | |
A da har Ma'aikatar kula da kiwon dabbobi ke akwai a lardin arewa, kuma duk shekara Gwamnati a kowane mataki tana kasafin kuɗi kan manoma kawai, amma su makiyaya ban da su, dole sai an zo an yi gyara da kuma adalci, sannan za a samu zaman lafiya mai ɗorewa. | |
Amma wannan yaƙin da ake yi ba zai haifawa ƙasar nan da Ɗa Mai ido ba, saboda dukkan su ƴan kasar nan ne, sulhu shi ne hanyar da ta dace. | |
A yi shi kuma da kyakkyawar niyya, za a samu zaman lafiya. | |
Abun nan fa ba mu kadai ya shafa ba. | |
Nan gaba ƴaƴanmu da jikokin, ya za su rayu nan gaba, nan ne babbar matsala. | |
A duniyar nan ba a taba yaƙi da bindiga wanda aka ƙarasa shi da bindiga ba, bisa teburi ake sulhunta shi. | |
Masana tsaro suna cewa ba a sulhunta wa da yan ta'adda, wannan gurguwar shawara ce, saboda ko Amerika da ke cewa ba ta sulhu da ƴan taadda, ai su nasu ƴan ta'addan ba yan ƙasar Amerika ba ne, mutanen wata ƙasa ne suke kai masu farmaki. | |
Mu kuma ƴan bindigar nan yan kasar nan ne, sai a ce ba za a yi sulhu da su ba. | |
FEPSAN Ta Yi Hadaka Da Manoma - Leadership Hausa Newspapers. | |
Kungiyar masu sarrafa takin zamani ta kasa FEPSAN, ta bayyana cewa, za ta yi hadaka da kungiyoyin manoma da ke kasar nan don yakar masu gurbata takin. | |
Babban Sakataren kungiyar ta FEPSAN Mista Gideon Negedu ne ya sanar da hakan a hirarsa da jaridar Banguard. | |
Babban Sakataren kungiyar ta FEPSAN Mista Gideon Negedu ya na bayani ne kan kokarin da kungiyar ta FEPSAN ke kanyi na magance ayyukan bata gari dake gurbata takin a kasar nan. | |
A cewar Babban Sakataren kungiyar ta FEPSAN Mista Gideon Negedu, kudin na takin zamani wanda a yanzu ya zamo doka, zai taimaka matuka wajen magance matsalar. | |
Har ila yau, Babban Sakataren kungiyar ta FEPSAN Mista Gideon Negedu ya bayyana cewa, hakan zai kuma bai wa Ma'aikar Aikin Gona da Raya Karkara damar yin amfani da dokar domin hukunta dukkan wanda aka kama yana gurbata takin na zamani. | |
Babban Sakataren kungiyar ta FEPSAN Mista Gideon Negedu ya kuma bayar sabbin lambobi guda biyu na karta kwana da jama'a za su kira domin fallasa masu aikata haramtacciyar dabi'ar kamar haka, 08175077773 da 08175777724. | |
A cewar Babban Sakataren kungiyar ta FEPSAN Mista Gideon Negedu, duk inda muke son zuwa yanzu shi ne fadada hanyoyinmu ko tattaunawa tare da kungiyoyin gona domin su kasance cikin sa ido kan mutanen da ke da hannu a kan wannan kuma nan da nan za su kai rahoto. | |
Ya kuma kara da cewa kungiyar ta yi ayyuka da yawa don dakile karancin takin, wannan ita ce, hanya daya tilo da muka yi ayyuka da yawa. | |
Babban Sakataren kungiyar ta FEPSAN Mista Gideon Negedu Mun yi aiki akan Tsarin Taki ta doka. | |
Ya kuma ce, kungiyar ta FEPSAN a matsayin kungiya a karkashin jagorancin Mista Thomas ya yi aiki sosai domin mayar da kudurin zuwa doka. | |
Babban Sakataren kungiyar ta FEPSAN Mista Gideon Negedu ya ce akwai abubuwa da yawa da za su iya yi. | |
An zartar da dokar a cikin doka. | |
Ya ce, duk wani dan kungiyar FEPSAN yasan karya kusantar da takin zamani, kuma ba wannan kadai ba, ana yiwa kowane dan kungiyar FEPSAN kwarin gwiwa domin tabbatar da cewa ya lura da ingancin kayan masarufinsa saboda akwai hukunce-hukuncen dokar a waccan dokar idan ya lalata takin. | |
Babban Sakataren kungiyar ta FEPSAN Mista Gideon Negedu ya sanar da cewa, "Mun yi aiki a kan hakan kuma muna aiki kan hakan don tabbatar da cewa tare da Ma'aikatar Aikin Gona wacce ita ce ke shugabantar su, sune suke aiwatar da dokar". | |
Babban Sakataren kungiyar ta FEPSAN Mista Gideon Negedu Muna aiki tare da su don tabbatar da cewa akwai kyakkyawan bin inganci. | |
Babban Sakataren kungiyar ta FEPSAN Mista Gideon Negedu ya ce FEPSAN tana da nata kwamiti na sa ido don yin aiki lokaci zuwa lokaci don bincika, amma ra'ayin shine cewa da zaran zamu iya samun wadannan abubuwan to yanzu zamu iya samun Ma'aikatar Aikin Gona ko Ma'aikatar Gogewar Injin Farji wacce ta aiwatar da wannan dokar kai tsaye. | |
Shugaban Afrika Ta Kudu Ya Yi Tir Da Takaddamar Da Ake Yi Kan Kwangiloli. | |
Shugaban Afrika Ta Kudu ya yi bayani na gwalewa saboda yadda rashawa ta yi katutu a jam'iyyar ANC ta kasar mai mulki. | |
Cyril Ramaphosa, a wata wasika da ya rubuta jiya Lahadi 23 ga watan Agusta, da aka tura wa duk mambobin jam'iyyar ta ANC, ya fara da caccakar batun cece-ku-cen da ake yi akan bada kwangiloli don taimakawa kasar wajen yaki da cutar coronavirus. | |
Abinda ya kawo cece-ku-cen shi ne akwai kamfanoni masu zaman kansu da wasu mutane, ciki har da jami'an gwamnati da suka yi amfani da matsalar kayan asibiti, da zamantakewar al'umma da kuma tattalin arziki domin azurta kansu, a cewar wasikar. | |
Ba za a yafe wannan yaudarar ta miliyoyin ƴan Afrika Ta Kudu ba da yanayin cutar COVID-19 ya shafa, suna fuskantar yunwa a kullum, da rashin ayyukan yi. | |
A cikin wasikar Ramaphosa ya kuma rubuta cewa an gano miliyoyin kudin kasar da ya kamata a yi amfani da su wajen inganta fannin sufuri, da samar da abubuwan more rayuwa ga talakawa. Da kuma ingantacciyar wutar lantarki, da taimakawa manoma bakar fata da ke tasowa da kuma bunkasa kasar baki daya, wadda miyagu suka sace suka sanya a aljihunsu. | |
Shugaba Ramaphosa ya ce kada jama'a su yi tunanin cewa jam'iyyar ANC wata hanya ce ta samun iko kawai, ko dukiya da fada a ji. | |
Yadda kwamishinan lafiya na jihar Legos ya kamu da Korona. | |
Kwamishinan lafiya na jihar Legos Farfesa Akin Abayomi ya kamu da cutar corona. | |
Hakan na cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Gbenga Omotoso ya sanyawa hannu. | |
Ta cikin sanarwar ta bayyana cewa Abayomi ya kamu da cutar ne sakamakon yin mu'amala da wani mnutum wanda yake fama da rashin lafiya kuma bayan yi masa gwajin an tabbatar da yana dauke da cutar covid-19. | |
Sanarwar ta kara da cewa tuni Abayomi ya dauki matakin killace kan sa biyo bayan tabbatar da ya kamu da cutar duk da cewa baya jin wasu alamu na bayyanar cutar. | |
Najeriya na fuskantar koma bayan tattalin arziki mafi tsanani a bana. | |
Wallafawa ranar: 24/08/2020 - 16:33. | |
Hukumar Kididdigar Najeriya ta sanar da cewar tattalin arzikin kasar ya samu koma bayan da ba a taba ganin irin sa ba a cikin shekaru 10 da suka gabata, sakamakon koma bayan da ya zarce sama da kashi 6 da aka gani tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni na wannan shekarar. | |
Alkaluman da Hukumar ta fitar yau sun nuna cewar tsakanin watannin Afrilu zuwa Yuni, sakamakon annobar COVID-19 da ta mamaye kasashen duniya da kuma dakatar da harkokin yau da kullum, tattalin arzikin Najeriya ya shiga yanayin da bai taba shiga ba tsakanin shekarar 2010 zuwa 2020. | |
Hukumar ta lissafa dalilan da suka haifar da matsalar da suka hada da tilastawa mutane zaman gida a fadin kasar da hana zirga zirgar ababan hawa da hana sufurin jiragen sama da rufe makarantu da kasuwanni. | |
Hukumar ta kara da cewar daukar irin wadannan matakai a kasashen duniya ya sa farashin man fetur ya fadi warwas, yayin da kuma aka rufe masana'antu a kasashen duniya domin tinkarar matsalar. | |
A watan Mayun da ya gabata, ministan kudin Najeriya Zainab Ahmed ta ce Hukumar Kididdigar ta yi hasashen fadawa cikin irin wannan yanayi, sakamakon wadannan matsaloli da suka hana gudanar da harkokin yau da kullum, abinda ya tilastawa gwamnatin kasar zabtare kasafin kudaden ta. | |
Akpabio ya fasa kwai kan kwangilar ƴan majalisun Najeriya. | |
Ministan Raya Yankin Niger Delta da ke Najeriya, Godswill Akpabio ya bayyana sunayen ƴan majalisun da Hukumar NDDC ta bai wa kwangilar gudanar da wasu manyan ayyuka. | |
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin shugabannin Hukumar Raya Yankin na Niger Delta NDDC da handame makuden kudade. | |
Daga cikin sunayen ƴan majalisun da suka karbi kwangilar har da shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai Kula da Yankin Niger Delta, Peter Nwabaoshi wanda ya karbi jerin kwangiloli har guda 53 kamar yadda Minista Akpabio ya sanar. | |
Mista Akpabio ya kuma ce, Sanata Mathew Urhoghide ya kabi kwangiloli shida, sai Sanata James Manager da shi ma ya karbi kwangiloli shida, yayin da tsohon Sanata, Samuel Anyanwu ya karbi 19. | |
Kazalika tsohon shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da Hukumar NDDC, Nicholas Mutu, ya amshi kwangiloli har guda 74, wanda shi ne adadi mafi girma kamar yadda Akpabio ya bayyana a cikin wasu takardu da ya aike wa kwamitin da ke gudanar da bincike kan zargin almundahana a Hukumar Raya Yankin Niger Delta. | |
Har ila yau an samu wasu ƴan tsirarun ƴan majalisu daga Ondo da Edo da suka karbi kwangilolin daga hukumar ta NDDC. | |
Takardun da Akpabio din ya fitar, sun nuna cewa, an bada akasarin kwangilolin ne a shekarar 2018, amma ba a bayyana adadin kudaden da aka kashe ba wajen gudanar da su. | |
Wannan na zuwa ne bayan kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya yi barazanar maka Akpabio a kotu bisa zargin sa da yunkurin bata wa ƴan majalisun suna. | |
MDD ta shawarci Buhari ya yi amfani da siyasa don magance matsalar tsaro. | |
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi amfani da tattaunawa da kuma tafarkin siyasa wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi kasar. | |
Babban Jakadan Majalisar da ke Najeriya Edward Kallon ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci wata tawaga zuwa fadar shugaban, inda ya ke cewa matsalolin tsaron da suka addabi kasar da ke da rassa daban daban na da wahalar magance su. | |
Kallon ya ce yayinda sojoji su ke can suna fafatawa, yana da matukar muhimmanci a goya musu baya wajen tattaunawa da amfani da hanyar siyasa domin samun zama lafiya. | |
Jami'in ya bayyana matsalolin da suka addabi Najeriya guda 3 da suka hada da matsalar zama dan kasa da mallakar dukiyar kasa da kuma rikicin shugabanci. | |
Kallon ya ce Majalisar na kashe akalla Dala biliyan guda da rabi kowacce shekara wajen gudanar da ayyukan jinkai a Najeriya, musamman a yankin da ake fama da rikicin boko haram. | |
Jami'in ya yabawa shugaba Buhari kan rawar da ya ke takawa wajen yaki da cin hanci da rashawa da kwato dukiyar jama'a tare da kuma sake fasalin ayyukan gwamnati, inda ya bukaci shugaban ya fadada wajen sanya hannu mazauna yankunan karkara cikin yakin. | |
Mayaƙan Boko Haram sun halaka dattijai 75 a Gwoza | |
Wallafawa ranar: 27/08/2020 - 10:55 Canzawa ranar: 27/08/2020 - 13:04 | |
Ɗan Majalisar Dattawan Najeriya dake wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewar mayakan Boko Haram sun yiwa dattijan dake karamar hukumar Gwoza 75 yankan rago a dare guda. | |
Ɗan majalisar ya ƙara da cewar baya ga dattijan da suka halaka a watannin baya lokacin da suke kan ganiyar kai hare-hare a sassan jihar Borno, mayaƙan na Boko Haram sun kuma yiwa matasa da dama kisan gilla a yankin na Gwoza, ta hanyar sanya su yin layi, inda suka kuma riƙa bi suna harbewa ɗaya bayan ɗaya. | |
Yayin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki da Majalisar ta shirya kan rikicin, a baya bayan nan, Sanata Ndume yace har ya zuwa wannan lokaci yankin sa na Gwoza na fama da matsalar tsaron da ba zai iya zuwa wurin ba. | |
Ɗan Majalisar wanda ya yabawa sojoji kan ƘoƘarin da suke, yace har yanzu rikicin Boko Haram bai Ƙare ba, ganin yadda suke ci gaba da hallaka mutane a Jiharsa. | |
Sanata Ndume ya kuma koka kan cewar har yanzu dubban al'ummar jihar Borno da sauran sassan yankin arewa maso gabashin Najeriya na fama da matsalar yunwa. | |
Kwamitin daukar ma'aikata na Kano zai magance yin kutse - Abubakar General - Freedom Radio Nigeria. | |
Kwamitin daukan ma'aikata a kananan hukumomin jihar Kano wanda gwamnatin tarayya za ta yi da ya kai dubu dari bakwai da saba'in da hudu a jihohin kasar nan 36, ya ce zai mangance yin kutse a shirin samar da aiki yi da za'a yi nan bada jimawa ba. | |
Sakataren yada labarai na kwamitin daukar ma'aikata na jihar Kano Abubakar Muhammad general ne ya bayyana hakan a yau, jim kadan bayan kammala shirin "Barka da Hantsi" na nan tashar freedom radiyo, wanda ya maida hankali kan yadda tsarin daukan matasan aiki zai kasance a jihar Kano. | |
A cewar General, kwamitin a nan Kano mai dauke da mutum Ashirin ya tsara rarraba form din shaidar samun gurbin aikin ga matasa domin magance samun masu yin kutse a irin wannan sha'ani. | |
Abubakar Muhammad ya kuma ce, za a fara shirin ne a ranar daya ga watan Okotoba, kuma zai dauki tsawon watanni uku ana yin sa tare da biyan ma'aikata dubu Ashirin a kowanne karshen wata. | |
General Abubakar ya ce, kwamitin ya hada da sarakunan gargajiya da malamai da sauran masu fada aji. | |
A don haka akwai bukatar al'ummar jihar Kano musamman wadanda suke da aiki su bai wa marasa aikin yi damar samun shiga shirin domin magance matsalolin matasa marasa aikin yi a kasar nan. | |
Yadda Na Tsere Daga Hannun Ƴan Sanda - Shahararren Mai Kisa Shodipe. | |
Shahararren dan ta'addar nan da Ƴan sanda suke nema ruwa a jallo da ya yi kaurin suna wajen kashe mutane, Sunday Shodipe, ya bayyana yadda aka yi ya samu dama ya tsere daga ofishin Ƴan sandan Mokola, Ibadan ta Jihar Oyo a ranar Talata. | |
Wanda ake zargin ya ce wata sabuwar shugaba ta reshen, wacce aka kawo ofishin Ƴan sandan kwanan nan ce ta umurci wani jami'i mai suna Funsho da ya bar shi ya yi wanka. | |
Ya ce jami'in ya gargade shi a kan kada ya yi yunkurin tserewa yayin da yake wanka, inda ya kara da cewa a wannan lokacin shi bai yi tunanin guduwa ba ma. | |
Shodipe ya bayyana cewa ya yi nasarar tserewa ne lokacin da ya ga cewa hankalin jami'in ya yi nisa wajen tattaunawa da wani mutum kuma baya lura da shi. | |
Ya ce wannan sabuwar DPO mace da aka kawo ta bukaci Funsho da ya kyale ni na yi wanka. | |
Ya gargade ni a kan kada na yi kokarin guduwa a lokacin da nake wanka. | |
Na tsere ne lokacin da naga yana tattaunawa da wani mutum. | |
Na hau saman tuka-tuka sannan na haura katanga. | |
Mutanen da ke zaune a yankin sun gan ni lokacin da nake tserewa amma basu fallasa ba. | |
Sahara Reporters ta tattaro cewa wani matashi daga Akure, jihar Ondo, wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya bayar da kansa domin taimakawa ƴan sanda lokacin da ya ga labarin cigiyar wanda ake zargin da kuma garabasar da aka sanya kan bankado shi. | |
Ya ce ya yi tattaki har zuwa Ibadan tare da wasu abokansa uku da niyyar farautar mai laifin na kwanaki uku. | |
Da isar su jihar, sai suka yada zango a wani otel inda suka kwana kafin suka bazama nemansa. | |
An tattaro cewa mutanen uku sun bibiye shi zuwa inda ya sayi tabar wiwi a birnin, amma sai suka yanke shawarar kin kama shi saboda dandazon jama'a a yankin. | |
Daga baya sai ƴan garin suka kama shi yayin da yake shi kadai a mabuyarsa. | |
Wanda ake zargin ya kashe kimanin mutum takwas wadanda suka kasance duk mata a Karamar Hukumar Akinyele da ke jihar Oyo. | |
Yobe Ta Kashe Sama Da N78.8m Wajen Farfado Da Kamfanin Leda - Leadership Hausa Newspapers. | |
An yaba da kokarin gwamnatin jihar Yobe, a karkashin Gwamna Mai Mala Buni wajen sake farfado da kamfanin leda da fatun buhunan leda, mallakin jihar (Yobe state Polythene Bag and Woben sacks Company), bayan shafe sama da shekaru 10 a garkame ba ya aiki. | |
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kamfanin (General Manager), Injiniya Sha'aibu Adamu Gadaka, a zantawar sa da wakilin mu a ofishin sa da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, a farkon mako. | |
Ya ce, kamfanin ya shafe sama da shekaru 10 a kulle, amma bayan zuwan Gwamna Buni ke da wuya ya kudurci aniyar sake farfado da shi, wanda nan take ya bayar da umurnin cire naira miliyan 78.8 domin gyara muhimman bangarorin kamfanin tare da karin naira miliyan 48 na gudanar dashi, yayin da hakan ya bai wa kamfanin damar takawa da kafafun shi. | |
Eng. Gadaka ya kara da bayyana cewa wannan ya ba su zarafin sayo kayayyakin da ake da bukata domin fara aiki a kamfanin, wadanda su ka hada da sabuwar na'urar bayar da wutar lantarki (Janareta) mai karfin 500 KbA, na'urar rarraba wutar lantarki (Taransifoma) 500 KbA, sabon injin din yayyanka fatun buhunan, injin din dinka buhunan (yan zamani) da sauran kayayyakin aiki wadanda kamfanin ke da bukata. | |
Sannan kuma ya kada baki ya ce, "Har wala yau kuma, babban makasudin wannan yunkuri na Gwamna Buni, wajen sake farfado da wannan kamfani shi ne don a samar wa da matasa ayyukan yi, tare da rage zaman kashe wando da samar wa da jihar Yobe kudin shiga". | |
In ji Gadaka. | |
A hannu guda kuma, ya ce kamfanin ya samu tagomashin masaya hajar da yake alkintawa, saboda yadda gwamnatin jihar ta farfado da kamfanin fulawa da abincin dabbobi (Yobe Flour and Feed Mill) da ke garin Potiskum da sauran yan kasuwar da ke zawarcin kayan da kamfanin ke samar wa. | |
Ya ce, dadin-dadawa kuma da yunkurin da gwamnatin jihar ke yi wajen gyara kamfanin takin zamani shima wata kafa ce ta sayen kayan da kamfanin ke sarrafawa. | |
A gefe guda kuma ya ce, "Akwai wasu kalubalen da mu ke fuskanta, bisa dalilin yadda kamfanin ya shafe sama da shekaru 10 a kulle, yayin da injinan sun fara aiki amma akwai bukatar sauya mu su wasu kayayyaki domin samun damar gudanar da aiki ba tare da wata fargaba ba". | |
Wanda mu na sa ran kafin ayyukanmu su kankama, za mu yi kokarin kawo sauran kayayyakin da mu ke da bukata. | |
Bugu da kari kuma, Gadaka ya ce, "A bangare guda kuma, mu na rokon gwamnatin Yobe ta kara ba mu sauran kayan aiki, babbar motar daukar kaya da motocin da za mu rika amfani da su wajen gudanar da ayyukanmu cikin sauki, musamman domin jigilar ma'aikatan mu zuwa ofis saboda kaucewa zuwa a makare, a lokacin da mu ka fara aiki gadan-gadan". | |
Haka kuma ya ce a halin da a ke ciki yanzu kamfanin ya tura matasa 25 don su samu horon yadda za su yi aiki da mashina da na'urarori tare da sarrafa kayayyakin da kamfanin ke amfani dasu a ayyukan shi kana da yadda za su yi mu'amalar kasuwanci da jama'ar da su ke hulda da su. | |
A karshe ya ce yanzu haka kamfanin ya fara samar da fatun buhunan leda kala daban-daban, wadanda su ka hada da ma su girman 100kg, 50kg da 25kg tare da bayar da kafa ga yan kasuwa dangane da kala da yanayin buhunan da su ke da muradi, kamfanin a shirye ya ke ya gamsar da su. | |
Wutar Daji Ta Halaka Mutum Biyar A California - Leadership Hausa Newspapers. | |
Yayin da sama da jami'an kashe gobara dubu 12 ke ta kokarin shawo kan wata wutar daji da ke ci a California da ke Amurka, gwamnan jihar Gavin Newsom ya ce, ya nemi taimakon kasashen Canada da Australia, baya ga tallafin da ya nema daga gwamnatin tarayya. | |
Gwamnan ya ce Australia na daya daga cikin kasashen da ke da "kwararrun jami'an kashe wutar daji a duniya". | |
A ranar Juma'a Newsom ya ce, wutar dajin ta yi ta'adi matuka a arewacin jihar, inda dubban mutane suka tserewa gidajensu kana wasu daruruwan gidaje da gine-gine suka kone. | |
A cewar Newsome, "an kwashe shekaru da dama rabon da jihar ta ga irin wannan wutar daji", yana mai cewa wutar tana karar da kudade da kayayyakin da ke hannunsu. | |
Akalla mutum biyar ne suka mutu kana wasu 43 suka jikkata ciki har da jami'an kashe gobara, a wannan wutar daji, da ta lakume yankin da nisansa ya kai kilomita dubu 2,020. | |
Cutar Koronabiros Na Ci Gaba Da Bazuwa A Najeriya. | |
Sabbin alƙaluman da hukumar NCDC ta fitar sun nuna cewa an samu karin ɗaruruwan mutane da suka kamu da cutar COVID-19 a ƙasar. | |
A cewar hukumar, mutum 648 ne cutar ta harba a ranar Litinin 27 ga watan Yuli, wanda hakan ya mayar da adadin mutanen da suka kamu da cutar a ƙasar zuwa 41,180. | |
Hukumar ta kuma bayyana cewa mutum 18,203 ne suka warke daga cutar yayin da mutum 860 suka mutu. | |
An samu sabbin alkaluman ne daga jihohi 21 kuma har yanzu jihar Lagas ce ke kan gaba a yawan waɗanda suka kamu da cutar ta koronabiros, yanzu ta sake samun mutum 180. | |
Sai jihar Plateau da ke bin ta da mutum 148. | |
Sauran jihohin da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar sun hada da birnin tarayya Abuja da Karin mutum 44, Ondo - 42, Kwara - 38, Rivers - 32, Oyo - 29, Kaduna - 21, Osun - 20, Edo - 17, Ogun - 17, Ekiti - 11, Kano - 9, Benue - 9, Delta - 9, Abia - 9, Niger - 7, Gombe - 3, Borno - 1, Bauchi - 1, Imo - 1. | |
Mali na ci gaba da neman dunke baraka. | |
Firaministan na kasar Mali Boubou Cisse, ya bukaci Imam Mahmoud Dicko, wanda a hannu guda babban malami ne mai wa'azin addinin Islama da kuma ke da karfin fadi a ji, da ya karbi tayin sasanci da gwamnati ta bayar, musamman ma wajen shawo kan jiga-jigan masu zafin adawa da gwamnatin. | |
A ranar Litinin da ta gabata, kungiyar ECOWAS ta bukaci Shugaba Ibarhim Boubacar Keita da ya samar da gwamnatin hadaka, sannan ya yi gyara ga kura-kuran siyasa da suka haddasa husumar da kasar ta fada. | |
Sai dai a nasu bangaren masu adawa da gwamnatin na Mali, sun yi watsi ne da shawarar ta ECOWAS, wadda wasu shugabannin Afirka ta Yamma suka bayar a zama karo na biyu da suka yi a Bamako babban birnin kasar. | |
Gwamnatin Najeriya ta sauya matsayinta kan jarabawar dalibai. | |
Gwamnatin Najeriya ta sauya matsayinta dangane da hana yara masu shirin kammala karatu damar zana jarabawar bana, sakamakon sabon matsayin da ta dauka na bude makarantun sakandare daga ranar 4 ga watan gobe domin gudanar da jarabawar. | |
Mai magana da yawun Ma'aikatar Ilimin Najeriya Ben Goong ya ce gwamnati ta sake matsayinta wajen amincewa da shirin gudanar da jarabawar wadda za ta fara daga ranar 17 ga watan Agusta mai zuwa. | |
Jami'in ya ce bude makarantun ranar 4 ga watan gobe zai bai wa daliban da ke aji 3 na manyan sakandare damar shiryawa na makwanni biyu kafin fara jarabawar. | |
Wannan sabon matsayi ya soke wanda Ministan Ilimi Adamu Adamu ya dauka wanda ya bayyana dakatar da jarabawar na illa-masha-Allahu saboda karuwar masu kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya. | |
A lokacin da yake bayani bayan daukar wancan matsayi, ministan wanda ya ce alhakin yara daliban Najeriya na wuyarsa ne, ya ce ba zai ki ba a soke jarabawar gaba daya a wannan shekara domin kare lafiyar yaran. | |
Wannan matsayi na shi ya gamu da suka daga sassa daban daban cikin su har da Majalisar Wakilan Najeriya dangane da hana dalibai masu shirin kammala karatu zana jarabawar. | |
Yayin da a bangare daya kuma kwamishinonin ilimi na jihohin arewa 19 suka goya masa baya. | |
Mutum 2,732 aka yi wa kisan-gilla cikin watan Afrilu da Yuni a Najeriya -Rahoto | |
An kiyasta cewa an kashe mutum 2,732 a Najeriya cikin watanni biyu kacal, daga Afrilu zuwa Yuni. | |
Rahoton wadda cibiya mai suna SBM intelligence ta fitar a Lagos, ta ce ta tattara bayanan ne a daga rahotannin da jaridu daban-daban ke wallafawa a ƙasar nan. | |
Rahoton ya tattara ƙididdiga daga jaridu da suka hada da kashe-kashen gilla, sun hada da kisa daga Boko Haram, kisa a bangaren masu garkuwa da mutane, samamen "yan bindiga, hare-haren makiyaya da kuma kashe-kashen da ke da kusanci da ƙabilanci da yankunan karkara. | |
Wannan gagarimin aikin ƙididdiga na haɗin-gwiwa ne tsakanin cibiyar SBM Intelligence da kuma wata kungiya mai suna "Enough is Enough". | |
Cikin watan Afrilu dai SBM ta wallafa ƙididdigar kisan-gilla ga kusan mutum 1,000 da ta ce su ne adadin waɗanda jaridu suka buga an yi wa kisan-gilla tsakanin watan Janairu zuwa Maris, 2020. | |
SBM ta ce rahoton ya jiɓinci hujjoji daga ɓangarorin nazarin harkokin tsaro, ƙungiyoyi masu sa-ido kan taɓarɓarewar matsalar tsaro na waje da kuma na cikin gida. | |
Kuma duk ta lissafa sunayen ƙungiyoyin. | |
Kisan-gilla kan waɗanda ba su ji ba, kuma ba su gani ba ya ƙara tsananin muni saboda rashin maida hankali kacokan da gwamnati da jami'an tsaro suka yi wajen koƙarin daƙile kashe-kashen. | |
Rahoton ya kuma yi tsokacin yadda kulle jama'a a gida saboda cutar Coronavirus ya haifar da ƙuncin rayuwa da rashin aikin yi ga matasan da aka yi ƙiyasi kusan kaso 43%. | |
Daga daga cikin masu nazarin harkokin tsaro a SBM Intelligence, mai suna Confidence Isaiah, ya bayyana wasu dalilan da suka haifar da ƙaruwar kashe-kashen daga watan Afrilu zuwa Yuni. | |
Isaiah ya ce akwai kisan-gillar da Boko Haram suka riƙa yi wa sojoji, Sannan kuma ƴan bindiga sun rikiɗe daga satar shanu da garkuwa da mutane, sun koma amfani da zabga-zabgan makamai su na karkashe mutane. | |
Sun yi rahoton kashe-kashen a jihohi 33 da Abuja, da suka haɗa da kisan jami'an tsaro 221 da suka haɗa da sojoji 173, ƴan sanda 39, NSCDC 3, duk a cikin wata uku. | |
Sannan kuma sun ce an kashe ƴan ta'adda 845, ƴan bindiga 502. | |
Mutum 941 aka kashe a Barno, 143 a Yobe, Taraba 113, Zamfara 444, Katsina 207, Sokoto 99, Kaduna 179. | |
Bata gari sun addabi yankin mu - Kwamitin cigaban Farawa - Freedom Radio Nigeria. | |
Kwamitin ci gaban al'ummar garin Farawa da ke karamar hukumar Kumbotso a nan Kano ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu bata-garin matasa suka addabi yankin na su tare da jefa al'umma cikin halin fargaba. | |
Shugaban kwamitin Alhaji Adamu Dahiru Farawa ne ya bayyana hakan lokacin da yake jan hankalin al'ummar yankin domin ganin sun mayar da hankali wajen samawa kansu tsaro musamman ma a tsakanin matasa. | |
Ya kara da cewa kwamitin ya samu rahotannin yadda wasu bata-gari ke haurawa gidajen mutane cikin dare tare da yi musu sace-sace da kuma yi musu barazana da lafiyarsu, yana mai cewar wajibi ne su tallafawa jami'an tsaro ta hanyar sanya ido sosai da kuma bayar da rahotan. | |
Alhaji Adamu Dahiru Farawa ya kuma bukaci rundunar ƴan sandan jihar Kano da ta kara musu jami'an tsaro a yankin don magance matsalar da suke fuskanta. | |
Wakilinmu Shamsu Da'u Abdullahi ya rawaito cewa al'ummar garin na cikin halin damuwa da fargaba da zarar magriba ta yi, inda suka yi kira ga mawadatan da ke cikinsu da su taimakawa ƴan kwamitin da kayan aiki. | |
Balbalin Gobara ta yi ajalin mutum daya a jihar Kano. | |
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa mutum daya ya rasu a gobarar da aka yi a Kofar Ruwa dake karamar hukumar Dala ranar Litinin. | |
Kakakin hukumar Saidu Mohammed ya ce wannan ibtila'i ya faru a daren Litini inda tanki dankare da man fetir ya Kama da wuta a gidan man Audu Manager. | |
Da misalin karfe 10:30 na dare wani Bello Musa ya kira hukumar mu yana bayanin cewa gobara a Kofar Ruwa. | |
Nan da nan ma'aikatan mu suka gaggauta garzayawa wannan wuri. | |
Isar su ke da wuya jami'ai suka yi kokarin kashe wutar sai dai kash, wani mai suna Adamu Salisu ya rasu a wannan gobara. | |
Idan ba a manta ba a watan Afrilu ne bukkokin masu gudun hijira 700 suka kama da wuta a sansanin "yan gudun hijira da ke Karamar Hukumar Mafa, cikin Jihar Barno. | |
Dimbin jama'a sun rasa matsugunan su sanadiyyar tashin gobarar, wadda ta barke wajen karfe 11 na safe kuma dauki tsawon lokaci ta na cin wuta. | |
Ya ce wutar wadda ta samo asali daga cikin wani tanti, ta kama sauran tantinan ne saboda babu gudummawar kashe gobara da gaggawa a sansanin. | |
Yan bindiga sun kashe mutane 20 a Dafur. | |
A karon farko cikin shekaru da dama ƴan bindiga sun kashe mutune 20, ciki har da yara kanana a yankin Dafur na kasar Sudan da yaki ya dai-dai-ta. | |
Wani shugaban Ƙabila ya bayyana cewa wannan na zuwa ne biyo bayan cimma wata yarjejeniya da masu gonaki cewar za su koma bakin aikin su na noma, sai dai a yammacin jiya ne ƴan tada kayar baya suka bude musu wuta tare da kashe mutane 20 ciki har da mata da kananan yara. | |
Lamarin ya faru ne a yankin Aboudous dake nisan kilomita 90 daga kudancin Nyala, babban birnin kudancin lardin Darfur. | |
A shekarar 2003 ne rikici ya barke a yankin Dafur tsakanin kabilu "yan tsiraru da "yan tawaye masu biyayya ga tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al-Bashir. | |
Majalisar dinkin duniya ta ce rikicin na yankin yayi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu 30, kana kuma ya raba miliyan 2 da rabi da muhallansu. | |
A cikin watan Afrilun shekarar 2019 ne aka hambarar da gwamnatin shugaba Omar Al-Bashir, biyo bayan watanni da aka kwashe ana zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa. | |
Ba Za A Daina Rigakafin Poliyo Ba - Ganduje. | |
Samun nasarar da Nijeriya ta yi na magance cutar Poliyo, ba ya na nufin tsayawa da kokarin da a ke yi na rigakafin cutar ba ne, inda kwararru da ma'aikatan lafiya za su cigaba gudanar da rigakafin cutar tare da sa ido, kamar yadda ka'idojin da a ka cimma da Hukumar Lafiya ta Duniya su ka tanada, domin dorewar wannan nasarar da a ka samu ta kawo karshen cutar ta Poliyo a Nijeriya, wato Shan'inna. | |
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kamar yadda babban daraktan yada labaransa, Malam Abba Anwar, ya bayyana. | |
Gwamnan ya bayyana haka ne a jawabin bude taron zaman Majalisar Zartawar da a ka gudanar jiya Laraba a dakin taron Fadar Gwamnatin Jihar Kano. | |
Ya kara da cewa, wannan matsayi ya biyo bayan hada karfin da a ka yi wajen yakar wannan cuta ne. | |
Zan iya tunawa a lokacin da na ke matsayin Mataimakin Gwamna, ni ke shugabantar kwamitin yaki da cutar Poliyo na Jihar Kano. | |
Dole na jinjina wa wadanda su ka bayar da gudunmawa wajen yakar wannan cuta. | |
"Dole na ambaci sunan Sarkin Yakin Kano, Alhaji Wada Aliyu Gaya, da sauran masu ruwa da tsaki, wadanda su ka tsaya tare da ni a lokacin wannan yaki", in ji shi. | |
Mutane irinsu Aliko dangote, wato Shugaban Gidauniyar dangote, da Bill Gates, Shugaban Gidauniyar Bill da Melinda, duk sun cancanci yabo, a cewar gwamnan, wadannan mutane sun kashe miliyoyin Daloli ko shakka babu sun cancanci a gode mu su kwarai da gaske. | |
Sauran masu ruwa da tsakin sun hada da abokan hadakarmu. | |
Gwamnan ya kara da cewa, dole mu gabatar da godiyarmu, dorewar wannan nasara na da muhimmacin gaske a dukkan al'amuran al'ummarmu na yau da kullum. | |
Hakan ce ta sa za mu ci gaba da kulawa da lamarin, domin tabbatuwar wannan matsayi. | |
Musulmai su dinga aikata ayyukan alheri - Empathy Foundation - Freedom Radio Nigeria. | |
Gidauniyar tausayawa da tallafawa mabuƙata wato Empathy Foundation ta ja hankalin al'ummar musulmi da su zage dantse wajen aikata ayyukan alkhairi a waɗannan kwanaki goma da muke ciki na zulhijja. | |
Shugaban kungiyar Mansur Musa Gabari ne ya bayyana hakan yayin da gidauniyar ta ziyarci gidan yara masu lalurar ƙwaƙwalwa ta "Torrey home" da ke unguwar Tudun Maliki da gidan kangararrun yara na Goron Dutse wato "Remand home" da na masu lalurar yoyon fitsari don raba musu kayan abinci. | |
Mansur Musa Gabari ya kuma ce, yana da kyau masu wadata su riƙa tallafawa waɗanda ba su dashi musamman a lokutan sallah. | |
Tun farko da ta ke jawabi, shugabar gidan kula da yara masu lalurar ƙwaƙwalwa ta "Torrey home" da ke unguwar Tudun-Maliki, Lauriya Sagir Garba, ta yabawa Gidauniyar ta Emphaty tare da buƙatar masu hannu da shuni | |
Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi'u ya rawaito cewa, a yau gidauniyar ta Emphaty za ta ziyarci Dawakin Kudu don bayar da tallafin kwanan rufi ga wani masallaci da ruwan sama ya yaye rufinsa. | |
Harin Rokoki Ya Shafi Wani Sansanin Sojin Amurka a Iraqi. | |
Wasu rokoki guda huɗu da aka harba sun dira kan wani sansanin soja da gamayyar dakarun da Amurka ke jagoranta ke amfani da shi a kudu da birnin Bagadaza ranar Juma'a 24 ga watan Yuli, kuma rokokin sun yi ɓarna amma ba a samu hasarar rai ba, a cewar wata sanarwar daga rundunar Sojin Iraqi. | |
Rokokin sun taɓa sansanin Besmaya, inda aka girke dakarun kasar Spain domin faɗan da suke yi da mayakan IS wanda Amurka ke jagoranta. | |
Amma gamayyar dakarun na rage yawan mayakanta a Iraqi. | |
A cikin ƴan watannin da suka gabata, an kai wasu hare-haren rokoki da suka taba sansanonin da aka tsugunnar da dakarun hadin gwiwar, suka kuma dira a kusa da ofishin jakadancin Amurka a Bagadaza. | |
Amurka ta dora laifin hare-haren kan ƙungiyoyin mayaƙan da Iran ke goyon baya. | |
Ya zuwa yanzu dai babu kungiyar mayaƙan da Iran ke mara wa baya da ta dauki alhakin hare-haren. | |
Kotu ta yi watsi da karar Sarkin Kano mai murabus - Muhammad Adamu - Freedom Radio Nigeria. | |
Babban Sufeto ƴan-sandan kasar nan Muhammad Adamu ya bukaci babbar kotun tarraya da ke zaman ta a birnin tarraya Abuja, da ta yi watsi da karar da Sarkin kano mai murabus Muhammdu Sunusi ya shigar gabanta, na hana shi shigowa jihar Kano. | |
A cewar Adamu, kotun ba ta da hurumin sauraren karar da Sarki mai murabus ya shigar gabanta. | |
Babban sufeton yan sandan kasar nan ya bayyana hakan ne ya yin, zantawa da manema labarai a birnin tarraya Abuja. | |
A cewar sa, kotun ta dakatar da karar ba tare da ba ta lokaci ba, zuwa wani lokacin. | |
Tun a ranar tara ga watan Maris wannan shekara ne dai, gwamnatin jihar Kano ta sauke Muhammad Sunusi daga kan karagar mulki. | |
Najeriya ta sauya ranar dawo da zirga-zirgar jiragen sama zuwa ƙasashen ƙetare | |
Wallafawa ranar: 27/08/2020 - 20:38 | |
Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage fara zirga zirgar jiragen sama zuwa ƙasashen duniya da aka shirya farawa daga ranar 29 ga watan nan saboda ƙaruwar masu kamuwa da cutar korona. | |
Ma'aikatar sufurin jiragen saman ƙasar ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin dakatar da fara zirga zirga saboda kar a buɗe ƙofa ga masu ɗauke da cutar daga ƙasashen duniya su daɗa yaɗa ta. | |
Sanarwar ta ce za a jinkirta buɗe ƙofofin ƙasar zuwa ranar 5 ga watan Satumba. | |
Najeriya ta samu mutum na farko da ya kamu da cutar korona ne a watan Fabarairu lokacin da wani ɗan ƙasar Italia ya shiga da ita. | |
Ya zuwa yanzu waɗanda suka kamu da cutar a Najeriya sun zarce dubu 50 yayin da sama da mutum dubu guda su ka mutu. | |
An yi wa sabbin jami'an ƴansanda karin girma a Kano - Freedom Radio Nigeria. | |
Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano Habu Sani ya buƙaci sabbin jami'an ƴan sanda da aka yi wa karin girma da su sadaukar da kawunan su wajen sauke nauyin da aka dora musu. | |
Wannan na kunshe cikin sanarwar da kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna ya sanya wa hannu. | |
Sanarwar ta kara da cewa daga cikin jami'an ƴan sandan da aka yiwa karin girman akwai masu rike da mukamin mataimakan Sufuritandan guda 9 da suka zama SP. | |
Sauran su ne jami'an ƴan sanda da aka daga linkafar zuwa DSP da kuma karin wasu jami'an su 239 da aka daga likkafar su zuwa ASP. | |